‘Kujerar Shettima Yake So’: Musulmi Sun Shawarci Fasto Ya Jira zuwa 2027

‘Kujerar Shettima Yake So’: Musulmi Sun Shawarci Fasto Ya Jira zuwa 2027

  • Wata kungiya mai kare hakkin Musulmi, MURIC ta ba fitaccen Fasto a Arewacin Najeriya, Rabaran Ezekiel Dachomo shawara
  • MURIC ta caccaki Rabaran Dachomo kan ikirarin cewa gwamnatin Bola Tinubu ta Musulmi da Musulmi ta haifar da “kisan gilla ga Kiristoci”
  • Kungiyar ta kuma yi zargin cewa ikirarin “kisan Kiristoci” wata dabara ce ta don neman kujerar siyasa ba ainihin kare mabiya addinin ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi, watau MURIC ta aika gargadi mai zafi ga wani Fasto a Arewacin Najeriya.

MURIC ta gargadi Rabaran Ezekiel Dachomo da cewa idan yana sha’awar zama mataimakin shugaban Najeriya ya jira 2027.

An soki Fasto kan taba kujerar Shettima
Fasto Ezekiel Dachomo da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima, Ezekiel Dachomo.
Source: Facebook

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin kungiyar da aka wallafa a jiya Talata 2 ga watan Disambar 2025.

Kara karanta wannan

An gano wanda zai iya maye gurbin Badaru a matsayin ministan tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Fasto Dachomo ya ce kan Shettima

A cikin kalamansa, Dachomo ya ce shugaban kasa Musulmi ne, haka kuma mataimakinsa inda ya bukaci a cire Shettima.

Rabaran Dachomo ya ce:

“Shettima Musulmi ne, shugaban ƙasa Musulmi ne. Shin wannan ba kisan gilla ga Kiristoci ba ne a siyasa? Magani shi ne a cire Shettima, kuma ina nan akan wannan magana.”

Martanin kungiyar MURIC ga Fasto Dachomo

A cewar Farfesa Ishaq Akintola wannan jawabi ne wajen mayar da martani kan ikirarin Fasto Dachomo cewa akwai “kisan gilla ga Kiristoci”.

Ta ce akwai zargin haka ne saboda shugaban ƙasa, Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima duk Musulmai ne.

MURIC ta yi zargin cewa kalaman Dachomo sun yi tsauri kuma suna cike da ƙaryar tashin hankali inda ta ce maganar ta nuna rashin girmama matakan da Najeriya ta bi daga kamfe zuwa zaɓe.

MURIC ta ce:

Kara karanta wannan

Ekane: Jagoran 'yan adawa da Paul Biya a Kamaru ya rasu a kurkukun soja

“Idan Rabaran Dachomo yana son zama mataimakin shugaban ƙasa, ya bi dokar damokraɗiyya, ya jira 2027.”
MURIC ta soki Fasto kan neman Shettima ya sauka
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Twitter

Zargin da MURIC take yi wa faston

Ƙungiyar ta kuma ce Rabaran ɗin ya nuna tsananin fargaba ga Musulmi, yana ganin tiktin Musulmi da Musulmi ko ina kamar wani abu ne da zai cinye shi.

Ta ce hakan ya jawo masa tunanin cewa kasancewar shugaban ƙasa da mataimaki Musulmai ne, tamkar “kisan Kiristoci” ne.

MURIC ta yaba wa Kiristocin da suka fuskanci gaskiya suka fahimci cewa zarge-zargen “kisan Kiristoci” ba su da tushe.

Ƙungiyar ta roki Musulmai da Kiristoci masu kishin ƙasa da su haɗu don magance matsalolin tsaro da ayyukan ‘yan bindiga a ƙasar.

A ƙarshe, MURIC ta gargadi Fasto Dachomo game da yadda yake fitowa da murya mai tsauri a kafafen watsa labarai.

Yan bindiga: Fasto ya bar wasiyya ga iyalansa

A baya, an ji cewa Malamin addinin Kirista a jihar Plateau ya yi magana kan masu garkuwa da mutane inda ya yi wa mabiyansa gargadi kan biyan kudin fansa.

Kara karanta wannan

"Shettima Musulmi ne": Fasto ya nemi a cire mataimakin Tinubu

Fasto Ezekiel Dachomo ya ce idan an sace shi, kada a biya fansa, yana mai cewa jininsa zai haifar da yaki na ’yantar da Kiristoci.

Malamin ya bayyana cewa ya yarda da haɗarin da yake ciki game da kisan gilla a Arewa, musamman waɗanda ke kai wa Kiristoci hari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.