Mutfwang: Gwamnan PDP da Ya Gana da Tinubu Zai Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

Mutfwang: Gwamnan PDP da Ya Gana da Tinubu Zai Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

  • Gwamna Caleb Mutfwang ya yanke shawarar barin PDP zuwa APC, kuma hakan na zuwa ne bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu
  • To sai dai kuma, wasu jiga-jigan APC na Plateau suna adawa da shirin karɓar Mutfwang, inda wasu ke barazanar komawa PDP
  • Duk da matsin lamba daga manyan ‘yan siyasa, shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya fara tattaunawar sulhu da masu adawar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Plateau — Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang na jihar Plateau yana dab da kammala shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Wasu sahihan majiyoyi sun shaida cewa Gwamna Mutfwang zai kammala dukkan tsare-tsaren shiga APC kafin ƙarshen watan Janairu 2026.

Gwamna Caleb Mutfwang ya kammala shirin shiga jam'iyyar APC
Gwamna Caleb Mutfwang ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a Aso Rock, Abuja. Hoto: @CalebMutfwang
Source: Twitter

Gwamna ya kammala shirin shiga APC

Majiyoyi daga fadar gwamnatin Plateau sun tabbatar wa jaridar The Cable cewa gwamnan ya gama yanke shawara cewa PDP ba ta da sauran makoma.

Kara karanta wannan

Awanni 24 bayan ganawa da Tinubu, Gwamna Fubara ya fice daga PDP zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kuwa ya faru ne saboda yadda jam’iyyar PDP ta tsage gida biyu a jihar, ta kuma fada cikin mummunan rikici da yazama mafi muni tun bayan kafuwarta.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Gwamna Mutfwang a Abuja, inda ya amince da shirin sauya shekar gwamnan.

Wannan ganawar ta karfafa gwiwar Gwamna Caleb Mutfwang na barin PDP, duk da ce-ce-ku-ce a siyasar jihar, a cewar majiyoyin.

Sai dai kuma, a Plateau, wasu jiga-jigan APC, wadanda ita kanta PDP ta kyankyashe su, sun nuna rashin amincewa da shirin karɓar gwamnan.

Wasu 'yan APC ba sa son karbar gwamna

Wasu ma sun yi barazanar komawa PDP idan har APC ta dage cewa za ta karbi gwamnan zuwa jam'iyyar.

A wani taron masu ruwa da tsaki na APC a Jos a ranar 17 ga Oktoba 2025, tsohon sakataren APC na ƙasa, Festus Fuanter, ya gabatar da kudurin kin karɓar Mutfwang, kuma amincewar taron baki ɗaya ta nuna yadda lamarin ya rikitar da jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya sa labule da Tinubu bayan ficewar 'yan majalisa zuwa APC

Shugaban APC na jihar Plateau, Rufus Bature, ya bayyana cewa dalilin da yasa wasu 'yan jam'iyyar suka ki amincewar da karɓar Mutfwang.

A zantawarsa da jaridar Daily Trust, Rufus Bature ya ce:

“Kamar kowanne mai sauya sheƙa, dole ya bi tsarin jam’iyya. Ya zo ya gana da shugabanni na ƙasa, a yi tattaunawa, a san me jam'iyya za ta amfana, sannan ne za a duba cancantar karɓarsa.”

Shugaban APC na kasa, Nentawe Goshwe Yilwatda, wanda shi ma ɗan jihar Plateau ne, ya fara ganawa da ɓangarorin da suka nuna adawa, domin lallashinsu kan karɓar Mutfwang.

Gwamna Mutfwang ya ce ya na samun matsin lamba ya shiga jam'iyyar APC.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya na jawabi a wani taron ziyara. Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

Abin da ya hana gwamna shiga APC yanzu

Wannan mataki ya nuna cewa kwamitin ƙasa na jam’iyyar ya fi karkata ga karɓar gwamnan, musamman ganin yanayin siyasar jihar.

Kuma tun kafin wannan lokaci, Gwamna Mutfwang ya ce ana matsa masa lamba ya sauka sheka zuwa APC, amma shi zai bi ra'ayin jama'a ne kawai, in ji rahoton Sahara Reporters.

A wani taro a fadar gwamnatin Plateau a watan Oktoba 2025, Gwamna Mutfwang ya ce:

“Ana matsa min lamba daga manyan ‘yan siyasa da in sauya sheƙa zuwa APC. Amma na gaya musu cewa akwai mutane biyu da za su iya bada wannan umarni — Allah Madaukaki da kuma al’ummar da suka zabe ni.”

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 sun dura fadar Aso Rock, sun shiga ganawa da Shugaba Tinubu

Duk da wannan furuci, alamun siyasa na nuna cewa ya kammala kaso 90 na shirin barin PDP zuwa yanzu, sai dai an gano cewa yana jiran a sulhunta lamarin a APC kafin ya sanar da matakin a bainar jama’a.

Gwamna Mutfwang ya musanta komawa YPP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu rahotanni da ake ta yadawa a soshiyal midiya sun nuna cewa Gwamna Caleb Mutfwang, ya fice daga jam'iyyar PDP.

Rahotannin sun yi ikirarin cewa Gwamna Mutfwang ya bar PDP, sannan ya kaucewa komawa APC mai mulki, inda ya zabi shiga jam'iyyar YPP ta adawa.

Sai dai gwamnatin jihar Filato ta karyata wannan labarin, tana mai bayyana cewa Gwamna Mutfwang na nan daram PDP, kuma ta ce an kirkiri rahotannin ne don wautar da jama'a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com