PDP ba Za Ta Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomin Jihar Borno ba, Ta Kawo Dalilai 2

PDP ba Za Ta Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomin Jihar Borno ba, Ta Kawo Dalilai 2

  • Jam'iyyar PDP ta ce ba za ta shiga zaben kananan hukumomi da hukumar zabe ta BOSIEC za ta gudanar a Borno a ranar Asabar ba
  • PDP ta ce BOSIEC ta gaza ba jam'iyyun adawa tabbacin cewa za ta gudanar da sahihin zabe, don haka tana zargin ba za ta yi adalci ba
  • Yayin da PDP ta kaurace, ita kuwa APC mai-ci ta tabbatar da shirin shiga zaben, tana mai cewa ta kammala dukkan shirye-shirye a kai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno – Jam’iyyar PDP a jihar Borno ta sanar da cewa ba za ta shiga zaɓen ciyamomin jihar da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, 13 ga Disamba, ba.

Jam'yyar PDP ta dauki wannan mataki ne bayan da ta yi zargin cewa hukumar zaɓen jihar ba za ta yi adalci ba, kuma an tsuga kudi a takardun neman tsayawa takara.

Kara karanta wannan

NLC: 'Yan kwadago sun saka ranar zanga zanga a jihohi 36 da Abuja

Jam'iyyar PDP ta ce tana ganin ba za a yi mata adalci ba a zaben kananan hukumomin Borno
PDP ta gudanar da taron jin ra'ayi na shugabanninta na kasa da na jihohi a Abuja. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

PDP ta fasa shiga zaben ciyamomi a Borno

Matsayar jam'iyyar adawar na kin shiga zaben ciyamomin Borno na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na jihar, Amos Adziba, ya fitar a ranar Juma’a,in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Amos Adziba ya rahoto cewa PDP ta yanke wannan hukunci ne a taron kwamitin zartarwa na jihar (SEC) da aka gudanar a birnin Maiduguri.

Sanarwar mai taken “Dalilin da ya sa muka kaurace wa zaɓen kananan hukumomin Borno” ta zargi hukumar zaɓen jihar, watau BOSIEC, da kasa bai wa jam’iyyun adawa kwarin gwiwa kan cewa za ta gudanar da sahihin zaɓe cikin adalci.

Dalilan PDP na kin shiga zaben Borno

Sanarwar ta ce:

“Jam’iyyar PDP a jihar Borno na sanar da cewa ba za ta shiga zaɓen kananan hukumomin da aka shirya yi a ranar 13 ga Disamba, 2025 ba saboda tsadar fom din takara, tare da matsalar rashin amincewa da hukumar zaɓe.”

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi takaici, ta fadi yadda ta rasa gwamnonin jihohi 2

A wata takarda da aka fitar bayan taron, Adziba ya lissafo dalilai da dama da suka sa PDP ta janye daga shiga zaben, ciki har da rashin amincewa da BOSIEC da kuma jam’iyya mai mulki ta APC.

Adziba ya ce:

“BOSIEC ba ta ba jam’iyyun adawa hujjojin da za su gamsar da su cewa za ta gudanar da sahihin zabe ba.
“PDP na zargin cewa hukumar zaɓen jihar ba ta kula da halin matsin tattalin arzikin da jama’a ke ciki ba, ganin yadda ta kakaba tsada kan fom ɗin takara.”
Jam'iyyar PDP ta ce ba za ta shiga zaben kananan hukumomi a Borno ba.
Taswirar jihar Borno, inda aka shirya yin zaben kananan hukumomi a ranar 13 ga Disamba, 2025. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ita APC ta ce za ta shiga zaben

Wani ƙarin korafi da jam’iyyar ta yi shi ne gazawar gwamnatin jihar na gyara dokar zaɓe, wanda zai ba da damar a sanar da sakamkon zaben kansiloli a sakatariyoyin gunduma, da na ciyamomi a sakatariyoyin kananan hukumomi.

A watan Oktoba, jaridar Punch ta ruwaito cewa jam’iyyar APC ta bayyana shirinta na shiga zaɓen. Shugaban jam’iyyar a jihar, Bello Ayuba, ya ce sun kammala duk shirye-shiryen da ake bukata.

Ayuba ya ce:

“Mun rubuta wa hukumar zabe cewa jam’iyyarmu za ta shiga zaɓen kananan hukumomi. Mun sanar da dukkan gundumomi da magoya bayanmu cewa za mu shiga zaben.”

Kara karanta wannan

Jita jita ta ƙare: Mataimakin gwamna da aka garzaya da shi asibiti ya mutu

Mace ta zama ciyaman a Borno

A wani labari, mun ruwaito cewa, a karon farko a tarihi, an samu macen da ta zama zababbiyar shugabar ƙaramar hukuma guda a jihar Borno da ke Arewacin Najeriya.

Hukumar zaɓe ta ayyana Hajiya Inna Galadima ta jam'iyyar APC mai mulki a jihar a matsayin wadda ta lashe zaɓen karamar hukumarJere a Borno.

Baturen zaɓen ƙaramar hukumar, Farfesa Mohammed Konto, shi ne ya ayyana Galadima, tsohuwar kwamishina da mai bada shawara a matsayin wacce ta ci zaɓen.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com