Jam'iyyar PDP Ta Yi Takaici, Ta Fadi yadda Ta Rasa Gwamnonin Jihohi 2
- Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ta bayyana takaici game da yadda ta yi sakaci wajen rasa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke
- Kakakin Yada Labarai na PDP na kasa, Ini Ememobong, ya amince cewa jam’iyyar ta nuna gazawa musamman a kan rikicin Osun
- Sai dai ya wanke PDP daga tunkuda Siminalayi Fubara na jihar Ribas zuwa APC, inda ya ce shi ya jefa kansa a cikin matsala da kansa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana takaicin ficewar Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, da ta Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara.
Jam'iyyar ta dora alhakin rasa manyan 'ya'yanta a kan gazawar jagorancin cikin gida da kuma rikice-rikicen da ba a magance tun da wuri ba, ba wai matsin lamba daga waje ba.

Source: Twitter
Da yake magana a shirin The Morning Brief na Channels TV, Kakakin Yada Labarai na PDP na kasa, Ini Ememobong, ya amince cewa jam’iyyar ta nuna gazawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda PDP ta rasa gwamnoni a jihohi 2
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Ini Ememobong ya ce PDP ta gaza daukar mataki da wuri kan alamu da suka bayyana tun farko, musamman game da lamarin Adeleke.
Ya bayyana cewa:
“Adeleke mutumin da ya fada cikin yanayi ne, kuma wadanda suka kirkiri yanayin wasu ne a cikin jam’iyya. Amma ba a dauki matakin da ya dace da wuri ba. Idan jagorancin jam'iyya ya tsaya tsayin daka tun 2023, da wannan sakamakon ba zai kasance haka ba.”
Ememobong ya ce shugabanni ya sa aka yi tunanin rikicin Osun zai lafa da kansa, saboda haka ba a dauki matakan da suka dace ba wajen kashe wutar.
PDP ta yi takaicin rasa Gwamna Fubara
Game da rikicin Ribas, Ememobong ya ce lamarin Fubara daban yake. Ya jaddada cewa gwamnan ne kansa ya hana jam’iyya shiga matsalar jihar tun farko duk da cewa shi da kansa ya zabi zama dan takarar PDP.

Source: Facebook
Kakakin PDP ya ce sun shiga damuwa ne lokacin da Fubara ya fito fili yana cewa ba ya jin tsaro cikin jam’iyyar, alhali a baya ya kira rikicin “na uba da ɗa.”
Dangane da korafin Fubara cewa PDP ta bar shi, Ememobong ya ce gwamnan ya ki amincewa da duk kokarin jam’iyyar na kare shi.
Ya kuma ambaci damuwar manyan lauyoyi kan rashin saka rana da Kotun Koli ta yi a karar da gwamnoni na PDP suka shigar.
Duk da ficewar gwamnonin biyu, Ememobong ya musanta cewa PDP ta karye, inda ya ce da karfinta za ta tunkari babban zaben 2027 mai zuwa.
Wasu gwamnonin jam'iyyar PDP sun sauya sheka
A baya, kun ji cewa duniya siyasar Najeriya ta sake daukar sabon salo bayan Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Biyo bayan sauya shekar Gwamna Fubara, yanzu PDP ta rasa gwamnoni biyar a cikin shekara biyu kacal, inda mafi yawansu suka sauya sheka zuwa jam'iyyar da ke mulki, wato APC.
Sauran gwamnonin da suka sauya sheka sun hada da Peter Mbah na Enugu, Douye Diri na jihar Bayelsa, Gwamnan Delta Sheriff Oborevwori, gwamnan Akwa Ibom Umo Eno da gwamnan Osun Ademola Adeleke.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


