'Sai Ka Dauki Mataki,' Matasa Sun Fadawa Tinubu abin da Zai Hana Shi Cin Zabe
- Matasa Arewa sun gargadi Shugaba Bola Tinubu cewa zai lashe zaben 2027 ne idan ya kawo karshen matsalar tsaro da matsin tattalin arziki
- Kungiyar matasan ta AYCF ta ya kashedi cewa goyon bayan gwamnoni da Tinubu ke samu yanzu ba shi ne zai sa ya lashe zaben 2027 ba
- Ba iya kungiyar matasan ba, akwai masu sharhin siyasa da suka ba Tinubu shawarwarin matakan da zai dauka idan yana so ya yi nasara a 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar matasan Arewa ta AYCF ta tunatar da Shugaba Bola Tinubu game da abubuwan da za su jawo nasararsa a zaben shugaban kasa na 2027.
A cewar matasan, nasarar Tinubu ba za ta dogara kan goyon bayan ’yan siyasa ko alkawura a kamfe ba, sai kan yadda gwamnatinsa za ta shawo kan matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki.

Source: Facebook
Matasa sun gargadi Tinubu kan zabne 2027
Shugaban kungiyar matasan Arewa na kasa, Yerima Shettima, ya bayyana wannan gargadi ne cikin hirarsa da jaridar Punch, inda ya ce matasan Arewa na cike da damuwa kan karuwar kashe-kashe, garkuwa da mutane da matsin tattalin arziki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya ce bai kamata Tinubu ya dora yakinin cin zaben 2027 kawai don ya na samun yabo daga gwamnoni ko manya ba, a cewarsa, irin wadannan goyon baya ba zai yi tasiri a lokacin ba.
Ya kuma tuna cewa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya samu irin wannan gagarumin yabo daga jihohi a lokacin zaben 2015, amma hakan bai hana shi faduwa ba saboda rashin gamsuwar jama’a.
A cewarsa, Najeriya tana cikin wani mawuyacin hali inda hare-haren ’yan bindiga, rikicin manoma da makiyaya, tashin hankali tsakanin al’umma da yawaitar hare-haren ta’addanci suka haddasa rashin kwanciyar hankali, suka kuma ta da hankali ga miliyoyin ’yan kasa.
Najeriya na cikin matsin tattalin arziki
Ya kara da cewa tattalin arzikin kasar ya kara dagulewa inda hauhawar farashi, rashin aikin yi, da tabarbarewar yanayin rayuwa ke ci gaba da raunana jama’a.
A cewarsa, yanayin matsin tattalin arziki zai sanya ’yan Najeriya su yi nazarin duk wasu manufofi da ayyukan shugaban kasa, musamman yadda zai magance tsadar rayuwa da faduwar darajar Naira.
Shettima ya jaddada cewa matasa—wadanda su ne kashi mafi yawa a kuri’un Najeriya—sun gaji da alkawuran siyasa, kuma za su zabi shugaba ne bisa aikin da ya yi, ba bisa alkawuran zabe ba.
Ya ce wannan lokaci ne da gwamnatin Tinubu za ta fahimci cewa abin da jama’a ke bukata shi ne tsaro da saukin rayuwa, ba hotuna da tarurrukan siyasa ba.

Source: Facebook
SDP ta goyi bayan kalaman AYCF
A gefe guda kuma, wasu manyan Arewa sun goyi bayan wannan gargadi na AYCF, kamar shugaban Jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam.
Shehu Gabam ya ce bai kamata a fara tattauna batutuwan nasarar zaben 2027 a yanzu ba, la'akari da cewa kasar na fama da rikicin tsaro a ko’ina.
Ya ce darasin da Jonathan ya koya a 2015 ya kamata ya zama izna ga duk wani shugaba: goyon bayan gwamnoni ba zai taba nuna nasara a zabe ba idan jama’a ba su gamsu da aiki ba.
Gwamna ya yi albashir ga Tinubu kan 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya halarci wani babban gangamin da aka shirya na jam'iyyar APC mai mulki.
A yayin gangamin, Gwamna Uba Sani ya karbi mambobin jam'iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC, tare da yin babban albishir ga Shugaba Bola Tinubu.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa yanzu babu sauran wata adawa a jihar Kaduna, kuma jam'iyyar APC za ta samu mafi yawan kuri'u a zaben 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


