"A Bayyane Yake": An Hango Abin da Tinubu Zai Yi Wa Shettima a Zaben 2027

"A Bayyane Yake": An Hango Abin da Tinubu Zai Yi Wa Shettima a Zaben 2027

  • Akwai alamun cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na iya ajiye Kashim Shettima a zaben shekarar 2027
  • Jita-jitar ta fito ne 'yan kwanaki kadan bayan FastoEzekiel Dachomo, ya nuna adawarsa kan jagororin kasar nan, inda ya bukaci a cire Shettima
  • Tikitin Muslim-Muslim na zaben shekarar 2023 ya tayar da muhawara kan tasirin da ya yi a Najeriya, yayin da ake ci gaba da zargin muzgunawa Kiristoci

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – Magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun yi hasashen cewa Shugaba Tinubu zai sauke Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben 2027.

‘Yan adawar sun ce suna sa ran Tinubu zai zabi abokin takara wanda ba Musulmi ba, idan har yana son samun nasara a yunkurinsa na sake darewa kan kujerar shugabanci.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Sheikh Zakzaky ya dauki zafi, ya kausasa harshe kan gwamnati

Ana hasashen Tinubu zai sauke Shettima
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima Hoto: @OfficialABAT, @Stanley_nkwocha
Source: Twitter

Daya daga cikinsu mai suna Abdulrasheed Shehu wanda yake hadimin Atiku ne, ya yi hasashen hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi maganganu kan siyasar Najeriya

Wannan hasashe ya zo ne makwanni bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa za a sanya Najeriya a jerin kasashen “da ake kula da su ta musamman".

A cewar shugaban na Amurka za a sanya Najeriya cikin jerin kasashen ne sakamakon kashe-kashen Kiristoci da masu tsattsauran ra’ayin Islama ke yi.

Haka kuma, hakan ya biyo bayan kalaman Rabaran Ezekiel Dachomo, jagoran Cocin Church of Christ in Nations, ya zargi tsarin Muslim-Muslim da cewa tamkar kisan kiyashin Kiristoci ne.

Masu sukar gwamnati sun bukaci Shugaba Tinubu da ya dauki mataki tun kafin zaben 2027, suna mai cewa ci gaba da rike Shettima a matsayin mataimaki na iya jawo masa shan kaye a zabe.

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

Ana hasashen Tinubu zai ajiye Shettima a 2027

Abdulrasheed Shehu ya bayyana ra'ayinsa ne a wani sharhi da ya yi a shafinsa na X kan wani bidiyon da ya nuna ana raba sababbin motocin Hilux da Hummer ga jihohi domin yakin neman zaben 2027.

Hadimin na tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna alamun cewa tuni Tinubu zai sauke Shettima domin nemo wani abokin takara daban a zaben 2027.

"Idan bayan ganin wannan tsari na yakin neman zabe har yanzu ba ka fahimci cewa Shettima ya tafi ba, to kai cikakken dalibin IST mugu ne a ajin farko. Tikitin Muslim-Muslim a 2027? Lokaci ne kawai zai nuna.”

- Abdulrasheed Shehu

Ana hasashen Tinubu zai ajiye Shettima a zaben 2027
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima Hoto: @Stanley_nkwocha
Source: Twitter

Haka zalika, Abubakar Yunusa, wani jigo kuma mai goyon bayan Atiku a jam’iyyar ADC ya yi irin wannan ikirari a ranar Juma’a, 12 ga Disamba a shafinsa na X.

Ya wallafa hoton Kashim Shettima tare da rubuta:

“Tinubu zai sauke Shettima.”

Shettima ya kaddamar da tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya kaddamar da shirin ba da tallafi ga 'yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Yadda Abdullahi Ramat ya rasa kujerar shugabancin hukumar NERC

Kashim Shettima ya ce gwamnatin Tinubu na goyon bayan ci gaban jama’a kai tsaye domin inganta al'umma.

Mataimakin shugaban kasar ya ce tsarin tallafin zai ƙara yawan sana’o’i, ya bunƙasa kuɗaɗen shiga, ya ƙarfafa matasa da mata, tare da rage dogaro da wasu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng