Ana Wasan Kora a PDP, Tsagin Wike Ya Kori Shugaban Jam'iyya da Wasu Mutum 17

Ana Wasan Kora a PDP, Tsagin Wike Ya Kori Shugaban Jam'iyya da Wasu Mutum 17

  • Tsagin jam’iyyar PDP da ke goyon bayan Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ta sake tabbatar da korar wasu manyan ’yan siyasa 18
  • Bangaren ya gargadi jama’a da su guji mu'amalantar mutanen da aka kora saboda zagrin cewa yanzu su ba 'yan PDP ba ne, sojan gona suke yi
  • Wannan ya kara dagula al'amura a jam'iyya, inda bangaren Shugaban jam'iyya Tanimu Turaki ya kori Wike da mutanensa daga cikin jam'iyyar adawar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wani bangare na PDP da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ke mara baya ya fitar da sanarwa, inda ya sake jaddada korar manyan ’yan siyasa 18 daga jam’iyyar.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da Mataimakin Sakataren Jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya fitar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Bola Tinubu zai jagoranci babban taron jam'iyyar APC a Abuja

An kori jiga-jigan PDP
Nyesom Wike, Magoya bayan jam'iyyar PDP Hoto: @GovWike/Kola Sulaiman
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa an gargadi jama’a da su yi hattara da masu jingina kansu da PDP, duk da cewa an riga an kore su tun ranar 18 ga Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin cikin gidan PDP ya kara dagulewa

Politics Nigeria ta wallafa cewa ta kori jiga-jigan cikinta ne saboda zargin aikata abin da ya sabawa jam’iyya da kuma rashin da’a, bisa tanadin kundin tsarin mulkin PDP na 2017 da aka yi wa gyara.

Daga a cikin wadanda aka kora akwai Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed; Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal; da Gwamnan Oyo, Seyi Makinde.

Haka kuma an saka sunan tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Emmanuel Udom; tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Adolphus Wabara; da tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyya (Kudu), Taofeek Arapaja.

Tsagin Wike ya kori Tanimu Turaki da wasu mutum 17
Shugaban PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki Hoto: Kabiru Tanimu Turaki
Source: Facebook

Sauran sun hada da tsohon Ministan Harkokin Musamman, Kabiru Tanimu Turaki; tsohon Mai Ba da Shawara ga Shugaban Kasa, Ben Obi; Chief Bode George; da tsohon Mukaddashin Shugaban Jam’iyya, Umar Iliya Damagum.

Kara karanta wannan

Adeleke: Martanin PDP bayan wani Gwamnan ya sake ficewa daga jam'iyyar

Akwai kuma Okechukwu Obiechina, Emmanuel Ogidi, Emmanuel Ebien, Suleiman Kadade Mohammed, Sunmaila Adamu Bunza, Koshoedo Setonji, Daniel Woyengikuro, da Umar Sani.

Tsagin Wike ya gargadi 'yan PDP

Bangaren PDP na Wike ya ce abin takaici ne yadda mutanen da aka kora ke ci gaba da magana da aikata abubuwa a madadin jam’iyyar, lamarin da ya ce haramun ne.

Ya bukaci jama’a da ’yan jam’iyya su yi watsi da duk wata sanarwa ko taro da wadancan mutanen za su fitar, domin ba su da matsayi ko iko a PDP.

Sanarwar ta kuma yi watsi da wani babban taro da aka yi a Ibadan da wasu daga cikin korarrun suka halarta, tana mai cewa taron.

Gwamnan Zamfara zai iya barin PDP

A baya, kun ji cewa Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ba zai koma APC mai mulkin Najeriya ba har sai an cika wasu muhimman sharudda da ya gabatar wa shugabannin jam’iyyar.

Daya daga cikin babban sharadin shi ne a cire Bello Matawalle daga mukaminsa a matsayin Karamin Ministan Tsaro, kafin ya yi watsi da jam'iyyarsa mai hamayya zuwa APC mai mulki.

Kara karanta wannan

PDP ta manta da adawa, ta koma neman taimako wajen Shugaba Tinubu

Rahotanni sun tabbatar da cewa Gwamna Dauda Lawal na neman cikakken iko da tabbacin cewa zai samu goyon baya a jihar kafin ya yanke shawarar komawa APC bayan kiraye-kirayen ya sauya sheka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng