Hon. Bichi Ya Gigita Kwankwasiyya a Jihar Kano, Ya Fice daga Jam'iyyar NNPP

Hon. Bichi Ya Gigita Kwankwasiyya a Jihar Kano, Ya Fice daga Jam'iyyar NNPP

  • Babban jigon siyasa a karamar karamar hukumar Bichi, Hon. Jamilu Kabir Bichi ya fice daga jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano
  • 'Dan siyasar, mai rike da sarautar Tafidan Bichi ya zargi NNPP da rashin yi masa adalci duk da irin gudummuwar da ya bayar har ta karbi mulki
  • Ya ce duk da rabuwa da NNPP mataki ne mai wahalar dauka, amma ba zai ci gaba da zama a jam'iyyar da ba a ganin mutuncinsa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Fitaccen jigo a NNPP daga karamar hukumar Bichi a jihar Kano, Hon. Jamilu Kabir Bichi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

Jamilu, wanda ake ganin yana cikin manyan kusoshin da suka taimaki NNPP, ya yi zargin cewa babu adalci a tafiyar jam'iyyar, kuma an yi watsi da shi duk da gudummawar da ya bada.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: PDP ta fatattaki Gwamna Bala da wasu gwamnoni 2 daga jam'iyyar

Jamilu Kabir Bichi
Hoton Hon. jamilu Kabir Bichi, wanda ya fice daga NNPP a Kano Hoto: Hon. Jamilu Kabir Bichi
Source: Facebook

A rahoton Daily Trust, an ji Hon Jamilu ya kuma zargi gwamnatin NNPP ta Kano da rashin karrama mambobin da suka yi wa jam’iyyar hidima tun kafin ta hau mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jamilu Kabir, wanda ya jagoranci kwamitin kamfen NNPP na zaben 2023 a yankin Bichi, ya mika takardar murabus dinsa a ranar 19 ga Nuwamba, 2025, ga shugaban jam’iyyar na mazabarsa.

Dalilin Hon. Jamilu Bichi na barin NNPP

A cikin wasikar, ya bayyana cewa matakin da ya dauka na fita daga NNPP ba abu ne mai sauki ba, amma ya zame masa dole saboda yadda da aka yi watsi da shi da magoya bayansa musamman a garinsu.

"Abin da shugabanni suka mana na kin karrama kokarinmu, biyayyar da muka nuna, hakuri da jajircewarmu, abu ne mai matukar bata rai,” in ji shi.

Jamilu Kabir ya koka cewa mambobin da suka sha wahala wajen gina jam’iyyar, suka yi aiki tukuru domin samun nasarar NNPP a zabe, ba su amfana da komai ba daga cikin mukaman jam’iyya ko na gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi ya daukarwa iyayen yaran da aka sace alkawari

"A matsayina na mutum mai tsayawa a kan ka’ida, ba zan iya cigaba da zama cikin jam’iyyar da ta sabawa nagarta da akida ta ba.

Jigon ya gode wa ubangidansa

Jamilu Kabir Bichi ya mika sakon godiya ga ubangidansa na siyasa, tsohon Ministan Ciniki da Masana’antu, Hon. Ahmad Garba Bichi.

Fitaccen dan siyasar ya kuma sake jaddada kudurinsa na yin “siyasa ba tare da kiyayya ba.”

A karshe, ya yi addu'ar Allah ya jagoranci al’ummar Bichi, Kano da Najeriya baki daya, yana mai cewa zai ci gaba da rike akidar yin siyasa don amfanar da al’umma ba don son rai ba.

Kabir Bichi da Abba.
Hoton Hon. Jamilu Kabur Bichi da Gwamna Abba Kabur Yusuf a wurin taro a Kano Hoto: Hon. Jamilu Kabir Bichi
Source: Facebook

'Yan NNPP akalla 650 sun koma APC

Ku na da labarin cewa aƙalla jiga-jigan NNPP da mambobi sama da 650 sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a Jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa sauyin sheƙar ta faru ne a unguwar Gobirawa da ke ƙaramar hukumar Dala, tare da wasu yankuna na kananan hukumomin Fagge da Ungoggo.

Da yake jawabi a madadin masu sauya sheka, Ahmad Gobirawa ya ce sun yanke shawarar komawa APC ne bayan ganin nasarorin da Shugaba Tinubu ya samu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262