Awanni 24 bayan Ganawa da Tinubu, Gwamna Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa APC
Rivers, Nigeria - Gwamnan Jihar Ribas, Siminialayi Fubara, da duka magoya bayansa sun yi watsi da jam’iyyar PDP, sun sauya sheka zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Hakan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan Gwamna Fubara ya ziyarci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a fadar gwamnatin tarayya, Abuja.

Source: Facebook
Gwamna Fubara ya tabbatar da sauya sheka zuwa APC ne yayin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a fadar gwamnatin Ribas da ke Fatakwal, in ji Vanguard.
Fubara ya ce fita daga PDP a wurinsa ya zama dole saboda jam'iyyar ta kasa kare shi a rikicin siyasar ya auku a jihar Ribas har sai da Shugaban Ƙasa Tinubu ya shiga tsaka i ya tsare shi daga tunbuke shi daga kujerar gwamna.
Gwamnan ya ce duka magoya bayansa sun amince da wannan shawara da ya yanke ta komawa APC saboda a cewarsu, hakan zai ba su damar marawa Shugaba Bola Tinubu a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa, Fubara ya ce:
“Abin da kuka dade kuna jira ya zo. Mun samu cikakken goyon bayan barin wurin da muke, domin ba mu samu wata kariya ba. Idan ba dan Shugaban Ƙasa ba, da yanzu ba za a kira ni gwamna ba.”
“Mu da magoya bayanmu, mun yanke shawara, daga yau mun koma jam'iyyar APC.”
Da yake tsokaci kan dalilin zuwansa fadar shugaban kasa da ganawa da Bola Tinubu, Gwamna Fubara ya ce ziyarar tana da alaka da goyon bayan tazarcensa a 2027.
Ya ce ya shaida wa Shugaba Tinubu cewa shi da magoya bayansa suna tare da shi, kuma za su yi aiki domin ganin ya cimma burinsa na tazarce zuwa wa'adi na biyu a zabe mai zuwa.
Karin bayani na nan tafe...
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
