Daruruwan 'Yan NNPP Sun Watsewa Kwankwaso a Kano, Sun Koma APC
- Rahotanni na nun da cewa daruruwan mambobin jam’iyyar NNPP sun koma APC a gundumar Rimin Gado a Kano
- Rabiu Sulaiman Bichi da ya karbe su ya bayyana cewa matakin ya nuna sun dauki muhimmiyar shawara ta siyasa
- Shugaban masu sauyin sheka, Mohammad Karofin-Yashi, ya bayyana dalilin da ya sa suka dauki matakin shiga APC
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Jam’iyyar APC ta karɓi sababbin mambobi 774 da suka sauya sheka daga jam’iyyar NNPP a gundumar Rimin Gado da ke jihar Kano.
Taron karɓar mutanen ya samu halartar shugaban hukumar tafkin Hadejia-Jam’are, Dr. Rabiu Sulaiman Bichi, wanda ya jagoranci taron.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa a wajen bikin, Rabiu Bichi ya bayyana wadannan sababbin mambobi da cewa sun yi sa’ar daukar shawara mai kyau.
Bichi ya jaddada cewa jam’iyyar APC ce kadai za ta iya tafiyar da Najeriya zuwa ci gaba mai dorewa da ake bukata.
Abin da ya sa 'yan NNPP komawa APC
Rabiu Bichi ya ce nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu musamman a Arewa suna tabbatar da cewa APC na kan hanyar ceto kasar nan.
Ya kuma danganta sauyin shekar wadannan mutane da irin kyakkyawan aikin da gwamnatin APC ke yi, musamman a Kano, inda ya bayyana cewa an kammala manyan ayyuka fiye da 18.
Rabiu Bichi ya yaba wa Bola Tinubu
A cewar Dr. Rabiu Bichi, gwamnatin tarayya ta kasance tana sakin makudan kudi domin tallafawa jihohi wajen ci gaba.
Saboda haka, ya yi nuni da cewa mulkin jam’iyyar APC na kasa yana ci gaba da samar da cigaba a fannonin da suka shafi ci gaban al’umma.

Source: UGC
Ya kara da cewa tsarin Renewed Hope na gwamnatin Tinubu ya samar da sauye-sauye masu amfani, musamman wajen farfado da tattalin arziki da tsaron abinci ta hanyar shirye-shiryen noma.
Bichi ya tabbatar wa sababbin mambobin cewa za a karbe su hannun biyu-biyu, tare da basu dukkan damar da suke samu kamar kowane tsohon dan jam’iyya.
Bayanin masu sauya sheka zuwa APC
Shugaban mutane 774 da suka koma APC, Mohammad Karofin-Yashi, ya bayyana cewa matakin da suka dauka ya samo asali ne daga ganin irin ci gaban da jam’iyyar APC ke kawowa jihohi.
Daily Post ta wallafa cewa Mohammad Karofin-Yashi ya ce suna da tabbacin cewa jam'iyyar APC ce za ta kai Kano da Najeriya gaba.
Ya bayyana cewa matakinsu ba na wucin gadi ba ne, domin sun yi nazari mai zurfi game da al’amuran siyasar kasar nan, kuma sun ga dacewar komawa jam’iyyar da ke da tsari.
Shugaban masu sauyin shekar ya kara da cewa suna da niyyar jawo karin mambobin NNPP da za su sake sauya sheka cikin kwanaki masu zuwa.
'Dan majalisar Kano ya ziyarci Ganduje
A wan rahoton, kun ji cewa dan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal ya ziyarci tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje.
Sagir Ibrahim Koki ya kai wa Abdullahi Ganduje ziyara ne bayan sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.
Bayan ziyarar, dan majalisar ya bayyana wa manema labarai cewa a yanzu Ganduje ne jagoransu a siyasar jihar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


