Rade Radi: Gwamna Dauda Zai Iya Komawa Jam'iyyar APC daga PDP

Rade Radi: Gwamna Dauda Zai Iya Komawa Jam'iyyar APC daga PDP

  • Akwai yiwuwar gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, na shirin sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki
  • Sai dai, jita-jita ta nuna cewa akwai abubuwan da yake so a cika masa kafin ya wanjke kafafunsa ya koma APC tare da magoya bayansa
  • Rade-radin da ake yadawa sun nuna cewa daga cikin abin da gwamnan yake akwai wanda zai iya shafar karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Jita-jita ta nuna cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, na iya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Gwamna Dauda dai ya kasance daya daga cikin gwamnonin da suka yi saura a jam'iyyar PDP mai adawa.

Gwamna Dauda na son a cire Matawalle daga Minista
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal da karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle Hoto: Dauda Lawal, Bello Matawalle
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce majiyoyi masu tushe sun ce gwamnan yana neman cikakken ikon APC a Zamfara kafin ya sauya sheƙa daga PDP zuwa jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Dalilin APC na kin karbar Gwamna Mutfwang zuwa cikinta

Gwamna Dauda ya gana da Tinubu

Jita-jita ta nuna cewa Gwamna Dauda ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a birnin Faris, Faransa, tare da gwamnonin Enugu da Taraba, inda ya bayyana shirinsa na komawa APC idan aka amince da sharuɗɗansa.

Wannan ganawar da aka yi a otal ɗin Peninsula watannin da suka gabata, ta zama muhimmin mataki a tattaunawar da ake yi, shafin TheNigerianLawyer ya dauko labarin.

Masu yada jita-jitar sun bayyana cewa tun bayan dawowarsa, Gwamna Dauda ya tsaya kai da fata yana matsawa fadar shugaban kasa kan a cire Matawalle daga gwamnati tare da ba shi ikon jagorantar APC a Zamfara.

Ana son raba Matawalle da kujerarsa

Murabus din Ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya kara wa gwamnan kwarin guiwa, inda ake zargin ya sake matsa kaimi a kan cewa lokaci ya yi da za a cire Matawalle daga majalisar zartarwa.

Masu sharhi kan al’amuran siyasa suna ganin wannan yunkuri na Gwamna Dauda yana da nasaba da burinsa na samun cikakken tasiri a APC idan ya kammala shirin sauya sheƙa.

Kara karanta wannan

Tsohon kakakin PDP na kasa ya bi sahun gwamnoni 5, ya fice daga jam'iyyar

Har ila yau, akwai rade-radin cewa gwamnan na samun goyon baya daga wasu manyan jami’an tsaro wajen tura rahotannin da za su iya rage karfin matsayin Bello Matawalle.

Ana kuma rade-radin cewa idan aka cire Matawalle, Gwamna Dauda zai jagoranci tsarin jam’iyyar PDP da magoya bayansa gaba ɗaya zuwa APC domin ya kafa cikakken rinjaye gabanin zaben 2027.

Gwamna Dauda na shirin komawa APC
Gwamna jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare Hoto: Mugira Yusuf
Source: Facebook

Wasu masu nazari sun ce gwamnan yana kallon Matawalle a matsayin babban cikas ga burinsa na siyasa, musamman a Arewa maso Yamma, inda tsohon gwamnan ya samu karuwar tasiri da yabo saboda aikace-aikacen tsaro da ya jagoranta.

A watannin baya-bayan nan, Matawalle ya samu karin farin jini bayan rawar da ya taka wajen ceto daliban da aka sace a jihar Kebbi da kuma muhimmiyar gudummawar da ya bayar wajen daidaita al’amuran tsaro a wasu sassan Sokoto da Zamfara.

An kai shugaban APC kara a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta reshen jihar Zamfara ta samu kanta cikin rikicin da ya kai zuwa ga kotu.

Rikicin ya yi kamari ne bayan wasu jiga-jigai sun maka shugaban jam’iyya na jihar, Tukur Danfulani, a gaban babbar kotu da ke Gusau.

Kara karanta wannan

Gwamna Inuwa ya yi karatun ta natsu, ya zakulo abin da ya haddasa rashin tsaro a Arewa

A cikin karar da suka shigar ranar 14 ga Nuwamba, sun bukaci kotu ta, tabbatar da cewa su duka halastattun ’yan jam’iyyar APC ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng