"Bai Ci Zabe ba a 2023": Sanata Ya Hango Makomar Tinubu a Zaben 2027
- Sanata mai wakiltar Abia ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya, Enyinnaya Abaribe, ya yi tsokaci kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027
- Enyinnaya Abaribe ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai kai labari ba a zaben shekarar 2027 domin 'yan Najeriya sun dawo daga rakiyarsa
- Sanatan ya lissafo abubuwan da za su sanya 'yan Najeriya tabbatar da cewa hugaba Tinubu bai sake samun damar ci gaba da zama a kan madafun iko ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sanatan da ke wakiltar mazabar Abia ta Kudu, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya hango makomar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Sanata Abaribe ya ce ba zai yiwu Shugaba Bola Tinubu ya sake samun nasara a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 ba.

Source: Twitter
Sanata Abaribe ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Abaribe ya ce Tinubu ya fadi zaben 2023
Enyinnaya Abaribe ya kuma yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu bai lashe zaben shekarar 2023 ba.
Sanatan ya ce irin wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu sun kara musu kwarin gwiwar tabbatar da cewa Tinubu bai dawo kan mulki bayan zaben 2027.
Me Abaribe ya ce kan Shugaba Tinubu?
Da yake mayar da martani ga maganar cewa Tinubu bai taba faduwa a zabe ba, Abaribe, sai ya kada baki ya ce:
“Ban yarda da hakan ba. Kowa yana faduwa a zabe, kuma za ku gani idan lokaci ya yi. Zai fadi a 2027 saboda na san abin da ’yan Najeriya ke ji a zahiri.”
“Tinubu bai lashe zaben 2023 ba, kuma kowa ya san hakan. Amma mun ce ba damuwa, an ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, babu matsala."
"Mun amince da shi a matsayin shugaban kasa, amma za mu hadu da shi a filin zabe, sannan mu ga yadda zai hada abin da zai sake ba shi nasara.”

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Malami ya yi sababbin zarge zarge kan shugaban EFCC bayan ci gaba da tsare shi
“Ba zai yi aiki ba, domin a wannan karon kowa a shirye yake. Ba zai zama sanarwa da karfe 3:00 na dare ba kafin mutane su farka da safe. A wannan karon, mutane a shirye suke, mu ma a shirye muke, talakawa ma sun fi kowa shiri.”

Source: Facebook
Sanatan, wanda ya ce tattalin arzikin kasa ya durkushe a karkashin mulkin Tinubu, tare da cewa shugaban kasar bai magance matsalar rashin tsaro ba, ya tambayi inda Tinubu zai samo kuri’un da zai yi nasara a 2027.
Shugaba Tinubu ya yaba wa Nyesom Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kwarara yabo ga Ministan na birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike game da jajircewarsa a gwamnati.
Ya bayyana Wike a matsayin shugaba mai iya shawo kan ƙalubale tare da yin abin da ya dace a duk aikin da aka ba shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
