Gwamna Ya Tona Silar Rikicinsa da Wike: “Ba Za Mu Bari Najeriya Ta Zama Jam’iyya 1 ba”

Gwamna Ya Tona Silar Rikicinsa da Wike: “Ba Za Mu Bari Najeriya Ta Zama Jam’iyya 1 ba”

  • Gwamna Seyi Makinde ya ce rikicin PDP ya wuce batun jam’iyya, yana da nasaba da kare dimokuraɗiyya daga wasu bata-gari
  • Makinde ya ce an gina Najeriya ne a kan tsarin jam’iyyu da dama, amma wasu na kokarin kakaba jam'iyya daya a kasar
  • Gwamna ya kuma yi tsokaci game da rikicinsa da Wike, yana mai cewa rikici ne kan makomar dimokuraɗiyyar Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya fito fili ya bayyana cewa rikicin da ke cikin PDP ya shafi makomar dimokuraɗiyyar Najeriya, ba wai batun jam’iyya kawai ba.

Ya ce rikicin ya ƙara bayyana yunkurin wasu shugabanni na ƙoƙarin juyar da ƙasar zuwa tsarin jam’iyya ɗaya, wanda ya saba wa tsarin da aka gina kasar a kai.

Kara karanta wannan

Ran APC ya baci, ta dura kan PDP bayan saboda taimakon Trump a Najeriya

Gwamna Makinde ya yi magana game da shirin wasu na kakaba tsarin jam'iyyar 1 a Najeriya.
Hoton gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da na ministan Abuja, Nyesom Wike. Hoto: @seyiamakinde, @GovWike
Source: Facebook

Gwamna Makinde ya ce dole a tsaya tsayin daka don kare tsarin jam’iyyu daga ire-iren wadannan shugabanni, in ji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makinde ya yi magana kan rigimarsa da Wike

Gwamnan na Oyo ya yi magana ne a lokacin da rikici ya barke a sakatariyar PDP da ke Abuja, inda ‘yan bangarori biyu suka yi turmutsutsu kan shugabanci.

Makinde ya zargi tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike da kokarin kakaba jam'iyya daya a Najeriya, wanda a cewarsa, ya saba da kudurin 'yan mazan jiya.

Da aka tambaye shi game da rashin jituwarsa da Wike, la'akari da cewa su aminai ne gabanin zaben 2023 kuma mambobi ne na kungiyar G5, Makinde ya ce:

"Eh to, masu karamin tunani ba su da aiki sai maganar mutane. Masu matsakaicin tunani ba su da aiki sai kananan maganganu. Mu mun fi gane wa yin magana kan matsaloli."

Gwamnan ya kara da cewa bai damu da takaddamarsu da Wike ba, domin matsalar ba kan mutum ɗaya ta tsaya ba, matsala ce ta makomar kasar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Halin da ake ciki bayan jibge jami'an tsaro a hedkwatar PDP

Makinde: “Ba za mu yarda da jam’iyya 1 ba”

Makinde ya ce manyan ‘yan PDP na da alhakin tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta ci gaba da kasancewa bisa doka, domin hakan ne mafi alheri ga zabukan da suka gabata da kuma masu zuwa.

Gwamna Seyi Makinde ya ce ba za su yarda a kakaba tsarin jam'iyyar daya a Najeriya ba.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya na jawabi a wani taro a Ibadan. Hoto: @seyiamakinde
Source: Facebook

Ya jaddada cewa manufarsu ita ce tabbatar da cewa kowa na da zaɓi mai inganci, inda yake cewa:

“Matsalar ba ta gina mutum ko wata ƙungiya ba ce. Abin da muka mayar da hankali a kai shi ne kare tsarin jam’iyyu ba wai jam'iyya daya ba a Najeriya.”

Gwamnan ya yi nuni da cewa sai an bi hanyar shari’a da doka wajen warware rikicin PDP domin kada a maimaita kuskuren baya, in ji rahoton Daily Post.

Ya ce su a matsayinsu na gwamnoni, za su ci gaba da tsayawa kan gaskiya don kare mutuncin jam’iyyar da dakile masu ƙoƙarin tilasta jam’iyya ɗaya a ƙasar.

Yadda rikicin PDP ya ƙara muni a Abuja

Tun da fari, mun ruwaito cewa, a ranar Talata, rikicin PDP ya yi kamari bayan fitowar sanarwa daban-daban na zaman NEC daga bangarorin Sanata Sam Anyanwu da Tanimu Turaki.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'

Gwamna Seyi Makinde da Bala Mohammed na Bauchi sun tsaya kai-da-fata a bakin sakatariyar, yayin da Nyesom Wike ya iso da tsaro mai ƙarfi.

An ce jami'an tsaro da aka tura wurin sun yi kokarin shawo kan rikicin da ya barke, tare da umartar duka shugabannin PDP sun tattara su bar harabar Wadata Plaza.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Sani Hamza, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com