Abba Ko Barau: 'Yan Majalisar Kano Sun Bayyana Dan Takararsu na Gwamna a 2027

Abba Ko Barau: 'Yan Majalisar Kano Sun Bayyana Dan Takararsu na Gwamna a 2027

  • Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Kano sun bayyana matsayarsu kan 'dan takarar gwamnan da suke goyon baya a zaben 2027
  • 'Yan majalisar da suka hada da tsofaffi da masu ci yanzu sun nuna goyon bayansu ga Sanata Barau Jibrin domin ya fito takarar gwamna
  • Shugaban kungiyar 'yan majalisar ya bayyana dalilai uku da suka sanya suke goyon bayan Sanatan ya fito takara a karkashin jam'iyyar APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Wasu 'yan majalisar dokokin jihar Kano da suka hada da tsofaffi da masu ci yanzu, sun amince Sanata Barau Jibrin ya fito takara.

'Yan majalisar sun nuna goyon bayansu ga mataimakin shugaban majalisar dattawan ya fito takarar gwamnan Kano a zaben shekarar 2027.

'Yan majalisa sun goyi bayan takarar Barau a 2027
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin Hoto: @barauijibrin
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa 'yan majalisar sun bayyana hakan ne yayin wata ziyara da suka kai wa Sanata Barau.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta yi magana da Allah ya yi wa sanata rasuwa a cikin dare

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa suke goyon bayan Barau Jibrin?

Mutanen wadanda sun fi 200 sun haɗa da ’yan majalisar dokoki daga 1999 zuwa yau, na karkashin jagorancin tsohon kakakin majalisar, Rt. Hon. Abdulaziz G. Gafasa (2007–2011), rahoton jaridar The Sun ya tabbatar da labarin.

Sun bayyana Sanata Barau a matsayin ɗan takarar da ya fi dacewa kuma mafi karɓuwa a jam’iyyar APC a Kano.

Har yanzu dai Sanata Barau, wanda ya dade a majalisa, bai bayyana aniyarsa ta takarar gwamna ba tukuna.

Amma muhimman shugabanni da masu ruwa da tsaki na APC a jihar sun nuna goyon bayansu gare shi, bisa la’akari da irin rawar da ya taka a majalisar dattawa cikin shekaru 10 da suka gabata.

“Mun zo ne mu bayyana cewa muna goyon bayanka saboda dalilai uku: Na farko, ka yi abubuwan kirki ga mutanenmu a dukkan yankunan Sanata uku na jihar Kano."
"Na biyu, ka kasance ginshiki ga jam’iyyarmu APC. Na uku, ka taɓa rayuwarmu kai tsaye, ko da yake ba kowa a cikinmu ya fito daga yankin da ka ke wakilta ba. Wannan ya sa ka zama ɗan takarar da ya fi dacewa a APC.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Sanatan Amurka ya taso gwamnati a gaba kan sace dalibai a Kebbi

- Hon Abdul'aziz G. Gafasa

A nasa jawabin, wani dan majalisar Kano da ke kan kujerarsa yanzu, Hon. Garba Yau Gwarmai na mazabar Ghari/Tsanyawa, ya ce za su tashi tsaye wajen wayar da kai da kuma tunkarar jama’a domin ganin Sanata Barau ya samu nasara a 2027.

Sanata Barau ya samu goyon baya kan zaben 2027
Sanata Barau Jibrin na jawabi a wajen wani taro Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Sanata Barau Jibrin ya yi godiya

Da yake mayar da martani, Sanata Barau ya gode musu sosai kan goyon bayan da suka nuna masa, yana mai cewa dole ne kowa ya haɗa kai domin dawo da martabar da Kano ta yi suna da ita a baya.

Ya bayyana su a matsayin manyan ’yan siyasa masu mutane, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da tallafa wa manufofin jam’iyyar APC da kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR.

Shirin jam'iyyar APC kan Kano a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai ba mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, shawara, Alwan Hassan, ya ce jam'iyyar APC za ta karbi Kano a 2027.

Kara karanta wannan

Sulhu ya yi rana: 'Yan bindiga sun sako mutanen da suka sace a Katsina

Alwan Hassan ya ce yana da cikakken tabbacin cewa jam’iyyar APC za ta karɓe mulkin jihar Kano daga NNPP a zaɓen 2027 saboda sabon shirin da take yi.

Jigon na APC ya ce yanzu haka ana haɗa kan manyan ’yan siyasa a fadin jihar domin tunkarar babban zaben da ke tafe don kifar da NNPP.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng