Gwamnan da ke Shirin Komawa APC Ya Gana da Shugaba Tinubu a Abuja
- Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja
- Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya halarci wannan zama, wanda ake ganin yana da alaka da batun taron karbar Gwamna Kefas
- Wannan dai na zuwa ne bayan Gwamna Kefas da magoya bayansa sun bar PDP zuwa APC amma har yanzu ba a karbe su zuwa jam'iyyar a hukumance ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karbinbakuncin gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.
Shugaba Tinubu ya yi ganawa ta musamman da Gwamna Kefas, wanda ya kwanan nan ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulkin kasar nan.

Source: Facebook
Tinubu, shugaban APC sun gana da Kefas
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya halarci taron Tinubu da gwamna Kefas a Aso Rock Villa yau Litinin, 1 ga watan Disamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ziyara ta Gwamna Agbu Kefas na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen tarbarsa a hukumance zuwa APC.
A kwanakin baya dai Gwamna Kefas ya sanar da komawa APC tare da duka magoya bayansa, amma har yanzu jam'iyyar ba ta karbe shi a hukumance ba kamar yadda ta saba bisa al'ada.
Me ya hana APC karbar Gwamna Kefas?
Legit Hausa ta fahimci cewa APC ta dage babban taron da ta shirya domin karbar gwamnan a hukumance saboda karuwar matsalar tsaro a wasu sassan kasar nan.
An soke gangamin taron sauya shekar da aka shirya yi a Jalingo ne a daidai lokacin da aka yi garkuwa da dalibai a Jihar Kebbi da kuma wasu mabiya addinin kirista a Majami’a a Jihar Kwara.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Yilwatda da Gwamna Kefas sun isa fadar shugaban kasa misalin ƙarfe 2:30 na rana yau Litinin.
A cewar rahoto daga fadar gwamnatin, an gudanar da taron ne a sirrince ba tare da barin 'yan jarida sun shiga ba, kuma har yanzu ba a bayyana sakamakon tattaunawar ba.

Source: Facebook
Dalilin zuwan Gwamna Kefas wurin Tinubu
Jaridar Punch ta fahimci cewa tattaunawar na iya ta’allaka kan ƙayyade sabon kwanan wata da za a gudanar da gangamin tarbar Gwamna Kefas da magoya bayansa cikin jam’iyyar APC.
Idan gwamnan Taraba ya koma APC mai mulki a hukumance, zai zama gwamnan PDP na biyar da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar tun bayan rantsar da Shugaba Tinubu a watan Mayu, 2023.
'Yan Majalisa 16 sun koma APC a Taraba
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta karbe ragamar shugabanci a Majalisar Dokokin Jihar Taraba bayan sauya shekar mambobi 16.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Rt. Hon. Kizito Bonzena, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC tare da mataimakinsa da yan Majalisa 14.
Rt. Hon. Bonzena ya bayyana cewa ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC ba don wata manufa ta kashin kansa ba, sai don maslahar jihar Taraba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

