ADC: Magoya Bayan Atiku Abubakar Sun Gwabza da Babachir Lawal
- Rikicin shugabanci a ADC ta Adamawa ya kara tsananta bayan sabani tsakanin Babachir Lawal da tsagin magoya bayan Atiku Abubakar karkashin Shehu Yohanna
- Rahotanni sun bayyana cewa magoya bayan Atiku Abubakar sun fice daga wani taron jam’iyyar adawa ta ADC bayan an tilasta wa Yohanna fita daga dakin taron
- Babachir, wanda shi ne mataimakin shugaban ADC na Arewa maso Gabas ya ce an kori Yohanna daga taron ne saboda ya kai jam’iyyar kotu kan rikicin shugabanci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Adamawa – Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar hamayya ta ADC a jihar Adamawa ya kara karfi a ranar Litinin, bayan takaddama mai zafi ta barke tsakanin 'ya'yanta.
Rahotanni sun ce Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, reshen Arewa maso Gabas, Injiniya Babachir David Lawal, da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Adamawa, Shehu Yohanna sun samu matsala.

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa Yohanna, wanda ke da goyon bayan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, na daga cikin mutum uku da ke ikirarin shugabancin jam’iyyar a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu baraka tsakanin 'yan ADC a Adamawa
Trust radio ta wallafa cewa Shehu Yohanna ne ya jagoranci karbar Atiku cikin jam’iyyar makon da ya gabata – taron da Babachir bai halarta ba.
A baya, Babachir Lawal ya nuna goyon bayansa ga Sadiq Dasin a matsayin shugaban jam’iyyar na jiha tare da amincewar kwamitrin zartarwa na jam'iyya, kafin daga bisani ya koma goyon bayan Mustapha Arabi.
A wani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya domin raba takardun rajista 'yan jam'iyya da tsara yadda aikin zai gudana, Babachir Lawal ya bukaci jami’an tsaro su fitar da Shehu Yohanna daga dakin taron.

Source: Twitter
Sai dai kafin wannan lamarin, masu ruwa da tsaki sun riga sun hana Yohanna da Arabi shiga dakin taron, suna cewa ba a warware rikicin shugabanci ba, sai aka hana su shiga.
Daga bisani, tsohon Sakataren gwamnatin ya shawo kan matasa, aka bar suka shiga, amma daga baya aka zargi Babachir da bayar da umarnin a sake fitar da Yohanna.
Magoya bayan Atiku sun harzuka
Wannan al'amari da ya haddasa fushin magoya bayan Atiku wadanda suka fice daga taron, sun kira lamarin cin amanar da ba ta taba faruwa ba a yankin.
Umar Sadiq Jada, daya daga cikin magoya bayan Atiku, ya ce:
“Babu dalilin zama wurin da ba a kaunar zuwanka.”
A martaninsa, Babachir Lawal ya ce an roki Yohanna ya fita ne saboda ya kai jam’iyyar kotu a kan rikicin shugabancin da ya dabaibaye ta.
Ya ce:
“Ba shi kadai ba ne aka bukaci a fitar da shi. Shugaban jam’iyyar ya ce ba zai zauna da wanda ya kai jam’iyya kotu ba.”
Bangaren Atiku zai jawo wasu zuwa ADC
A baya, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya fara kokarin tattaro manyan 'yan siyasa su koma jam'iyyar hamayya ta ADC gabanin babban zaben 2027 da ke tunkarowa.
Rahotanni sun ce bangaren na Atiku ya fara neman ɗan takarar mataimakin shugaban kasa daga Kudu domin takara a zaben shekarar 2027 domin a hada karfi wajen fatattakar APC daga mulki.

Kara karanta wannan
Sace dalibai a Neja: Ribadu ya bada tabbaci bayan ganawa da shugabannin Kiristoci
Wata majiya ta ce idan Peter Obi ya ki amincewa ya tsaya tare da Atiku, to Atiku zai koma neman tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi domin a hada kai gabanin babban zaben.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

