Bayan Komawa APC, Gwamna Fubara Ya Yi Wa Tinubu Alkawari kan Zaben 2027

Bayan Komawa APC, Gwamna Fubara Ya Yi Wa Tinubu Alkawari kan Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya nuna cikakken goyon bayansa ga tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027
  • Fubara wanda ya koma APC cikin 'yan kwanakin nan, ya nuna cewa gwamnatinsa tana aiki tukuru a jihar Rivers
  • Gwamnan ya kuma yi kira da babbar murya ga mutanen jihar kan abin da ya kamata su yi wa Mai girma Bola Tinubu

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi magana kan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Gwamna Fubara ya sake jaddada cewa a shirye yake ya goyi bayan sake zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Gwamna Fubara ya nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sir Siminalayi Fubara
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce Gwamna Fubara ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Disamban 2025, yayin kaddamar da titin Egbeda–Omerelu, bikin farko da ya bayyana a bainar jama’a tun bayan komawarsa jam’iyyar APC a farkon makon nan.

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Fubara na son zaman lafiya

Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa ta mayar da hankali kan zaman lafiya, cigaban jiha gaba ɗaya, da kuma tafiya tare ta fuskar siyasa da fadar shugaban kasa.

Yayi kira ga ’yan jihar da su zauna lafiya, inda ya ce cigaba ba zai samu a wajen da ake rigima ba, jaridar The Nation ta dauko labarin.

“Kowa ya yi kokari a samu zaman lafiya, ba za mu samu ci gaba a wurin da ake rigima da rarrabuwar kai ba. Cigaba ba zai zo wa mutanenmu ba idan akwai rashin jituwa."

- Gwamna Siminalayi Fubara

Gwamna Fubara ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da samar ci gaba wanda zai shafi kowane yanki.

“Duk abin da ya dace na yi domin a samu cikakken zaman lafiya, zan ci gaba da yi. Mutanen Rivers, cigaba zai isa kowane lungu da sako na jihar nan."
"Za mu tabbata mun taba kowane bangare. Wannan alkawari ne, kuma za mu cika shi.”

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Yadda Abdullahi Ramat ya rasa kujerar shugabancin hukumar NERC

- Gwamna Siminalayi Fubara

Fubara ya yi shagube ga 'yan adawa

Gwamna Fubara ya ce bikin kaddamar da titin ya zama dole don karyata jita-jitar da ke cewa gwamnatinsa ba ta yin ayyuka a jihar.

“Mun zo nan ne don mu nuna wa duniya cewa duk da kalubalen da muke ciki, hankalinmu yana kan kawo wa jama’a romon dimokuradiyya. Za mu ci gaba da yi wa mutanenmu aiki cikin mutunci da girmamawa.”

- Gwamna Siminalayi Fubara

Gwamna Fubara ya ce gwamnatinsa na aiki a Rivers
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara a ofis Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Me Fubara ya ce kan tazarcen Tinubu?

A yayin da yake magana kan siyasar 2027, Gwamna Fubara ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Shugaba Tinubu tare da kira ga mutanen Rivers su marawa shugaban kasa baya.

“Mun riga mun san matsayinmu, mun tabbatar cewa cigaba ya zagaye ko’ina a Rivers, kuma hanyar da za mu bi ita ce goyon bayan shugaban kasa."
"Mun fara, za mu mara wa sauran kungiyoyi baya domin mu tabbatar mun kawo nasara ga Shugaba Tinubu a 2027.”

Kara karanta wannan

Jami'in kwastam da ya yi fatali da cin hancin $50,000 ya samu karin girma

- Gwamna Siminalayi Fubara

PDP ta ragargaji Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi wa Gwamna Siminalayi Fubara martani kan sauya sheka zuwa APC.

Jam’iyyar PDP ta bayyana sauya shekar da gwamnan na jihar Rivers ya yi zuwa jam’iyyar APC a matsayin rauni da ya jawo wa kansa matsala.

PDP ta ce duk wanda ya bi labarin rikicin siyasar Rivers zai gane cewa gwamnan ne ya jagoranci kansa zuwa halin da ya ke ciki a yanzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng