Ana Wata ga Wata: Sule Lamido Ya Sake Tayar da Kura a Jam'iyyar PDP

Ana Wata ga Wata: Sule Lamido Ya Sake Tayar da Kura a Jam'iyyar PDP

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya koka kan rikicin da ya dade yana addabar babbar jam'iyyar PDP mai hamayya
  • Sule Lamido ya bukaci a soke zaben shugabannin PDP da aka yi yayin babban taronta na kasa da aka gudanar a birnin Ibadan
  • Tsohon ministan harkokin wajen ya kuma bada shawarar kafa kwamitin rikon kwarya domin jagorantar ragamar jam'iyyar

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ba shugabancin jam’iyyar PDP na kasa sabon wa'adi.

Sule Lamido ya bada wa’adin kwana 10 don magance matsalolin cikin gida da ya ce suna ta kara ta’azzara a jam’iyyar.

Sule Lamido ya ba jam'iyyar PDP wa'adi
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido Hoto: Sule Lamido
Source: Twitter

Jaridar Tribune ta ce Sule Lamido ya bayar da wannan wa’adin ne lokacin da yake karɓar dubban magoya baya, ciki har da tsofaffin shugabanni, kwamishinoni da abokan siyasa.

Kara karanta wannan

El Rufai ya bi sahun Atiku wajen shiga ADC, ya sha alwashi kan APC a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Sule Lamido ya ce kan PDP?

Sule Lamido ya yi kira da a soke babban taron Ibadan na zaben shugabannin jam’iyya gaba ɗaya, rahoton ya zo a jaridar The Punch.

Haka kuma ya nemi a gaggauta kafa kwamitin rikon kwarya na kasa da zai jagoranci jam’iyyar a cikin wannan rikici da take ciki yanzu.

Tsohon gwamnan ya koka cewa fitattun jiga-jigan jam’iyya irin sa, suna ta samun wulakanci da tursasawa daga “sababbin jini” masu kokarin karya tsarin jam’iyyar da aka dora tun farko.

Ya yi zargin cewa wasu daga cikin waɗannan matsaloli suna da alaka da kokarin raunana tasirinsa cikin jam’iyyar.

Sule Lamido ya ce matakan da ya ɗauka a kotu ba don neman mulki ba ne ko neman wata madafa ta shugabanci, face kare tsarin PDP da kuma kare haƙƙinsa na jam’iyya da ya ce an take su.

Ya dage cewa bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, Umar Damagum da Sanata Samuel Anyanwu su ne sahihan shugabannin PDP har zuwa ranar 8 ga Disamba, 2025 lokacin da wa’adinsu zai ƙare.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta kunno kai a ADC, an gargadi Atiku, Peter Obi da sauransu

Sule ya nemi hadin-kan 'yan PDP

'Dan siyasar ya yi gargadi cewa barin jam’iyyar cikin rudani da rashin sahihin jagoranci zai iya jefa ’yan takara, masu rike da mukamai, da masu neman takara cikin haɗari.

“Ni ina neman kafa kwamitin rikon kwarya. Ina kira ga Wike, Damagum da sauran shugabanni su yafewa juna, su goyi bayan samar da kwamitin rikon kwarya guda ɗaya.”

- Sule Lamido

Sule Lamido ya yi maganganu kan rikicin PDP
Babban jigo a jam'iyyar PDP, Sule Lamido Hoto: Sule Lamido
Source: Facebook

Sule Lamido ya bukaci shugabancin jam’iyyar ya kira taro na hadin gwiwa domin tattauna matsalolin jam’iyyar cikin gaskiya da neman hanyar da za ta dawo da ɗa’a, haɗin kai da amincewa a cikin jam’iyyar.

Ya kuma roƙi magoya bayansa da su kasance masu hakuri da natsuwa har zuwa 8 ga Disamba, yana mai cewa abubuwan da za su faru cikin kwanaki masu zuwa za su bayyana hanyar da jam’iyyar PDP za ta bi.

PDP: Sule ya musanta janye kara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya musanta janye karar da ya shigar da jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: PDP ta fatattaki Gwamna Bala da wasu gwamnoni 2 daga jam'iyyar

Sule Lamido ya karyata rahotannin da ke cewa ya janye karar domin ba PDP gudanar da babban taronta na kasa.

Tsohon gwamnan ya bayyana labarin cewa ya janye karar a matsayin karya tsagwaronta wadda babu kamshin gaskiya a cikinta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng