Manyan Hadakar Adawa Masu Niyyar Kifar da Tinubu Sun Shiga Tattaunawar Sirri

Manyan Hadakar Adawa Masu Niyyar Kifar da Tinubu Sun Shiga Tattaunawar Sirri

  • Manyan jagororin jam’iyyar ADC sun gudanar da muhimmin taro a sabon hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja
  • Taron ya samu halartar David Mark, Babachir Lawal, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi da sauran fitattun ’yan siyasa
  • Ana kyautata zaton taron ya shafi batun tsaro da gina dunkulalliyar adawa gabanin zaben 2027 inda za a fafata da APC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugabannin jam’iyyar ADC sun gudanar da wani muhimmin taro a Abuja, wanda ake ganin na iya zama daya daga cikin tarukan siyasar da za su ja hankalin kasa a shekarar nan.

Taron ya gudana ne a sabon hedikwatar ADC da aka kaddamar a unguwar Wuse, Abuja kwanaki kadan bayan Atiku Abubakar ya yanki tikitin jam'iyya.

Kara karanta wannan

Atiku: "Ba a taba jam'iyyar da ta azabtar da 'yan Najeriya kamar APC ba"

Manyan ADC sun sa labule
Wasu daga cikin manyan ADC a yayin wani taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Legit ta wallafa cewa Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata David Mark, ya jagoranci taron, tare da halartar tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan 'yan adawa sun hallarci taron ADC

Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon Gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai; da tsohon Gwamnan Jihar Ribass, Rotimi Amaechi sun halarci.

Haka nan tsohon shugaban jam’iyyar, Dr. Ralph Nwosu, da Sakataren Yada Labarai na Kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, sun halarta.

Duk da cewa ba a bayyana dalilin taron kai tsaye ba, majiyoyi sun nuna cewa tattaunawa kan tsananin rashin tsaro a kasar nan da ma sauran kalubale.

Haka kuma ana ganin taron zai mayar da hankali a kan shirin jam’iyyar gabanin zaben 2027 yayin da ake shirin raba Bola Tinubu da kujerar Shugaban kasa.

Jam'iyyar ADC na shirin kara hade kai

Taron ya zo ne kwanaki kadan bayan da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya karɓi katin rijista na jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya koma ADC

Majiyoyi sun shaida cewa taron cewa an hada taron don haɗa manyan masu ruwa da tsaki a cikin sabuwar dunkulalliyar tafiyar kifar da APC a 2027.

Ana tattauna batun kabe mulki daga APC
Wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar hamayya ta ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Wasu na ganin cewa haɗuwar David Mark, El-Rufai, Amaechi da Babachir Lawal a lokaci guda na nuna wani sabon salo na tsara adawa da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

A cewar majiyar jam’iyyar, akwai yiwuwar ana tattaunawa kan yadda za a gina karfin siyasa, dabarun yada sakonni, da kuma yadda za a janye hankalin ’yan Najeriya daga APC.

ADC ta dura a kan jam'iyyar APC

A baya, mun wallafa cewa shugaban ADC na ƙasa na kasa, David Mark, ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a karkashin APC da shirin dakile farin jinin da suka zo da shi kafin 2027.

Sanata Mark ya yi wannan zargi ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar lauyoyin ADC, karkashin jagorancin barrista Abdullahi Abdurrahman, inda ya ce su zauna da shiri.

Ya ce akwai yiwuwar amfani da tsarin shari’a na yawan zuwa kotu a matsayin makami domin kalubalantar jam’iyyar ADC, musamman yadda take samun karbuwa a sassa daban-daban na ƙasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng