Jerin Manyan 'Yan Takara 5 da Suka Samu Tikitin Gwabzawa a Zaben Gwamnan Osun 2026
Osun, Nigeria - Jam'iyyun siyasa na ci gaba da shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar a shekarar 2026.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gwamna Ademola Adeleke, wanda wa'adinsa na farko zai kare a shekarar 2026, ya shirya neman zango ma biyu domin kammala shekaru takwas da doka ta kayyade.

Source: Twitter
A sanarwar da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, hukumar zabe (INEC) ta tsara gudanar da zaben gwamnan jihar Osun a ranar 22 ga watan Satumba, 2026.
Wa'adin da INEC ta ba jam'iyyu
A jadawalin zaben da INEC ta fitar, ta bai wa jam'iyyun siyasa damar gudanar da zaben fitar da gwani daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2024 zuwa 15 ga watan Disamba, 2025.
Bayan haka, INEC ta bayyana cewa za ta karbi sunayen 'yan takara na kowace jam'iyya daga nan zuwa 4 ga watan Maris, sannan za ta fitar da sunayen 'yan takara na karshe ranar 9 ga Maris, 2025.
Tuni jam'iyyun siyasa kamar APC da PDP suka gudanar da zabukan fitar da gwani, inda suka zabi dan takarar da zai fafata a zaben gwamnan Osun 2026.
Jerin manyan 'yan takara a zaben Osun
Legit Hausa ta tattaro muku jerin sunayen 'yan takarar da suka samu nasara a zabukan fitar da gwani na jam'iyyu siyasa a Osun, ga su kamar haka:
1. Gwamna Ademola Adeleke (Accord)
A ranar 2 ga watan Disamba, 2025, Gwamma Adeleke ya tabbatar da ficewarsa daga PDP saboda rigingimun cikin gida da suka addabi jam'iyyar.
Wasikar fitar gwamnan daga PDP na dauke da kwanan watan 4 ga watan Nuwamba, 2025, yana mai cewa ya dauki wannan mataki ne saboda rashin tabbatar a jam'iyya.
Kwanaki kadan bayan haka, Gwamna Adeleke ya sauya sheka zuwa jam'iyyar Accord domin samun damar tsayawa takara cikin aminci a zaben Osun da ke tafe.

Source: Facebook
Tashar Arise tv ta ruwaito cewa awanni 24 bayan sauya shekarsa, Gwamna Adeleke ya samu nasarar zama dan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar Accord.
Ademola Adeleke ya samu tikitin takarar jam'iyyar Accord ne a zaben fitar da gwanin da aka gudanar ranar Laraba, 10 ga watan Disamba, 2025 a Osogbo.
Adeleke, wanda shi kaɗai ne ya tsaya takara a zaben, ya samu nasara da kuri’u 145 daga cikin 150 da wakilan jam'iyyar suka kada.
2. Bola Oyebamiji (APC)
Tsohon shugaban hukumar NIWA ta kasa, Bola Oyebamiji ya lashe tikitin takarar gwamnan Osun karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaben fitar da gwanin da aka yi Asabar, 13 ga watan Disamba, 2025.
APC ta tsaida Oyebamiji ne bayan cimma yarjejeniyar masalaha da sauran 'yan takara tare da kada kuri'ar murya a wurin zaben fitar gwanin, wanda Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya jagoranta.
Daily Trust ta ce jimillar wakilai 1,660 da aka zabo daga kananan hukumomi 30 da kuma mazabu 332 a jihar Osun ne suka tabbatar da takarar Oyebamiji ta hanyar kada masa kuri'a.

Source: Twitter
Bayan kowa ya amince, Gwamna Okpebholo ya bayyana cewa:
"Bisa ikon da aka ba ni, ina gabatar muku da Bola Oyebamiji a matsayin ɗan takarar gwamnan Osun na jam’iyyarmu ta APC.”
3. Adebayo Adedamola (PDP)
A ranar Talata 2 ga watan Disambar 2025, Adebayo Adedamola ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar PDP domin zaben gwamnan Osun na 2026.
Vanguard ta kawo rahoton cewa Adedamola ya samu kuri’u 919 daga cikin kuri’u 957 da aka kada, wanda hakan ya ba shi nasarar zama dan takarar PDP.
Shugaban kwamitin zaben fitar da gwanin PDP, Humphrey Abba ne ya sanar da sakamakon bayan kammala zaben a Osogbo.
Abba ya bayyana cewa tun kafin fara kada kuri'a daya daga cikin yan takara ya janye, wanda hakan ya ba Adedamola damar samun nasara cikin sauki.
“An samu kuri’un da suka baci guda 20. Mun shaida muku tun da farko cewa ɗaya daga cikin ‘yan takara ya janye. Adebayo Adedamola ya samu kuri’u 919, kuma ya zama wanda ya yi nasara.”

Source: Facebook
4. Hon. Najeem Salaam (ADC)
Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Osun, Hon. Najeem Salaam, ya samu nasarar zama 'dan takarar jam'iyyar ADC a zaben gwamnan Osun na 2026.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Salaam ya sami tikitin jam'iyyar ADC bayan zaben fitar da gwani na jam'iyyar da aka gudanar a Cibiyar Al'adu ta Ultimate da ke Osogbo.
Yayin da yake jawabi ga wakilan jam'iyyar kafin fara kada kuri'a, Shugaban Kwamitin Zaben na ADC, Mista Emeka Nwajiuba, ya ce Salaam ne kadai 'dan takarar da ya nuna sha'awarsa.

Source: Facebook
Da yake sanar da sakamakon, Nwajiuba ya ce jimillar kuri'u 528 ne aka kada, wanda daga cikinsu 'dan takarar ya samu kuri'u 520, yayin da aka soke takwas.
"Bisa ikon da kundin tsarin mulkin ADC ya bai wa wannan kwamitin, ni, Emeka Nwajiuba, shugaban kwamitin, ina sanar da wanda aka zaba ya gwabza a zaben gwamnan Osun na 2026: Najeem Salaam," in ji shi.
5. Hon. Adewale Adebayo (APM)
An tabbatar da Hon. Adewale Adebayo, fitaccen mai zanen gidaje, a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Osun na jam'iyyar APM a zaɓen 2026.
Shugaban kwamitin zaben fitar da gwanin APM, Idowu Babarinde, ne ya tabbatar da takararsa a sakatariyar jam'iyyar da ke yankin Ogo-Oluwa a Osogbo.
The Nation ta ruwaito cewa Babarinde ya tabbatar da nasarar Adebayo ne bayan da 'yan jam'iyyar suka gabatar da shi a matsayin ɗan takara daya tilo da ke neman tikitin APM.
Babarinde ya ce,

Kara karanta wannan
Abubuwa 5 da muka sani game da daukar sababbin 'yan sanda 50,000 da za a yi a Najeriya
"Hanyar da muka amince da ita a zaben fidda gwani na yau ita ce tabbatar da dan takararmu, Hon. Adewale Adebayo, bayan bin matakan maslaha da tsarin adalci.

Source: Facebook
Me yasa Gwamnan jihar Osun ya bar PDP?
A wani rahoton, kun ji cewa kwamishinan yada labarai na Osun, Kolapo Alimi ya ce Gwamna Adeleke ya dade da yanke shawarar raba gari da PDP kafin zaben Osun.
Alimi ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida na PDP a matakin ƙasa ne suka tilasta wa Adeleke raba gari da jam'iyyar, musamman ganin cewa zaben gwamna na kara gabatowa.
Ya ce wa'adin hukumar INEC na karɓar sunayen ’yan takara zai kare a ranar 15 ga Disamba, 2025, amma kuma babu wata alamar masalaha a PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



