Fubara, Adeleke da Wasu Gwamnoni 3 da Suka Fice daga Jam'iyyar PDP a Shekara 2

Fubara, Adeleke da Wasu Gwamnoni 3 da Suka Fice daga Jam'iyyar PDP a Shekara 2

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya sauya sheka daga PDP zuwa APC bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa, Abuja
  • Ficewar Fubara ta kara dagula siyasar PDP wadda tuni ta rasa gwamnoni biyar, kuma ake sa ran wasu biyu za su bar ta nan da Janairun 2026
  • Legit Hausa ta jero gwamnonin PDP da suka sauya sheka tun daga 2023, tare da jero sauran gwamnoni shida da suka rage a jam’iyyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC, wanda hakan ya kara dagula rikicin da jam’iyyar adawa ta PDP ke fama da shi.

Fubara, wanda ya kasance ɗaya daga cikin gwamnonin da suka rage a PDP, ya bayyana sauya shekarsa ne a taron da ya gudanar a ranar Talata, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Ka jefa kanka a matsala": PDP ta zargi Gwamna Fubara da rauni bayan komawa APC

JAm'iyyar PDP ta rasa gwamnoni fiye da 5 daga 2023 zuwa 2025
Kungiyar gwamnonin PDP sun yi taro kafin wasu daga cikinsu su bar jam'iyyar. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

A taron, jaridar Punch ta rahoto Fubara ya na cewa ziyarar da ya kai wa Shugaba Bola Tinubu, a ranar Litinin, “ba ta da nasaba da bukatarsa ta kashin kai, sai dai don tattaunawa kan bukatun jihar.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Fubara:

“Ba zan so in kara yin wani kuskure ba. Na samu izinin barin PDP saboda babu kariya a jam’iyyar, kuma ta gaza gare ni daga rigingimun jihar da aka yi. Don haka mun yanke hukuncin komawa APC.”

Jerin gwamnonin PDP da suka bar jam’iyyar

Sauyin shekar Fubara ya kara yawan gwamnonin da suka fice daga PDP zuwa APC tun bayan 2023, kamar yadda rahoton The Nation ya nuna.

Yawancin gwamnonin da suka fice daga PDP, su danganta sauya shekarsu da bukatar da suke ganin akwai na “hada kai da gwamnatin tarayya don kawo ci gaba” a jihohinsu.

Gwamnonin da suka bar PDP zuwa APC su ne:

1. Jihar Enugu - Peter Mbah

Kara karanta wannan

Mutfwang: Gwamnan PDP da ya gana da Tinubu zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

A ranar 14 ga Oktoba, 2025, gwamnan Enugu, Peter Mbah, ya sanar da komawarsa APC. Ya ce hakan na da nasaba da bukatar “hada hannu da gwamnatin tarayya don samar da ayyukan ci gaba ga mutanen Enugu.”

2. Jihar Bayelsa - Douye Diri

Gwamna Douye Diri ya fice daga PDP a watan Nuwamba bayan dogon lokaci ana yada jita-jitar sauya shekarsa.

Douye Diri, a wani taron majalisar zartarwar jihar ya ce ya yanke shawarar barin PDP bayan tattaunawa mai zurfi, kuma 'yan majalisar dokokin jihar 23 za su bi sahunsa.

3. Jihar Delta - Sheriff Oborevwori

A ranar 23 ga Afrilu, 2025, gwamna Sheriff Oborevwori ya koma APC, bisa bayanansa don “karfafa ci gaban jihar da kare amincin jama’a.”

4. Jihar Akwa Ibom - Umo Eno

Gwamna Umo Eno ya fice daga PDP a ranar 6 ga Yuni, 2025, yana mai cewa ba ya ganin jam’iyyar za ta iya ci gaba da samun nasara a siyasar kasa.

Jaridar Leadership ta rahoto kwamishinan watsa labaran jihar, Charles Aniagwu, ya ce matakin gwamnan yana da nasaba da kaunarsa ga jihar, inganta tsaro da walwalar al'umma.

5. Gwamnan Osun ya koma Accord

Kara karanta wannan

Awanni 24 bayan ganawa da Tinubu, Gwamna Fubara ya fice daga PDP zuwa APC

A ranar 2 ga Disamba, 2025, gwamnan Osun, Ademola Adeleke, aka ji ya yi murabus daga PDP saboda rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinye wa.

Legit Hausa ta rahoto cewa Gwamna Adele ya kuma sanar da shigarsa jam'iyyar Accord Party, wadda ya ce ta fi dacewa da manufofinsa, kuma a nan zai yi takarar gwamna a zaben 2026.

Gwamnonin da suka ayyana shirin barin PDP

A Plateau, magoya bayan PDP daga kananan hukumomi 17 sun gudanar da gangami suna matsa wa Gwamna Caleb Mutfwang lamba ya koma APC.

Legit Hausa ta rahoto cewa Gwamna Mutfwang ya kammala kaso 90 na barin PDP zuwa APC, inda ake sa ran zai sauya shekar kafin karshen Janairu, 2026.

A Taraba kuwa, Gwamna Agbu Kefas ya kammala shirinsa na komawa APC, inda aka tabbatar za a yi bikin shigar sa a Janairu 2026.

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Taraba ya ce gwamnan ba zai sauya sheka a shekarar nan saboda karancin lokaci, dole sai watan gobe, kamar yadda muka ruwaito.

Gwamnonin PDP da dama sun fice daga jam'iyyar daga 2023 zuwa 2025
Kungiyar gwamnonin PDP sun yi taro kafin wasu daga cikinsu su sauya sheka daga 2023 zuwa 2025. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Facebook

Gwamnonin da suka rage a PDP (Disamba 2025)

Kara karanta wannan

Ganduje ya hango matsalar da APC za ta iya shiga a Kano kan ayyana dan takara

  • Ahmadu Fintiri – Adamawa
  • Bala Mohammed – Bauchi
  • Caleb Mutfwang – Plateau
  • Agbu Kefas – Taraba
  • Dauda Lawal – Zamfara
  • Seyi Makinde – Oyo

Gwamnonin PDP da suka koma APC daga 2023

  • Umo Eno – Akwa Ibom
  • Sheriff Oborevwori – Delta
  • Peter Mbah – Enugu
  • Douye Diri – Bayelsa
  • Siminalayi Fubara – Rivers

Sauya sheka: PRP ta gargadi Gwamna Bala

A wani labarin, mun ruwaito cewa, PDP na ci gaba da rasa manyan jiga-jiganta yayin da ake shirye-shiryen babban zabe mai zuwa a shekarar 2027.

Awanni kadan bayan ficewar gwamnan Ribas, an fara rade-radin Gwamna Bala Mohammed na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar PRP.

Sai dai, PRP ta bayyana cewa ko da wannan labari gaskiya ne, ba za ta karbi Gwamna Bala ba saboda yadda ya maida jihar Bauchi baya a mulkinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com