Bayan Dogon Lokaci, Jonathan Ya Fadi Babban Dalilin da Ya Sa Ya Ja Baya daga Shiga Siyasa

Bayan Dogon Lokaci, Jonathan Ya Fadi Babban Dalilin da Ya Sa Ya Ja Baya daga Shiga Siyasa

  • Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi tsokaci kan dalilin da ya sanya ya yi baya-baya da harkokin siyasa
  • Dr. Goodluck Jonathan ya bayyana cewa aikin da yake yi tare da wata kungiya ne ya sanya dole ya ja baya da siyasa
  • Tsohon shugaban kasar ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu mutane ke neman mukaman shugabanci ba tare da wata kwarewa ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana dalilin da ya sa ya daina shiga harkokin siyasa kai tsaye a ’yan shekarun nan.

Jonathan ya bayyana cewa rawar da yake takawa a matsayin mamba a kungiyar West African Elders Forum (WAEF) na bukatar tsantsar rashin nuna goyon baya ga wani bangare.

Jonathan ya fadi dalilin daina shiga siyasa
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce Jonathan ya yi wannan bayani ne a wani taro da aka gudanar a Abuja domin bikin cika shekara 10 da kafuwar gidauniyar Goodluck Jonathan Foundation (GJF).

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda Jonathan ya ceto siyasar Najeriya da taimakonsa da ya yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kuma shirya liyafar cin abincin dare domin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta cika shekara 68.

Meyasa Jonathan ya daina shiga siyasa?

Jonathan ya bayyana cewa zama mamba na WAEF yana zuwa ne da sharadi ɗaya mai tsauri, ba za ka ci gaba da shiga siyasa ta jam’iyya ba.

Ya bayyana WAEF a matsayin wata kungiya ta diflomasiyya, wacce ta ƙunshi tsofaffin shugabannin kasashen Yammacin Afrika, masu zuwa kasashe a lokutan zaɓe domin sasanta rikici da kauce wa tashin hankali daga rashin kyakkyawan gudanar da zaɓe.

“Manufarmu ita ce mu sa ido a kan zaɓe, amma ba mu cikin jerin masu sa ido kai tsaye. Muna zuwa ne domin idan muka ga wani abu na neman rikicewa, mu shiga tsakani kafin ya rikide ya zama babban rikici.”

- Goodluck Jonathan

Ya bayyana cewa sharuddan zama mamba sun haɗa da kasancewa tsohon shugaban kasa a yankin Afrika ta Yamma da kuma kasancewa tsohon shugaban kungiyar ECOWAS, labarin ya zo a The Punch.

Kara karanta wannan

PDP ta fara adawa mai zafi, ta ragargaji Tinubu kan sace dalibai a Kebbi

“Wani sharadi shi ne ba za ka ci gaba da zama ɗan siyasa ba. Wannan ne dalilin da ya sa na bata ran wasu abokan siyasa ta." "Suna tsammanina zan koma siyasa, amma kafin na yi hakan, sai na fara yin murabus daga WAEF.”

- Goodluck Jonathan

Jonathan ya koka kan yadda ake siyasa

A game da lamurran cikin gida, Jonathan ya nuna takaici kan yadda siyasa ke tabarbarewa, yana kira ga ’yan siyasa da su rika nuna kwarewa da mutunci.

Ya soki yadda wasu mutane ke neman mukaman jagoranci ba tare da shiri, horo ko kwarewa ba, sabani da sauran fannoni da ke bukatar takardar shaida kafin mutum ya yi aiki.

“Dole mu canja yanayin siyasa. Ya kamata mu ga siyasa a matsayin aiki na mutanen da ke da alhakin jagoranci.”

- Goodluck Jonathan

Jonathan ya soki sace dalibai
Goodluck Jonathan zaune a wajen wani taron jami'a Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Jonathan ya yi Allah wadai da sace dalibai

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi Allah-wadai da sace ’yan mata 25 a jihar Kebbi, yana mai cewa lamarin ya tuna masa da sace ’yan matan Chibok lokacin mulkinsa.

Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya faru da su, ciki har da iyalan mataimakin shugaban makarantar da aka kashe, tare da kira ga yin addu’a domin a dawo da wadanda aka sace cikin aminci.

Kara karanta wannan

Tinubu ya taya Jonathan murnar cika shekaru 68, ya fadi kyawawan halayensa

Shugaba Tinubu ya yabawa Jonathan

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Shugaba Tinubu ya yaba kan gudummawar da ya bai wa kasar nan tun daga lokacin yana kan mulki har zuwa yau, wanda ya kara darajar Najeriya da dimukaradiyyarta a idon duniya.

Mai girma Tinubu Shugaba Tinubu ya ce saukin hali da natsuwa sun kasance ginshikin jagorancin Jonathan, musamman yadda ya nuna salon kishin kasa a zaben 2015.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng