Hankalin Wike Ya Tashi da Ya Ji PDP Ta Kira Trump, Ya Yi Martani
- Ministan harkokin Abuja Nyesom Wike ya karyata ikirarin cewa dimokuraɗiyyar Najeriya na cikin hatsari a kan rikicin PDP
- Ya ce furucin shugaban PDP, Tanimu Turaki game da kiran Donald Trump batu ne da zai iya tayar da tarzoma da lalata sunan ƙasa
- A daya bangaren kuma, Nyesom Wike ya gargadi sabuwar hukumar SSDC da aka kafa da kada ta bari siyasa ta kassara aikinta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ce dimokuraɗiyyar Najeriya ba ta fuskantar kowace irin barazana.
Wike ya yi martani ne bayan shugaban jam’iyyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki ya ce kasar na bukatar agajin Donald Trump na Amurka.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Wike ya ce furucin shugaban PDP kan kiran Trump siyasa ne kawai kuma zai iya tayar da hargitsi a ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba yayin da ya karɓi shugabanni da kwamitin gudanarwa na hukumar SSDC.
Martanin Wike kan kiran Trump Najeriya
A jawabinsa, Nyesom Wike ya mayar da martani ga shugaban PDP, Tanimu Turaki kan kalamansa da ya kira masu “hadari ga tsaron ƙasa”.
Turaki ya yi ikirarin cewa Kiristoci na fuskantar kisan kare-dangi a Najeriya, sannan daga bisani ya ce dimokuraɗiyyar ƙasar tana bukatar taimakon ƙasashen waje domin ci gaba da wanzuwa.
Wike ya ce:
“Ku duba abin da wani ya fada jiya. Kuna rikici a jam’iyyarku, amma sai ka fito a talabijin ka ce ana kisan kare-dangi ga Kiristoci.
"Kai dai kana gaya wa duniya cewa gwamnatin nan na aikata kisan kare-dangi. Idan jami’an tsaro suka gayyace ka don ka yi bayani, sai a ce ‘ana son a kashe shi’.
"Wannan barazana ce ga tsaron ƙasa. Wasu ma suna kira ga Trump ya zo ya ‘cece su kan dimokuraɗiyya’. Yaya za ka kira baƙo ya cece ka alhali kai baka bin umarnin kotu?”
Ministan ya ce furucin na ƙarya ne da zai bata sunan Najeriya a idon duniya, yana mai cewa dimokuraɗiyyar ƙasar za ta ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali.
Maganar Wike kan rikicin jam'iyyar PDP
Wike ya kara da cewa rikicin PDP da ake magana a kai bai shafi tsarin mulki ba, ya ce matsalar siyasar mutanen da ba sa iya sarrafa gidajensu ne suke son bata sunan gwamnati.

Source: Twitter
A bidiyon da Imaran Muhammad ya wallafa a X, Wike ya ce:
“Ba za ka iya gyara gidanka ba, sai ka daura wa wasu alhakin gazawarka. Rashin bin doka ba zai cigaba da wanzuwa ba.”
Wike ya gargadi hukumar SSDC
Wike ya yi gargadin cewa kada SSDC ta bari siyasa, bambance-bambance ko matsin lamba daga waje su kawo tarnaki ga aikinta.
Ya tuna cewa wasu hukumomin cigaba a baya sun durƙushe ne saboda rashawa, rabuwar kai da jagoranci mara inganci.
Manyan Najeriya sun isa kasar Amurka
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta tura tawaga mai karfi kasar Amurka kan zargin kisan Kiristoci.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne ya jagoranci tawagar kuma sun gana da 'yan siyasar Amurka.
Tawagar Najeriya da ta hada da hafsun tsaro, sufeton 'yan sanda ta bayyana matsayin kasar game da rashin tsaro a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


