Mutanen Kano Sun Ajiye Abba a Gefe, Sun Ce Barau Suke So a 2027

Mutanen Kano Sun Ajiye Abba a Gefe, Sun Ce Barau Suke So a 2027

  • Daruruwan shugabanni daga Bagwai da Shanono sun kai ziyarar nuna goyon baya ga Barau Jibrin a birnin tarayya Abuja
  • Tawagar ta bayyana aniyar mara wa Bola Tinubu baya a 2027 tare da kira ga Barau da ya tsaya takarar gwamnan jihar Kano
  • Shugabannin sun yaba da ayyukan da aka kawo yankunansu, suna cewa za su tashi tsaye wajen ganin APC ta samu nasara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja — Manyan shugabanni, dattawa, matasa, mata, ‘yan kasuwa da manoma daga ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono na jihar Kano sun kai ziyarar nuna goyon baya ga Sanata Barau Jibrin.

Ziyarar, wacce Hon. Farouk Lawan ya jagoranta, ta nuna cikakken amincewa da jagorancin gwamnatin Bola Tinubu da manufar Renewed Hope.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume da Oshiomhole sun gwabza a majalisa kan tantance Omokri

Barau tare da 'yan Kano a Abuja
Mutanen Kano na gaisawa da Barau da ua shiga dakin taro a Abuja. Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Sanata Barau ya wallafa a Facebook cewa kalaman da suka fito daga bakin wakilan yankin sun ƙara masa ƙwarin guiwa, musamman yadda suka bayyana gamsuwa da ayyukan da gwamnatin tarayya da na ofishinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana so Barau ya nemi gwamnan Kano

Wakilan sun nuna godiya bisa yadda gwamnatin Tinubu ta shawo kan matsalolin tsaro a yankunansu da kuma ayyukan raya ƙasa da dama da aka kaddamar a Bagwai da Shanono.

Sun kuma bayyana aniyar su ta yin aiki tukuru wajen ganin an sake zaben Tinubu a karkashin jam'iyyar APC a 2027.

Hon. Ahmed Muhammad Kadamu ya ce:

“A 2027, Bagwai da Shanono za su zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa, kuma Barau gwamnan Kano. Mutanen Kano suna bayanka.”

Shi ma Hon. Farouk Lawan ya ce:

“Sakonmu zuwa fadar shugaban kasa abu guda ne; a 2027, Tinubu ne shugabanmu, kuma Kano ta na tare da Sanata Barau.”

An jaddada goyon bayan Barau a Kano

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

Wani hadimin shugaban kasa, Alhaji Mahmoud Danlarabawa, ya jaddada cewa Kano na da cikakken goyon bayan gwamnati wajen warware matsalolin da ta ke fuskanta.

Ya ce:

“Kano ta Tinubu ce, ta Barau ce, kuma ta mu ce duka.”

Sanata Barau ya gode wa al’ummomin Bagwai da Shanono bisa biyayya da goyon bayan da suke ba shi tsawon shekaru.

Ya kuma yi jaje kan matsalolin tsaro da suka faru a kwanakin baya, yana mai cewa suna aiki tare da hukumomin tsaro don magance lamarin.

Maganar Sanata Barau kan makomar Kano

Barau ya koka da yadda Kano ta rasa matsayinta na zama cibiyar kasuwanci ta biyu bayan Legas, yana mai cewa akwai bukatar dawo da martabar jihar.

Sanatan ya kuma ƙara da cewa Bagwai da Shanono mutanensa ne, kuma ya na da cikakkiyar niyya wajen ci gaba da kare muradunsu da raya yankunansu.

Barau tare da mutanen da suka ziyarce shi
Sanata Barau yayin karbar mutanen Kano a Abuja. Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Ya bayyana cewa suna fatan Kano ta dawo hayyacinta game da rushewar ilimi, rashin ruwan sha, karayar tattalin arziki da matsalolin tsaro.

Gargadin Ganduje kan batun takara a Kano

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Sanata Ndume ya yabi Shugaba Tinubu, ya ba gwamnoni shawara

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi 'yan APC kan ayyana dan takara.

Abdullahi Ganduje ya ce bai kamata 'yan APC su fara bayyana wanda suke so ya fito takarar gwamnan jihar ba a halin yanzu.

Tsohon shugaban APC ya ce lokacin bayyana dan takara bai yi ba tukuna, kuma hakan zai kawo rabuwar kawuna a jam'iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng