Da Yawan Shugabannin Siyasa a Najeriya Basu San Matsalolin Jama'arsu Ba, Sanata Abaribe

Da Yawan Shugabannin Siyasa a Najeriya Basu San Matsalolin Jama'arsu Ba, Sanata Abaribe

- Sanata Abaribe na jam'iyyar PDP, yace mafi yawancin shugabannin siyasa basu san matsalolin da jam'arsu ke ciki ba

- Mr. Abaribe, wanda shine shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai yayi ƙauran suna wajen sukar gwamnatin shugaba Buhari

- A baya-bayan nan, Abaribe yayi kira ga shugaba Buhari yayi murabus daga kujerarsa sabida gazawarsa a ɓangaren tsaro

Sanatan Najeriya, Eyinnaya Abaribe, yace mafi yawancin shugabannin siyasa a Najeriya basu san matsalolin mutanen su ba, kamar yadda premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru a Waya

Mr. Abaribe, Sanata mai wakiltar Abia ta kudu, wanda yayi jawabi a wajen ƙadɗamar da littafi ranar Asabar, yace wannan ya faru ne sabida rashin kyaun tsarin matakan jagoranci a ƙasar.

Da Yawan Shugabannin Siyasa a Najeriya Basu San Matsalolin Jama'arsu Ba, Sanata Abaribe
Da Yawan Shugabannin Siyasa a Najeriya Basu San Matsalolin Jama'arsu Ba, Sanata Abaribe Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yayin da yake gabatar da littafin wanda akai ma take da "Tabon zamanin mu akan wariyar launin fata" Mr. Abaribe yace:

"Da yawan shugabannin Najeriya basu san tarihin su ba, tsarin jagoranci an gurɓata shi, shiyasa idan mutane suka dafe madafun iko basa sanin matsalolin dake damun al'ummar su."

Sanatan ya ƙara da cewa matsalar kuma dokar tilasta yin aiki an gurbata ta da batun kabilanci da ya mamaye ƙasar.

Yace: "Babbar matsalar Nigeriya itace ƙabilanci, hakan ya ƙara yawan rashin hukunci a cikin ƙasa."

Mr. Abaribe, Mamba ne na babbar jam'iyyar hamayya PDP, kuma shine shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai, yayi ƙauran suna wajen sukar gwamnatin shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

KARANTA ANAN: Hukumar Yan Sanda Ta Tabbatar da Fafatawa da Yan Bindiga, Ta Bayyana Jami’ai, Yan Bindigan da Aka Kashe

A baya-bayan nan sanatan yayi kira ga shugaban ƙasa Buhari yayi murabus daga muƙaminsa saboda gazawarsa wajen daƙile matsalar tsaron da ƙasar ke fama da ita.

A shekarar 2018, jami'an tsaron farin kaya (SSS) sun kama shi sannan suka rike shi na tsawon wasu yan kwanaki bisa zargin yana da alaƙa da ƙungiyar IPOB.

A lokacin da aka kama shi, sanatan yana daga cikin waɗanda suka tsayawa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, wanda yake fuskantar shari'a a kan ƙoƙarin sa na kafa ƙasar Biafara.

A wani labarin kuma AIB Ta Gano Wani Muhimmin Akwati a Hatsarin Jirgin COAS Attahiru, Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Bincike

Hukumar AIB ta bayyana cewa ta samu nasarar gano akwatin dake naɗar bayanai da murya yayin da jirgi ke tafiya a sama, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Hukumar tace zata sauke duk abinda ke ciki sannn tayi nazari akansu domin gano musabbabin hatsarin jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel