Magana Ta Kare: APC Ta Yi Wa Gwamna Rijista, Ya Zama Cikakken 'Dan Jam'iyyar
- Daga canza sheka, Gwamna Sim Fubara na jihar Ribas ya yi rijista kuma ya karbi katin zama cikakken dan jam'iyyar APC ranar Juma'a
- Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan gwamnan ya sanar da cewa shi da magoya bayansa sun fice daga PDP zuwa APC mai mulki
- Shugaban APC na kasa, Yilwatda Nentawe ya taya Gwamna Fubara murna, yana mai cewa hakan zai kawo zaman lafiya a siyasar jihar Ribas
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya karbi katin zama cikakken ɗan jam’iyyar APC a hukumance bayan ya sanar da barin PDP.
Gwamna Fubara ya zama cikakken dan APC ne bayan an masa rijistar zama mamba tare da mika masa kati a fadar gwamnatinsa da ke Fatakwal yau Juma'a.

Source: Facebook
Gwamna Simi Fubara ya karbi katin APC
Tashar Channels ta ce shugaban APC a jihar, Tony Okocha, wanda ya wakilci Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ne ya mika wa Gwamna Fubara katin zama mamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi, Gwamna Fubara ya ce shigarsa APC wani mataki ne da ya dauka domin ƙarfafa hadin kai da cigaba a Jihar Ribas.
Ya bayyana cewa ya zama dole ya hada inuwa daya da jam’iyyar da ke mulkin ƙasa domin tabbatar da zaman lafiya, daidaiton siyasa da kuma samun ayyukan ci gaba a jihar.
Fubara ya jaddada goyon baya ga Tinubu
Fubara ya ce goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ba kawai batun siyasa ba ne, godiya ce bisa yadda shugaban kasa ya tsaya tsayin daka domin ganin gwamnatinsa ta tsira lokacin rikicin siyasar jihar.
Gwamnan ya kara da cewa yanzu da Ribas ta hade a ƙarƙashin jam’iyya daya da gwamnatin tarayya, ya fi sauƙin gina jam’iyyar da kuma tunkarar zaben 2027 cikin kwanciyar hankali.
Ya tabbatar wa jagorancin APC na ƙasa cewa Ribas za ta kasance garkuwar jam’iyyar, tare da ɗaukar nauyin duk abin da ya dace domin ƙarfafa ayyukan jam’iyya a fadin jihar.
Ya gode wa magoya baya da shugabannin da suka tsaya masa, tare da kira gare su da su kara jajircewa domin shiga sabon babi na karfafa siyasa da ci gaban jihar.

Source: Twitter
Shugaban jam'iyyar APC ya taya Fubara murna
A nasa jawabin, Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ta bakin wakilinsa, Tony Okocha, ya taya gwamnan murna bisa wannan “mataki da ya dauka mai cike da jarumta."
Farfesa Yilwatda ya ce dalilan da suka sa gwamnan ya sauya sheka suna da tushe kuma suna da amfani ga jihar, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Ya kara da cewa zuwan Fubara cikin APC ya bude sabon babi na hadin kai a siyasar Ribas, inda manyan ’yan siyasa za su yi aiki tare ƙarƙashin inuwa daya.
Gwamna Fubara ya yi wa Bola Tinubu alkawari
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya jaddada cikakken goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali kan zaman lafiya, cigaban jiha gaba ɗaya, da kuma tafiya tare ta fuskar siyasa da fadar shugaban kasa.
Fubara ya kuma sha alwashin cewa zai tabbatar Shugaba Tinubu da APC sun lashe kuri'un jihar Ribas a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


