'Ba APC ba ce': Gwamna Adeleke Ya Shiga Sabuwar Jam'iyya bayan Ficewa daga PDP
- 'Yan kwanaki bayan ya sanar da ficewarsa daga PDP, Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya shirya babban taron shiga jam'iyyar Accord
- Gwamnan Osun ya bayyana cewa Accord ce jam'iyyar da zai yi takarar gwamna karkashinta a zaɓen jihar na 2026, kuma zai samu nasara
- Adeleke ya jaddada cewa al’ummar Osun da suka goyi bayansa a 2022 za su sake zabensa a 2026 domin karasa ayyukan raya jiha da ya fara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya tabbatar da cewa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar Accord, ’yan kwanaki bayan ficewarsa daga PDP.
A gagarumin taron shiga sabuwar jam'iyyar da ya shirya, Adele ya kuma sanar da cewa zai shiga takarar wa’adi na biyu a zaben gwamnan jihar na 2026 a karkashin Accord.

Source: Twitter
Gwamna Adeleke ya shiga jam'iyyar Accord
Gwamna Adeleke ya yi wannan sanarwar ne a babban dakin taro na gidan gwamnati a ranar Talata, a gaban manyan shugabannin jam’iyyar Accord na ƙasa da jiha, in ji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adeleke ya ce:
“Na shiga jam'iyyar Accord Party tun watan da ya gabata, tun a ranar 6 ga Nuwamba, inda a nan ne zan nemi wa’adi na biyu a zaben gwamna mai zuwa a 2026.
"Na yanke wannan shawara ne bayan doguwar tattaunawa da neman shawarwari daga shugabanni da masu ruwa da tsaki na jiharmu mai albarka.”
Ya bayyana cewa jama’ar Osun sun san dalilan da suka sa ya ɗauki wannan mataki, yana mai cewa akwai bukatar ya kammala “ayyukan da ya fara” na kyautata mulki da hidimar jama’a.
“Accord ta yi daidai da manufar mu” — Adeleke
Gwamna Adeleke ya ce jam'iyyar Accord ta na da manufofin da suka yi daidai da nasu, musamman kan mayar da hankali wajen samar da walwala ga jama’a, da gina jihar.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, gwamnan ya ce:
“Na zaɓi Accord saboda manufarta ta samar da walwala ta yi daidai da abin da nake yi tun farko; na kasance ina kiyaye jin daɗin ma’aikata da talakawa.”
Gwamna Ademola Adeleke ya ce yanzu Accord ce jam’iyyarsa, kuma ya yi maraba da shugabannin jam’iyyar a gidan gwamnati na jihar Osun.
Ya kara da cewa jam’iyyar za ta samar da wani yanayi da zai tafi da kowa da kowa, sannan a shirya tunkarar zaben shekara mai zuwa.

Source: Twitter
“Accord ita ce jam'iyyar nasara a 2026”
Gwamna Adeleke ya ce daga Osun ta Yamma zuwa ta Gabas da kuma ta Tsakiya, jam'iyyar Accord ce za ta kasance mai nasara a zaben jihar mai zuwa, in ji rahoton Punch.
Ya yi kira ga daukacin masu kada kuri'a a jihar, yana mai cewa:
“Daga Igbomina zuwa Ijeshaland, Ifeland, Osogbo, Iwo, Modakeke, Gbongan, Igbajo, Ikire, Ikirun da Ede, ku sani lokaci ne na goya mana baya domin ci gaba da samar maku da ayyukn more rayuwa."
Gwamnan ya ce Osun ta zabe shi a 2022, kuma yana da yakinin cewa zai sake samun goyon bayan jama’a a zaben 2026 mai zuwa.
Gwamnan Rivers ya sauya sheka zuwa APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya sanar da sauya shekarsa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
Fubara ya ce ya yanke shawarar barin PDP ne a ranar Talata, 9 ga Disamba, 2025 saboda jam'iyyar ta gaza ba shi kariya a rikicin siyasar da ya auku a jihar.
Wannan sauya sheka na zuwa ne awanni 24 bayan gwamnan ya ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


