An Bukaci Gwamna Ya Gaggauta Fita daga PDP a Wata Wasika da Aka Rubuta a Filato

An Bukaci Gwamna Ya Gaggauta Fita daga PDP a Wata Wasika da Aka Rubuta a Filato

  • Kungiyar magoya bayan PDP a jihar Filato ta ce akwai bukatar Gwamna Caleb Mutfwang ya hada inuwa daya da Bola Tinubu a siyasa
  • Bisa haka kumgiyar ta rubuta wasika zuwa ga gwamnan, tana mai rokon ya gaggauta sauya sheka daga PDP zuwa APC mai rike da mulkin kasa
  • Ta kafa hujja da yadda gwamnatin Tinubu ke nuna kauna ga jama'an jihar Filato, tana mai cewa komawar Mutfwang APC za ta kara kawo ci gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau, Nigeria - 'Yan siyasa da wasu magoya bayan PDP na ci gaba da kokarin shawo kan Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato domin ya sauya sheka zuwa APC.

Kungiyar magoya bayan PDP ta Coalition of PDP Supporters reshen jjhar Filato ta shiga layin wadanda ke ganin ya kamata Gwamna Mutfwang ya koma APC ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Sharadin da Gwamna Dauda ya kafa don komawa jam'iyyar APC

Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang.
Gwamna Caleb Mutfwang a fadar gwamnatin jihar Filato da ke Jos Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa bisa haka, kungiyar ta rubuta wasika ta musamman kuma ta kai wa gwamnan har gidan gwammati da ke Jos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An nemi gwamnan Filato ya koma APC

A cikin wasikar, kungiyar ta bukaci Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, da ya koma jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya cikin gaggawa.

Shugaban ƙungiyar, Hon. Christopher Dajem, ya bayyana haka ne yayin mika wa gwamnan wasiƙar buƙatar sauya sheka a Fadar Gwamnati da ke Little Rayfield, Jos.

Dajem ya ce bukatar ta zo ne bayan nazari mai zurfi da ƙungiyar ta yi kan halin da siyasar Najeriya ke ciki.

Ya ce:

"Muna kira ga Gwamna Caleb Mutfwang da ya koma APC domin ƙarfafa haɗin kan kasa.”

'Tinubu na kaunar jama'an Filato'

Ya kara da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana nuna kauna ga jama’ar Filato, inda ya tunatar da yadda uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu, ta ziyarci jihar domin jajantawa lokacin hare-haren da suka jawo asarar rayuka.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano

Dajem ya ci gaba da cewa:

“Muna rokon ka da ka hada kai da shugaban ƙasa a jam’iyya guda domin Filato ta ci gaba da amfana da romon dimokuraɗiyya.”
Gwamna Mutfwang da Tinubu.
Gwamna Caleb Mutfwang tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Gwamna Mutfwang ya amince da bukatar?

A nasa jawabin, Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Filato, Jeremiah Satmak, wanda ya karɓi ƙungiyar a madadin gwamna, ya yaba musu saboda nuna damuwa da kishin ci gaban jihar.

A rahoton Punch, Satmak ya ce:

“Za mu miƙa wannan saƙo ga mai girma gwamna. Kun san shi mutum ne mai son ci gaba, kuma ya shahara wajen aikin al’umma. Za ku ji daga gare shi a lokacin da ya dace."

APC na shirin kwace mulkin Filato a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi karbi wasu mambobin jam'iyyun adawa da suka sauya sheka zuwa APC a Filato.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce jam’iyyar APC na da cikakkiyar damar kwace mulki daga PDP a zaben gwamnan jihar Filato mai zuwa a 2027.

Kara karanta wannan

PDP ta manta da adawa, ta koma neman taimako wajen Shugaba Tinubu

Ya kara da cewa yana da kwarin guiwar APC za ta lashe zaben shugaban kasa, na ‘yan majalisar dattawa, wakilai da na majalisar dokoki ta jiha a babban zabe mai zuwa a Filato.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262