Atiku: "Ba a Taba Jam'iyyar da Ta Azabtar da 'Yan Najeriya kamar APC ba"

Atiku: "Ba a Taba Jam'iyyar da Ta Azabtar da 'Yan Najeriya kamar APC ba"

  • Tsohon 'dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya zargi jam’iyyar APC da jefa Najeriya cikin talauci da tabarbarewa
  • Ya ce ba zai daina adawa da APC ba har sai an kore ta daga mulkin ƙasa saboda ceto 'yan kasar nan daga halin da ake ciki
  • Atiku ya bayyana wannan ne a lokacin da ya koma ADC a hukumance, yayin da ake daura damarar babban zabe mai zuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon dan takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana takaicinsa kan halin da Najeriya ta tsinci kanta.

Tsohon mataimakin Shugaban Kasa ba zargi jam’iyya mai mulki ta APC ta bar kasar cikin mawuyacin hali fiye da duk wani lokaci tun tarihin siyasar zamani.

Kara karanta wannan

Oshiomowhole: Tsohon shugaban APC ya yi wa Atiku shagube kan komawa ADC

Atiku Abubakar ya kulla aniyar kifar da APC
Alhaji Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Atiku Abubakar/Ajuri Ngelale
Source: Twitter

Atiku, wanda aka wallafa bayanansa a wani bidiyo da @jrnaib2 ya wallafa a shafin X, ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen ceto Najeriya daga barnar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya dura a kan APC

Atiku ya yi wannan jawabi jim kadan bayan ya koma jam’iyyar ADC a hukumance a jihar Adamawa, inda ya yi ikirarin cewa kuduri aniyar ceto kasar nan.

Ya ce zai dauki matakin ne don ganin an farfado da kasar nan kuma ya yi zargin cewa APC ta kuntata wa jama’a tafiye da kowace jam'iyyar siyasa a Najeriya.

Atiku ya yi takaicin halin da Najeriya
Tsohon dan takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku ya ce:

"Daga yau, na fara fada ke nan da jam'iyyar APC, azzalumar jam'iyya. Ba mu taba yin jam'iyya wacce ta cuci 'yan Najeriya, ta azabtar da 'yan Najeriya, ta talautar da 'yan Najeriya, ta kawo rashin tsaro a Najeriya, kamar jam'iyyar APC ba."

Jawabin Atiku na zuwa ne a lokacin da ya sauya sheka a hukumance, yayin da ake shirin tunkarar zaben 2027 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya koma ADC

Jama'a sun caccaki Atiku a X

Kalaman Atiku Abubakar sun jawo martani masu zafi daga masu amfani da shafukan sada zumunta,inda suka zarge shi da kawo APC kasar nan.

Mai amfani da X, @LekavelliL ya ce:

"Kowa ya san Atiku ba ya sha’awar zama shugaban kasa, yana tsayawa ne don hana samuwar shugaban kasa na yankin Igbo.

@realmexis ya yi tambaya:

“Shin ba Atiku ne ya taimaka wajen kawo APC mulki a 2015 ba?”

@NigIsland, wanda ya yi kakkausar suka, ya ce:

"Idan da gaske yana son ganin mugun abu, ya fara da kallon madubi."

Atiku ya koma ADC bayan barin PDP

A baya, mun wallafa cewa bayan dogon lokaci da barin PDP ba tare da bayyana sabuwar mafaka ba, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya koma ADC.

Wannan sauyin sheka ya zo ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaben 2027, inda Atiku ke daga cikin manyan jagororin hadakar ’yan adawa da ke neman kifar da gwamnatin APC.

Kara karanta wannan

Jira ya kare: Atiku ya sa lokacin zama dan jam'iyyar ADC bayan ya dade da barin PDP

Mai taimaka wa Atiku kan harkokin sadarwa, Abdulrasheed Shehu, ya ce Atiku ya zama cikakken 'dan ADC bayan karɓar katinsa na shiga jam’iyyar a garin Jada na jihar Adamawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng