Bayan Rushe Ofishin Kamfen Tinubu, Gwamna Ya Magantu kan Jita Jitar Barin APC

Bayan Rushe Ofishin Kamfen Tinubu, Gwamna Ya Magantu kan Jita Jitar Barin APC

  • Gwamna Hyacinth Alia ya fito ya yi magana game da yada jita-jita da ake yi a kafofin sadarwa wai ya shirya barin APC
  • Rabaren Alia ya musanya cewa ya sauya sheƙa, yana mai cewa an ƙirƙiro maganar ne domin bata masa suna da kawo ruɗani
  • Ya bayyana cewa ganawarsa da manyan jiga-jigai a Benue, cikin yunƙurin haɗa kai ne, ba don siyasa ko addini ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia ya yi magana da kansa bayan yada rahotanni cewa zai bar APC.

Gwamnan ya sake tabbatar da biyayyarsa ga jam’iyyar APC, inda ya karyata jita-jitar cewa ya sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya.

Gwamnan Benue ya karyata shirin barin APC
Gwamna Alia Hyacinth da Bola Tinubu. Hoto: Fr. Alia Iormen Hyacinth, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Martanin Gwamna Alia kan shirin barin APC

A jawabin da mai magana da yawunsa, Tersoo Kula ya wallafa a shafinsa na Facebook inda Alia ya bayyana labarin da cewa 'abin dariya, sharri kuma yunƙurin ɓatanci.'

Kara karanta wannan

Sace ɗalibai: Yadda mahaifin yara 3 da aka ɗauke ya mutu saboda bugun zuciya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya mayar da martani ne kan wani rahoton kafafen sada zumunta da ke cewa ya ziyarci tsohon Shugaban Majalisar Dattawa da kuma tsohon shugaban PDP, Sanata Iyorchia Ayu, domin tattauna sauya sheƙa.

Ya ce labarin karya ne da kuma siyasar ɓata suna da kuma karkatar da hankalinsa daga mulkin da yake aiwatarwa, tare da neman yaudaran Fadar Shugaban Kasa don wasu manufofi na siyasa.”

Sanarwar ta bayyana cewa ganawar da yake yi da shugabanni da dattawan jihar ciki har da Ayu na cikin yunƙurin haɗa kai ne, ba don siyasa ko wata manufa ta addini ba.

Sanarwar ta ce:

“Yanzu haka, bisa umarnin Gwamna, kusan dukkanin manyan shugabannin jam’iyyun adawa a Benue suna tarwatsewa suna koma wa APC.
"A dukkan kananan hukumomi ana samun tarukan sauya sheƙa, inda mutane masu tasiri ke barin tsofaffin jam’iyyunsu suna shiga APC da mutane masu dimbin yawa.”
“Gwamna Alia yana da cikakkiyar niyya wajen gina APC mai karfi da haɗin kai a Benue.”

Kara karanta wannan

Minista ya yi zazzafan martani ga APC a Kano, ya koya mata yadda ake siyasa

Gwamna ya soki masu yada wai zai bar APC
Gwamna Alia Hyacinth yana jawabi ga manema labarai. Hoto: Fr. Alia Iormen Hyacinth.
Source: Facebook

Shirin da gwamnan ke yi kan zaben 2027

Har ila yau, sanarwar ta ce gwamnan yana shirye ya tattauna da ko wane hamshakin abokin hamayyarsa don shigarsa jam’iyyar, a matsayin dabarar siyasa.

Ya ce hakan na da nasaba da nufin karfafa matsayin gwamnati da kuma shirye-shiryen 2027 ga kansa da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnan ya bukaci jama’a su yi watsi da labarin da ya yadu a kafafen sada zumunta, yana gargadin cewa irin waɗannan bayanan karya na iya jefa jama’a cikin rudani.

An rusa ofishin kamfen Tinubu a Benue

An ji cewa hukumar raya birane ta jihar Benue ta rusa wani bangare na ofishin yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu a birnin Makurdi.

Magoya bayan Tinubu sun bayyana hakan a matsayin mataki maras hujja, suna masu cewa su na da lasisin mallakar filin.

Gwamnatin jihar ta musanta cewa siyasa ce ta haddasa hakan, ta kuma bayyana dalilin daukar matakin rusa ofishin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.