"Ba Zan Taba Komawa APC ba," Sanata Ya Yi Kaca Kaca da Gwamnoni 6 a Najeriya
- Sanata Enyinnaya Abaribe ya nesanta kansa da batun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da rinjaye a majalisa
- Dan Majalisar dattawa mai wakiltar Abia ta Kudu ya caccaki gwamnatin Tinubu saboda wahala da kuncin rayuwa da jama'a ke fuskanta
- Abaribe ya yi ikirarin cewa babu ta yadda shugaban kasa, Bola Tinubu zai samu nasara a 2027 domin mutane sun shirya kayar da shi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Sanata ami wakiltar Kudancin Abia a Majalisar Dattawan Najeriya, Enyinnaya Abaribe, ya bayyana cewa ba zai taɓa tunanin sauya sheƙa zuwa APC mai mulki ba.
Kalaman Sanata Abaribe na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnoni, sanatoci da yan Majalisar Wakilai ke ci gaba da tururuwar komawa APC.

Source: Twitter
Da yake jawabi a cikin shirin Politics Today na tashar Channels ranar Litinin, Sanata Abaribe ya ce ba zai taba bin zugar masu sheka zuwa jam'iyya mai mulki ba
A baya-bayan nan, gwamnonin jihohin shida da suka hada da Akwa Ibom, Bayelsa, Enugu, Delta, Ribas da Taraba sun fice daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC.
Sanata Abaribe ya nesanta jansa da APC
“Idan har akwai wanda zai sauya sheƙa zuwa APC, ina ganin ni ne zan zama na ƙarshe-ƙarshe. A ranar da zan sauya sheƙa, hakan na nufin ba wata jam’iyya da ta rage a Najeriya, har da APC kanta.”
“Ku tambayi kanku, a duk jihohin da ake samun sauya sheƙa, me ke faruwa a can? Waɗannan gwamnonin 'yan adawa ne, sun yi aiki tuƙuru wajen adawa da Tinubu a zaɓen 2023.
"Sai kuma ga shi kwatsam sun sauya sheƙa, kuma an mika jam’iyyar a hannunsu. Ya kamata ku yi wa kanki alkalanci a kan haka."
- Sanata Abaribe.
Abaribe ya koka kan kuncin da mutane ke ciki
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Abia ya koka kan tsananin wahala da kuncin rayuwa da ’yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu karkashin mulkin APC.
Abaribe ya yi ikirarin cewa al’ummar Najeriya sun ƙara shiri kuma sun ƙuduri aniyar tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu bai koma kan karagar mulki bayan 2027 ba.

Source: Twitter
Sanatan ya kuma ce tattalin arzikin ƙasa ya durƙushe ƙarƙashin mulkin Tinubu, tare da cewa har yanzu shugaban bai warware matsalar tsaro ba, in ji rahoton Vanguard.
Ya karkare da cewa babu ta hanyar da Shugaba Tinubu zai samu kuri'un da za su sake ba shi nasara a zaben 2027 idan aka duba halin da jama'a ke ciki.
An yi wa Sanata Natasha tayin APC
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti ta bayyana cewa wasu hadimai daga fadar shugaban kasa aun mata tayin sauya sheka APC mai mulkin kasa.
Natasha ta jaddada cewa babu wata barazana ko zuga da za ta sa ta koma APC, tana cewa kasancewarta a jam’iyyar a baya ba ita ce hujjar da zai ta koma jam'iyyar ba.
Ta kuma tabo batun wahalhalu da kalubalen da take fuskanta a rayuwarta, ta yi kira ga mata yan uwanta su ci gaba jajircewa a duk halin da suka tsinci kansu a ciki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

