'Ku Yi Likimo', Ganduje Ya Fadawa 'Yan APC Dabarar Nasara a 2027

'Ku Yi Likimo', Ganduje Ya Fadawa 'Yan APC Dabarar Nasara a 2027

  • Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi ‘yan jam’iyyar da su guji zafafa gaba a fafatawar takarar gwamna a jihar
  • A ganawa da ya yi da wasu magoya baya, Ganduje ya bukaci a yi hakuri, a yi dabara da hikima, sannan a yi likimo domin kai wa ga ci
  • Shugaban APC ya ce duk wanda ya samu tikitin takara a mara masa baya, wanda ba zai samu ba idan aka zafafa gaba tun yanzu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga ‘yan jam’iyya da su kauce wa rikici da zafafa gaba yayin shirye-shiryen tunkarar zaben gwamnan Kano.

A wani taro da ya yi da magoya baya, Abdullahi Ganduje, ya jaddada muhimmancin hakuri, dabara da hadin kai domin samun nasara mai dorewa, musamman a zaɓen gwamna.

Kara karanta wannan

Ganduje na fuskantar barazanar shari'a game da yi wa Hisbah kishiya a Kano

Ganduje ya shawarci ƴan APC game da takarar 2027
Tsohon Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Source: Facebook

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na Siyasar Kano, Ganduje ya lissafa dimbin alherin da ke tattare da likimo a siyasance.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Ganduje ya shawarci ƴan APC

A cikin bidiyon, Ganduje ya bayyana yanzu ba lokaci ne da ƴan APC za su rika adawa ko zafafa gaba a tsakaninsu saboda batun takarar gwamna a 2027 ba.

A cewar Ganduje, bai dace a zafafa gaba a takara ba, sai dai a bi a hankali tare da amfani da dabara da hikima da kuma sanin muhimmancin 'likimo.'

Ya ce abin da ake kira “likimo” ba barci ba ne ko rashin iya aiki ba, illa dabara ce da fasaha, hankali da kuma dogaro da Allah domin cimma manufofin da aka saka a gaba.

Ganduje bayyana cewa zafafa gaba da goyon bayan son rai na iya janyo rarrabuwar kai, wanda hakan zai iya lalata burin jam’iyya gaba daya a Kano.

Kara karanta wannan

Sababbin jakadu: Mutane 5 da Tinubu ya nada da suka fuskanci manyan zarge zarge

Tsohon Shugaban APC ya kara da cewa idan aka bari ‘yan takara su gwada kawunan magoya baya, sakamakon hakan shi ne rashin hadin kai da ake bukata domin samun nasara.

Ya jaddada cewa jam’iyya na bukatar zaman lafiya da fahimtar juna domin ci gaba da rike matsayinta a siyasar kasar nan.

Ganduje ya nanata amfanin 'likimo'

Ganduje ya nanata cewa duk dan takara yana da ‘yancin tsayawa takara muddin ya cika sharuddan jam’iyya ba tare da an tsangwame shi ba.

Tsohon gwamnan Kano na son a haɗa kan ƴan APC
Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Facebook

A cewarsa, jam’iyya ta riga ta dauki matsaya cewa duk dan takarar gwamna ko wani mukami, idan aka fitar da wanda ya yi nasara ta hanyar da doka ta tanada, wajibi ne a hada kai a mara masa baya.

"A yi sanda, a yi likimo, ba barci ba ne, ba rashin dabara ba ne, likimo ba rashin hikima ba ne. likimo aiki ne da fasaha, aiki ne da hankali, kuma likimo roko ne a wajen Allah."
"Saboda haka, ina rokon kada ku yadda yan takara su gwada kawunan ku."
"Muna rokonku, kada ku yadda ƴan takara su gwara kawunanku, domin in sun gwara kawunanku, ƙarshen ta ba za a samu hadin kan da ake so ba. Mu kuma muna so a samu hadin kai, duk wanda Allah Ya ba. A taimaka masa."

Kara karanta wannan

Jami'in kwastam da ya yi fatali da cin hancin $50,000 ya samu karin girma

Ganduje ya jawo ce-ce-ku-ce a Kano

A baya, kun ji cewa yunkurin tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya kinkimo aikin da ya jawo ce-ce-ku-ce a jihar.

Shirin Ganduje na kafa sabuwar hukumar Hisbah mai zaman kanta ya haddasa muhawara mai zafi a fadin jihar Kano, inda jama’a ke bayyana damuwa kan illar da hakan.

Tuni mahukunta da masu sharhi ke son a takawa tsohon burki, inda tsohon Kwamishina a gwamnatinsa, Injiniya Muazu Magaji, ya fito fili ya soki shirin .

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng