Magana Ta Fara Fitowa, An Ji Dalilan da Suka Jawo Gwamna Ya Fita daga PDP
- A jiya Litinin, 1 ga watan Disamba, 2025 Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP
- Kwamishinan yada labarai na Osun, Kolapo Alimi ya ce Gwamna Adeleke ya dade da yanke shawarar raba gari da PDP kafin zaben Osun
- Ya ce gwamnan ya dauki wannan mataki ne saboda rashin tabbas a PDP bayan darewar jam'iyyar gida biyu a matakin kasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeria - Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Osun, Kolapo Alimi, ya bayyana dalilin da ya sa Gwamna Ademola Adeleke ya fita daga jam'iyyar PDP tun kafin zaben fitar da dan takara.
Gwamna Adeleke ya ce ya mikawa shugabannin jam’iyya a Sagba Abogunde, gunduma ta 2, karamar hukumar Ede ta Arewa, takardar ficewarsa tun ranar 4 ga Nuwamba, 2025.

Source: Twitter
Tribune Online ta ce a wata hira da aka yi da shi a ranar Talata, Alimi ya ce ba haka kurum gwamnan ya bar jam'iyyar ba face sakamakon rikice-rikicen cikin gida da suka dade suna faruwa a PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Adeleke ya dade da yanke shawara
A cewar Kolafo Alimi, Gwamna Adleeke ya dade da yanke shawara, kuma ya rubuta takardar barin jam’iyyar PDP tun watanni da suka gabata.
Ya ce:
“Gwamnan Jihar Osun kuma Asiwaju na Ede ya fice daga jam’iyyar PDP a hukumance. Ya dade da aikawa da takardar ficewarsa tun can baya.”
Ya kara da cewa gwamnan yana godiya bisa goyon bayan al’ummar Osun, yana rokon su da su ci gaba da kasancewa da shi, rahoton People Gazette.
“Lokaci ya yi. Muna godiya da goyon bayan jama’a. Muna rokon al’umma su ci gaba da mara masa baya,” in ji shi.
Dalilan da suka sa Adeleke ya bar PDP
Alimi ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida na PDP a matakin ƙasa ne suka tilasta wa Adeleke raba gari da jam'iyyar, musamman ganin cewa zaben gwamna na kara gabatowa.
Kwamishinan ya kara da cewa wa'adin hukumar INEC na karɓar sunayen ’yan takara zai kare a ranar 15 ga Disamba, 2025, amma kuma babu wata alamar masalaha a PDP.
“Da ba don rikicin da ke faruwa a PDP ta ƙasa ba, wanda yana da matuƙar tasiri ga zaben fitar da gwani, da gwamnan bai bar jam’iyyar ba.
"Lamarin ba batun sauya sheka ba ne kawai, shi ne hakikanin abin da ke faruwa, domin zabe na gabatowa, kuma INEC za ta rufe karbar sunaye 'yan takara a ranar 15 ga Disamba. Saboda haka dole ne gwamnan ya yi murabus daga PDP."

Source: Twitter
PDP ta tsaida dan takarar gwamna a Osun
A wani rahoton, kun ji cewa Adebayo Adedamola ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar Osun na jam’iyyar PDP a zaben da za a yi a shekara mai zuwa, 2026.
Adedamola ya samu kuri’u 919 daga cikin kuri’u 957 da aka kada wanda shugaban kwamitin zaben fitar da gwanin, Humphrey Abba ya sanar.
PDP ta gudanar da zaben fitar da dan takararta ba tare da Gwamna Adeleke ba, wanda tuni ta sanar da ficewarsa daga jam'iyyar saboda rikicin cikin gida.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


