Siyasar Najeriya: 'Dan Majalisar Tarayya Ya Burma Matsala, An Kore Shi daga YPP

Siyasar Najeriya: 'Dan Majalisar Tarayya Ya Burma Matsala, An Kore Shi daga YPP

  • Jam'iyyar YPP ta bayyana cewa ta samu bidiyo da ke tabbatar da zargin da ake wa dan majalisar wakilai, Hon Uzokwe Peter na cin amana
  • A taron kwamitin zartarwa (NEC) na YPP ta kasa, jam'iyyar ta yanke shawarar korar dan Majalisa bisa zarge-zargen da ke kansa
  • Haka nan kuma YPP ta yi fatali da duk wani yunkuri na maida Najeriya kasa mai bin tsarin jam'iyya daya, ta ce hakan barazana ce ga dimokuradiyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar adawa ta YPP ta kori ɗan majalisar wakilai na tarayya, Hon. Uzokwe Peter, bisa zargin aikata ayyukan cin amana da zagon kasa.

Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da jam’iyyar YPP ta kuma zaɓi sababbin shugabanninta domin cike guraben kujeru da suka zama babu kowa a kai.

Kara karanta wannan

'Yan Biyafara sun taru sun harzuka bayan daure Nnamdi Kanu a Sokoto

Hon. Uzokwe Peter.
Dan Majalisar Wakilai, Hon. Uzokwe Peter da aka kora daga YPP Hoto: Ifeanyi Uzokwe Peter
Source: Facebook

Tashar Channels ta rahoto cewa hakan na cikin wata sanarwa da YPP ta fitar bayan taron kwamitin zartarwa (NEC) na gaggawa karo na 24 da aka yi a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun YPP na kasa, Egbeola Martins, ya rattaba hannu a takardar mai dauke da kwanan watan 5 ga Disamba, 2025.

Dalilin korar ɗan majalisa daga YPP

A cewar jam’iyyar, an kori Uzokwe Peter, wanda ke wakiltar Nnewi ta Arewa, Nnewi ta Kudu da Ekwusigo a Majalisar Wakilai ne bayan korafe-korafen da bidiyon da ke nuna yadda ya ke cin amanar YPP.

Ta ce abubuwan da dan majalisar ya aikata sun karya wasu sashe na kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP kamae sashe na 36(7), Article b, f & o, shafi na 70–71.

Jam’iyyar ta bayyana cewa a shirye take ta dauki mataki kan duk wanda ya yi yunkurin ruguza hadin kan mambobinta da rashin ladabi da biyayya da dokoki.

Kara karanta wannan

Kuɗin da yawa: Gwamna Zulum ya faɗi biliyoyin Naira da ya kashe kan tsaro a 2025

YPP ta zabi sababbin shugabanni

NEC ta kuma kada kuri’ar goyon baya tare da amincewa da Shugaban Jam’iyyar YPP na ƙasa, Bishop Amakiri.

Shugaban YPP na Kaduna, Mikailu Abubakar, ya gabatar da kudirin amincewa da shugaban jam'iyya na kasa kuma ya samu goyon bayan Shugaban jam'iyya na Ekiti, Owoola Daramola.

Jam'iyyar YPP.
Tambarin jam&iyyar adawa a Najeriya, YPP Hoto: YPP Nigeria
Source: Facebook

YPP ta soki duk wani yunƙuri daga Shugaba Bola Tinubu, ko wasu ‘yan siyasa na ƙoƙarin maida Najeriya zuwa tsarin jam’iyya ɗaya, tana mai cewa hakan barazana ce ga dimokuraɗiyyar ƙasa.

Jam’iyyar ta jaddada cewa ƙarfafa tsarin jam’iyyu da dama, yarda da sabani, da ‘yancin shiga kowace jam’iyya sune ginshiƙan dimokuraɗiyya, kamar yadda Leadership ta rahot.

Majalisar za ta dauki matsaya kan gyaran dokoki

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta sanar da cewa za ta kada kuri'a kan yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawul a ranakun 10 da 11 ga Disamban 2025.

Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na rana Talata, 2 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Da gaske an kama Wike a Faransa? Ministan ya fadi halin da yake ciki

Ya bayyana cewa kwamitin ya kammala dukkan ayyukan da ake buƙata, kuma ana shirya takardun da aka haɗa gaba ɗaya domin gabatarwa ga ’yan majalisa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262