Reshe Ya Juye: Fiye da Magoya bayan Jam'iyyar APC 1,600 Sun Sauya Sheka a Jigawa

Reshe Ya Juye: Fiye da Magoya bayan Jam'iyyar APC 1,600 Sun Sauya Sheka a Jigawa

  • Fiye da magoya bayan jam'iyyar APC 1,600 ne suka sauya sheka zuwa PDP mai adawa a wani gangami da aka gudanar a Jigawa
  • Mataimakin shugaban PDP a jihar ya bayyana cewa kwace mutum 1,600 daga APC zai matukar taimaka masu a zabukan gaba
  • Wadanda suka sauya sheƙar sun ce sun koma PDP ne saboda gwamnatin APC ta gaza samar da ayyuka da saukin rayuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jigawa - Fiye da mutane 1,600 da ke goyon bayan jam'iyya mai mulki ta APC a jihar Jigawa sun sauya sheƙa zuwa PDP.

Wadannan 'yan siyasar 1,6000 sun fice daga APC zuwa PDP a wani gagarumin gangami da aka gudanar a Limawa, karamar hukumar Dutse.

Jam'iyyar PDP ta kwace magoya bayan APC 1,600 a jihar Jigawa.
Hoton wani gangamin jam'iyyar PDP da aka gudanar a jihar Osun. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Jigawa: Magoya bayan APC sun koma PDP

Kara karanta wannan

Daruruwan 'yan NNPP sun watsewa Kwankwaso a Kano, sun koma APC

Wannan ya faru ne a ranar Juma’a, inda dubban mutane suka taru domin shaida canjin siyasar da ake kira “babbar guguwar sauyi” a APC, in ji rahoton Punch.

Rahotanni sun nuna cewa matasa, maza da mata daga yankuna daban-daban na Limawa sun hallara da tutar PDP, inda suka bayyana cewar sun gaji da “alkawuran APC da ba a taɓa cika wa ba.”

Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Jigawa, Hon. Umar Danjani ne ya karɓi masu sauya sheƙar, yana mai cewa adadin wadanda suka sauya shekan ya girgiza siyasar Dutse.

Dalilin sauya sheƙar mutane 1,600 daga APC

A jawabinsa, Danjani ya bayyana cewa Limawa ba babban yanki ne da APC ke takama da shi, domin daga nan ne suka fitar mai tallafawa gwamna kan harkokin dalibai, da kuma dan majalisar Dutse a majalisar dokokin jiha.

Don haka, a cewar mataimakin shugaban jam'iyyar, rasa mutum 1,600 daga wannan yanki “babbar asara ce ga APC.”

Danjani ya ce:

“Mutane 1,600 ne suka bar APC. Wannan ya nuna yadda jama'a ke cike da fushin yadda APC ta kawo rabuwar kai, ta bar talakawa cikin yunwa, rashin aiki da rashin tsaro.”

Kara karanta wannan

Tirkashi: Shugaban jam'iyyar PDP, ƴan majalisa 16, kwamishinoni 22 sun koma APC

Ya ƙara da cewa PDP za ta yi amfani da wannan karfin ne domin kwato Jigawa daga gwamnatin da ta yi sakaci ga ci gaban al'umma.

Wannan sauya sheka ya girgiza jam'iyyar APC a jihar Jigawa.
Hoton tutar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: UGC

Me ya janyo mutane suka fice daga APC?

Jagoran masu sauya sheƙar, Umar Abubakar (Young Danmodi), ya bayyana dalilan da ya sa suka fice daga APC zuwa PDP:

“Mun bar APC ne saboda alkawuran da suka gagara cikawa. Mun tsaya tsayin daka tsawon shekaru a jam'iyyar, ba wani ci gaba, ba ayyuka, kuma ba a sauraren jama'a.
“Duk da cewa Limawa na da manyan jiga-jigan APC, hakan ba zai hana mu jawo sauran magoya baya su koma PDP domin a ceci jama’a ba.”

- Umar Abubakar (Young Danmodi).

Abubakar ya bayyana cewa jama'ar Limawa sun gaji da halin ko in kula daga gwamnati, a cewarsa, an gaza gyara tituna, ba matasa aiki da samar masu walwala a yankin.

PDP ta yi wa APC lahani a Jigawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, daruruwan 'yan siyasa da ke goyon bayan APC a gundumar Sakwaya cikin karamar hukumar Dutse, a Jigawa sun koma PDP.

Kara karanta wannan

Sule lamido ya fadi matsayarsa kan taron PDP da ya nemi kotu ta dakatar

Mataimakin shugaban PDP na jihar, Umar Danjani ne ya wakilci shugaban jam’iyyar na jihar domin tarbar sababbin mambobin da suka bar APC.

Hajiya Harira Sakwaya, jagorar sababbin mambobin da suka sauya sheka, a bayyana cewa jam’iyyar APC ta gaza a jihar, lamarin da ya tilasta masu neman mafita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com