Gwamna Mutfwang Ya Yanke Shawarar Komawa APC, An Ji Abin da Ya Kore Shi daga PDP

Gwamna Mutfwang Ya Yanke Shawarar Komawa APC, An Ji Abin da Ya Kore Shi daga PDP

  • Watakila Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang na dab da sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulkin kasar nan
  • Mai ba gwamnan shawara kan harkokin siyasa, Istifanus Nwansat ya yi bayani kan abin da ya sa Mutfwang ya yanke shawarar koma wa APC
  • Wannan labari ya bayyana ne yayin da APC ke murna bayan Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya karbi katinsa na zama cikakken dan jam'iyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau, Nigeria - Rahotanni sun tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba gwamnan jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang zai sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.

An jima ana yada jita-jitar cewa Gwamna Mutfwang zai koma APC amma gwamnatin jihar Filato na fitowa tana karyata wannan labari.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya goyi bayan wa'adi 1 a mulki, ya fadi amfaninsa

Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang
Gwamnan jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang yana jawabi a gidan gwamnatinsa Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

A makon da ya gabata, Daily Trust ta kawo rahoton da ke tabbatar da cewa gwamnan ya fara tattaunawa da makusantansa na siyasa domin duba yiwuwar raba gari da PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Caleb Mutfwang zai koma APC

Amma a yau Litinin, 15 ga watan Disamba, 2025, Mai ba gwamnan Filato shawara kan harkokin siyasa, Istifanus Nwansat, ya tabbatar da cewa mai gidansa na dab da komawa APC.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa hadimin gwamnan ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Litinin, 15 ga watan Disamba, 2025 a Abuja.

Nwansat ya ce dalilin da ya sa gwamnan ke shirin shiga jam’iyyar APC shi ne saboda ita ce zaɓi mafi aminci da ke da ƙarancin haɗari, la’akari da rikice-rikicen da ke addabar jam’iyyar adawa ta PDP.

Ya bayyana cewa shirin sauya sheƙar Muftwang zuwa APC zai kuma dace da tafiyar siyasa da manufar Shugaba Bola Tinubu a Jihar Filato da ma Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: APC ta yi wa gwamna rijista, ya zama cikakken 'dan jam'iyyar

Dalilin gwamnan Filato na guje wa PDP

Ya ƙara da cewa rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP ya sa jam’iyyar ta zama wuri mara tabbas ga ’yan siyasa da ke son tsayawa takara a zaɓe na gaba.

A cewarsa:

“Bayan nazari da tantance dukkan zaɓin da muke da su, mun fahimci cewa mafi amincin shawara a halin yanzu, wadda ke da ƙarancin haɗari, ita ce mu shiga jam’iyyar APC."
“Shi ya sa gwamnan ke shirin shiga APC. Bugu da ƙari, gwamnan na ganin cewa a matsayinsa na jagora, abu ne mai kyau kuma mai ma’ana ya jagoranci mutanensa su daidaita kansu da shugaban kasa.
“Bisa nazarin da muka yi, duk da yake mu ’yan jam’iyyar PDP ne, amma muna yaba wa da kuma girmama ƙoƙarin da Shugaban Ƙasa ke yi wajen daidaita al’amura."
Gwamnan Filato.
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang da tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Gwamna Kefas ya zama dan jam'iyyar APC

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya yi rajistar zama dan APC a hukumance, inda ya karɓi katin jam’iyya daga shugabannin mazabarsa.

Kara karanta wannan

Ta tabbata, gwamna ya fara laluben jam'iyyar da zai koma Idan ya fice daga PDP

Rahoto ya nuna cewa an yi wa Gwamna Kefas rajista a wani dan karamin taro da aka ahirya a gidan gwamnati da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Gwamna Kefas ya ce rajistar ta zama wajibi domin ya samu cikakken ikon jagorantar harkokin APC da kuma karfafa tafiyar mulki a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262