NNPP Ta Yi Tsokaci game da Muhimmancin Kwankwaso, Hadaka da APC
- Jam'iyyar hamayya ta NNPP ta yi magana game da tattauna wa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu gabanin zaben 2027
- Shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Ajuji Ahmed, ya ce 2027 za ta zamanto zaben da mutanen Kano za su yanke hukunci
- Jam’iyyar ta jaddada cewa karfinta da tsarinta ne za su kai ta ga nasara, ba shiga kawance da APC da ke mulki ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa tana ci gaba da aiki wajen shirin tunkarar zaben 2027, ba tare da wata boyayyar alaka da Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban jam'iyyar na Kasa, Dr. Ajuji Ahmed ne ya tabbatar da hakan yayin da ake rade-radin akwai yiwuwar APC da Shugaban Kasa suna zawarcin manyan NNPP.

Source: Twitter
A tattaunawarsa da jaridar The Nation, Dr. Ahmed ya yi karin haske game da makomar APC da matsayarta kan sake nasara a zaben Kano a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPP ta barranta kanta da Shugaban Kasa
Politics Nigeria ta ruwaito cewa babu wata tattaunawa ko boye-boye a tsakanin NNPP da Shugaba Bola Ahmed Tinubu game da sauya sheka.
A cewarsa:
“Zan gaya maka cewa jagoranmu na kasa ba ya yin wata tattaunawa da Shugaba ko Fadar Shugaban Kasa, wannan ba siyasa ba ne, gaskiya ce.”
Dr Ahmed ya jaddada cewa NNPP ta shirya shiga zabe da cikakken karfin gwiwa, ba tare da dogaro da wata yarjejeniya ko kawance da APC ba.
NNPP ta magantu kan nasarar zabe a Kano
Ya ce rikici ko hadin gwiwar jam’iyyun siyasa ba su da tasiri wajen yanke makomar Kano a 2027, domin al’ummar jihar su ne za su yanke hukuncin karshe.
Ajuji Ahmed ya ce NNPP ba za ta yi hadin gwiwa da APC ba domin, a ra’ayinsa, hakan zai gurgunta makomar jam’iyyar a Kano.

Source: Facebook
Shugaban jam’iyyar ya kara da cewa manufar NNPP ita ce fadada karfinta a dukkannin jihohi da kananan hukumomi domin a yi gogayya da ita a zabe mai zuwa.
Ya yi nuni da cewa bayan APC, NNPP ce kadai ke da tsari mai karfi a duk fadin kasar nan kuma tana kara karfin ta kafin zabe.
Game da yiwuwar takarar shugaban kasa, ya ce NNPP za ta bude kofarta ga kowane dan takara da yake son gwada karfinsa.
Ya jaddada cewa ko da yake Rabi’u Musa Kwankwaso na da tasiri, ba shi ne mai yanke hukuncin makomai NNPP ba.
“NWC ce ke da ikon yanke hukunci, kuma shi ma ya san haka, zai kuma mutunta shi."
Tsagin NNPP ya nemi afuwan Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsagin jam’iyyar NNPP ya bayyana damuwa tare da neman afuwa daga Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC kan wasu kalaman Rabiu Musa Kwankwaso.
sagin jam'iyyar ya ce akwai cin fuska cikin kalaman da tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi a kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Tsagin na NNPP ya ce Sanata Kwankwaso ya riga ya fita daga cikinta tun tuni, don haka bai da hurumin amfani da sunanta wajen sukar shugabanci ko jam’iyyar APC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


