Magana Ta Kare: Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar Ya Koma ADC
- A karshe dai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yanki katin zama cikakken dan jam'iyyar ADC a jihar Adamawa
- Tun a watan Yulin 2025, Atiku ya fice daga PDP saboda jam'iyyar ta sauka daga kan akidun da aka kafa ta a kansu a shekarar 1998
- Dubban magoya baya ne suka tarbi Atiku lokacin da ya isa wurin da zai karbi katin jam'iyyar ADC a yau Litinin, 24 ga watan Nuwamba, 2025
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Adamawa, Nigeria - Bayan tsawon lokaci, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC a hukumance.

Kara karanta wannan
Jira ya kare: Atiku ya sa lokacin zama dan jam'iyyar ADC bayan ya dade da barin PDP
Atiku, wanda ya jima da barin jam'iyyar PDP, yana daya daga cikin jagororin hadakar 'yan adawa, wadanda suka kudiri aniyar kifar da gwamnatin APC a zaben 2027.

Source: Twitter
Mai taimaka wa Atiku kan harkokin sadarwa, Abdulrasheed Shehu ya tabbatar da komawar Wazirin Adamawa ADC a shafinsa na X yau Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka tarbi Atiku a Adamawa
Tun farko Atiku Abubakar ya isa garin Jada a Jihar Adamawa da safiyar Litinin domin karɓar katin zama cikakken mamba na jam’iyyar ADC, inda aka tarbe shi cikin gagarumin farin ciki daga magoya bayansa.
Bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna jerin gwanon motocinsa na shiga Jada, yayin da magoya baya ke ta shewa, buga ganguna da rera waka.
Wasu daga cikinsu na ɗauke da fastocinsa tare da rubuce-rubuce irin su “Welcome Daddy”, yayin da Atiku ke daga hannu yana gaisawa da masu tarba daga cikin motarsa.
Atiku ya tabbatar da zai koma ADC
Atiku ya nuna alamun zai karbi katin zama cikakken dan jam'iyya a wurin ganawarsa da shugabannin ADC a Yola, inda ya ce:
"Kun san cewa akwai sabuwar tafiyar siyasa a Najeriya, ko ba haka ba? Wannan tafiya ina ta kai mu? ADC, don haka mutanen Adamawa da Najeriya, jam’iyyarmu yanzu ita ce ADC.
“A ranar Litinin zan koma ADC a hukumance. A da ban shiga ba; kun riga ni shiga jam'iyyar, ina so na sani, shin za ku karɓe ni?”
Kuma jama’a suka amsa da ƙarfi da cewa, “Eh!”

Source: Twitter
Atiku ya zama dan ADC a hukumance
Kamar yadda ya ambata a wannan taro, tsohon mataimakin shugaban kasar ya yanki katin zama cikakken dan ADC a mazabar Jada da ke Adamawa yau Litinin.
"Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shiga jam'iyyar ADC a wani sabon yunkuri na siyasa," in ji Abdulrasheed.
A watan Yulin 2025 Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP, kuma bayan nazari da kammala duk wasu shirye-shirye, ya koma jam'iyyar hadaka, ADC.
Rigima ta kunno kai a jam'iyyar ADC
A wani labarin, kun ji cewa wani sabon rikici ya sake kunno kai a jam’iyyar ADC mai adawa yayin da ake shirin tunkarar zaben 2027
Tsagin ADC da ke goyon bayan shugaban rikon kwarya, Nafiu Bala, ya gargadi fitattun ’yan adawa ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi, da Nasir El-Rufa’i da su guji kokarin kwace jam’iyyar.
Bayan haka, tsagin Nafiu Bala ya soki hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan amincewa da shugabancin Sanata David Mark.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

