Shugaban Gwamnonin PDP Gaba Daya na Shirin Ficewa daga Jam'iyyar? Gaskiya Ta Fito

Shugaban Gwamnonin PDP Gaba Daya na Shirin Ficewa daga Jam'iyyar? Gaskiya Ta Fito

  • Gwamnan Bauchi, Sanata Bala A. Mohammed ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa yana shirin fita daga PDP ya koma PRP
  • Bala ya kuma soki kalaman da PRP ta yi, yana mai cewa ba zai bari karya da kage su dauke masa hankali daga kawo cigaba a Bauchi ba
  • Gwamnatin Bauchi ta ce Gwamna Bala na taka muhimmiyar rawa wajen warware rikicin PDP kuma bai taba tunanin sauya sheka ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - A 'yan kwanakin nan ne aka fara yada wata jita-jita cewa shugaban gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed na shirin komawa PRP.

Jim kadan bayan bullar wannan jita-jita, jam'iyyar PRP ta fito ta bayyana cewa ko da labarin ya zama gaskiya, ba za ta karbi Gwamna Bala ba.

Kara karanta wannan

PRP ta rufe kofa da aka fara rade radin Gwamna Bala zai fice daga PDP

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamna Bala Mohammed lokacin da aka ba shi wata lambar yabo a gidan gwamnatin Bauchi Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Da gaske Gwamna Bala zai koma PRP?

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa Gwaamnan Bala Mohammed, ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa yana shirin komawa jam’iyyar PRP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mukhtar Gidado, ya fitar ranar Laraba, gwamnatin Bauchi ta yi kakkausan raddi kan jita-jitar da ta kira “ƙarya da kage, da suka saɓa wa hankali."

Sanarwar ta ce:

"Akwai wani rubutu da aka danganta wa PRP na cewa ba za ta karbi Gwamna Bala zuwa cikin jam’iyyar ba. Wannan magana karya ce kuma tunanin marubuci ne kawai.”

Gwamnati Bauchi ta ce babu wani lokaci da gwamnan ya yi tunanin barin PDP, balle kuma shirin komawa wata jam’iyya ta daban.

Gwamnan Bauchi na kokarin saita PDP

A cewar Mukhtar Gidado:

“Kowa ya san Gwamna Bala na sahun gaba wajen ceto PDP daga rikice-rikicen da wasu ke ƙulla wa domin maida Najeriya ƙarƙashin mulkin jam’iyya ɗaya.”

Kara karanta wannan

Fubara, Adeleke da wasu gwamnoni 3 da suka fice daga jam'iyyar PDP a shekara 2

Ya kara da cewa Gwamna Bala ya gwada jarumtaka da cancantarsa, musamman ganin cewa ya doke PRP sau biyu a manyan zaɓe da suka gabata a jihar Bauchi.

A cewarsa, yanzu Bauchi na da martaba a Arewacin Najeriya saboda shugabancin Bala Mohammed da ya mayar da hankali kan raya ƙauyuka, tsara birane, ci gaban masana’antu, gina tituna da taimakon talakawa.

Gwamna Bala Mohammed.
Shugaban gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed
Source: Facebook

Gwamnati ta jaddada cewa duk da ƙalubalen da PDP ke fuskanta, gwamnan zai ci gaba da jajircewa wajen daga kimar Bauchi, ba tare da ya bari sharri ko kazamar siyasa ta dauke masa hankali ba.

Sanarwar ta ƙare da cewa gwamnan na da ‘yancin zabar hanyar siyasa da zai bi a nan gaba, idan lokacin ya yi, amma ba zau fada tarkon matsin lamba da masu sharrin siyasa ba, in ji Leadership.

Tsagin Wike ya kori gwamnan Bauchi daga PDP

A baya, kun ji cewa tsagin jam’iyyar PDP da ke goyon bayan Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ta sake tabbatar da korar wasu manyan ’yan siyasa 18.

Daga cikin wadanda aka kora akwai Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed; Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal; da Gwamnan Oyo, Seyi Makinde.

Kara karanta wannan

"Ka jefa kanka a matsala": PDP ta zargi Gwamna Fubara da rauni bayan komawa APC

Bangaren PDP na Wike ya ce abin takaici ne yadda mutanen da aka kora ke ci gaba da magana da aikata abubuwa a madadin jam’iyyar hamayyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262