Ana Zargin EFCC na Kokarin Dakile Shirin Malami na Neman Takarar Gwamna a 2027
- Jam'iyyar hadaka ta bayyana soke belin Abubakar Malami da EFCC ta yi a matsayin wani yunkuri na ruguza shirinsa na siyasa a jihar Kebbi
- Abubakar Malami, tsohon Ministan shari'a na fuskantar bincike daga EFCC kan zargin karkatar da kudin gwamnati a mulkin Muhammadu Buhari
- Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya ce babu wasu hujjoji da suka nuna Abubakar Malami ya karya sharuddan belin da EFCC ta ba shi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam'iyyar hadaka, ADC ta nuna bacin ranta kan matakin da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta dauka na soke belin da ta ba Abubakar Malami.

Kara karanta wannan
"Ba ka cika sharudda 5 ba," EFCC ta maida zazzafan martani, ta yi kaca kaca da Malami
Malami, tsohon Antoni Janar kuma Ministan Shari'a ya fara fuskantar bincike a hukumar EFCC, inda ya shafe kwanaki a tsare kafin a sake shi a matsayin beli.

Source: Twitter
Sai dai kuma daga baya, Daily Trust ta rahoto cewa EFCC ta soke belin da ta bai wa Abubakar Malami, wanda ke da niyyar neman kujerar gwamnan Kebbi a zaben 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ADC ta caccaki EFCC kan belin Abubakar Malami
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ADC, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, ADC ta ce bisa dukkan hujjojin da ke akwai, Malami bai karya ko ɗaya daga cikin sharuddan belin da aka ba shi tun farko ba.
Ya ce soke belin, musamman bayan Malami ya halarci wani gangamin siyasa a Kebbi, na iya sa a fahimci cewa an ɗauki matakin ne domin takaita harkokinsa na siyasa, ba wai domin neman adalci ba.
Jam’iyyar ADC ta jaddada goyon bayanta ga EFCC da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa wajen aiwatar da ayyukansu na bincike da gurfanar da masu laifi.
Amma ta yi gargaɗin cewa nuna son kai ko amfani da bincike a matsayin makamin siyasa kan ’yan adawa na iya rage sahihancin yaƙi da cin hanci da rashawa.
ADC ta zargi EFCC da nuna bangaranci
ADC ta ce hakan na iya jefa hukumomin cikin zargin taimaka wa gwamnati wajen murƙushe ’yan adawa da masu ra’ayi.
“Soke belin Malami bayan ya halarci wani taron siyasa na iya sa mutane tambayar manufar EFCC, da kuma tunanin ɓangaren siyasar da take mara wa baya, ko zarginta da keta dokokin da take ikirarin karewa," in ji ADC.
Jam'iyyar adawan ta nuna damuwa kan wannan salo na EFCC a binciken Abubajar Malami, tana ami cewa hukumar ta sanya siyasa a lamarin.

Source: Facebook
ADC ta kuma yi zargin cewa EFCC ta soke belin Abubakar Malami ne saboda harkokinsa na siyasa wanda ya kunshi shirin neman kujarar gwamnan Kebbi.
A rahoton Tribune, Bolaji Abdullahi ya ƙara da cewa jam’iyyar ADC na tare da Malami, “wanda muke ganin ba shi da laifi har sai wata kotu mai hurumi ta tabbatar da laifinsa."
EFCC ta gurfanar da Chris Ngige
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, kan tuhumar rashawa da almundahana.
Ta gurfanar da shi gaban Mai Shari’a Mariam Hassan na Babbar Kotun Abuja da ke Gwarinpa inda ake tuhunmarsa a kan laifuffukan da suka danganci rashawa.
EFCC na tuhumarsa da karɓar kyaututtukan kuɗi sama da N119m daga wasu kamfanoni yayin da yake rike da mukamin minista.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

