Zaben 2026: Gwamna Adeleke Ya Samu Tikitin Takara bayan Ya Fice daga Jam'iyyar PDP

Zaben 2026: Gwamna Adeleke Ya Samu Tikitin Takara bayan Ya Fice daga Jam'iyyar PDP

  • Jam'iyyar Accord ta bayyana Gwamna Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani da aka gudanar yau Laraba
  • Hakan ya sa Adeleke ya zama dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin inuwar jam'iyyar Accord a zaben shekarar 2026
  • Tuni dai jam'iyyar Accord ta bai wa Gwamna Adeleke shaidar zama halastaccen dan takararta a zaben gwamnan Osun na gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Gwamna Ademola Adeleke ya shiga jam'iyyar Accord da kafar dama yayin da ake shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Osun a shekarar 2026.

Idan ba ku manta ba a jiya Talata, 9 ga watan Disamba, 2025, Gwamna Adeleke, wanda ya fita daga PDP a farkon watan Nuwamba, 2025, ya sanar da shiga jam'iyyar Accord.

Gwamna Adeleke.
Gwamnan jihar Osun, Adelmola Adeleke a wurin zaben fitar da gwani na jam'iyyar Accord Hoto: Afebio Abiodun
Source: Facebook

Gwamna Adeleke ya lashe tikitin Accord

Kara karanta wannan

PRP ta rufe kofa da aka fara rade radin Gwamna Bala zai fice daga PDP

The Nation ta ruwaito cewa awanni 24 bayan haka, Gwamna Adeleke ya samu nasarar zama dan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar Accord a zaben Osun 2026 da ke tafe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ademola Adeleke ya samu tikitin takarar jam'iyyar Accord ne a zaben fitar da gwanin da aka gudanar yau Laraba, 10 ga watan Disamba, 2025 a Osogbo.

Gwamna Adeleke, wanda shi kaɗai ne ya tsaya takara a zaben fitar da gwanin, ya samu nasara da da kuri’u 145 daga cikin 150 da wakilan jam'iyyar suka kada.

Sakamakon zaben fitar da gwani na Accord

Sakataren kwamitin gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar Accord, Abdulazeez Salaudeen, ne ya bayyana sakamakon zaben bayan wakilai sun kammala kada kuri'a.

Abdulazeez Salahudeen, wanda ya sanar da sakamakon, ya ce wakilai 150 ne suka kada kuri’a, inda Adeleke ya samu 145, yayin da kuri’u 5 suka lalace.

Tun farko, kwamitin tantance ’yan takara na jam’iyyar, ƙarƙashin jagorancin Elder Ibe Thankgod, ya tantance Adeleke kuma ya bayyana shi a matsayin ɗan takara guda ɗaya da ya cika dukkan sharuddan jam’iyyar Accord.

A yayin kada kuri’ar, wakilai biyar daga kowace daga cikin kananan hukumomi 30 da aka tantance tun farko ne suka jefa kuri’a, kuma jami’an hukumar INEC sun halarci wurin domin sa ido.

Kara karanta wannan

'Ba APC ba ce': Gwamna Adeleke ya shiga sabuwar jam'iyya bayan ficewa daga PDP

Gwamna Adeleke na Osun
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun da tutar jam'iyyar Accord Hoto: @Adeleke01
Source: Twitter

Jam'iyyar Accord ta ba Adeleke satifiket

Shugaban jam’iyyar Accord na ƙasa, Maxwell Mgbudem, ya mika wa Adeleke takardar shaidar lashe zaben, tare da taya shi murna, kamar yadda Leadership ta rahoto.

A jawabin karɓar nasara, Gwamna Adeleke ya gode wa kwamitin zabe da ’yan jam’iyyar Accord baki ɗaya saboda ba shi damar samun tikiti a zaben gwamna mai zuwa.

Dalilin Gwamna Adeleke na barin PDP

A wani labarin, kun ji cewa kwamishinan yaɗa labarai na jihar Osun, Kolapo Alimi, ya bayyana dalilin da ya sa Gwamna Ademola Adeleke ya fita daga jam'iyyar PDP.

Alimi ya ce ba haka kurum gwamnan ya bar jam'iyyar ba face sakamakon rikice- rikicen cikin gida da suka dade suna faruwa a PDP.

A cewar Kolafo Alimi, Gwamna Adeleke ya dade da yanke shawara, kuma ya rubuta takardar barin jam’iyyar PDP tun watanni da suka gabata.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262