Zaben 2027: Baba Adinni Ya Ba Limamai Shawara kan Tazarcen Tinubu

Zaben 2027: Baba Adinni Ya Ba Limamai Shawara kan Tazarcen Tinubu

  • Baba Adinni na Legas, Sikiru Alabi-Macfoy, ya yi kira ga limaman Yarbawa su bada gudunmawa wajen ganin Bola Tinubu ya koma mulki
  • Alhaji Sikiru Alabi-Macfoy ya bukaci a kafa cibiyar adana tarihin Musulunci da littattafai na zamani a Legas da yankin Kudu maso Yamma
  • Hakazalika jagoran addinin ya ja hankalin Musulmi su shirya tun yanzu kada abin da ya faru a zaben da ya gabata ya maimaita kansa

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Baba Adinni na Legas, Alhaji Sikiru Alabi-Macfoy, ya yi kira ga limaman Yarbawa kan sake zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Alhaji Sikiru Alabi-Macfoy ya bukaci limaman na Yarbawa da su himmatu sosai wajen tabbatar da sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.

Baba Adinni ya bukaci a sake zaben Tinubu a 2027
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta ce ya bayyana hakan ne a jawabinsa na fatan alheri a taron “Raabitah Eko 2025” da kungiyar limaman ta shirya a Legas.

Kara karanta wannan

An sake rashin babban dan kasuwa a Kano, Abba Kabir ya tura sakon ta'aziyya

Wace shawara Baba Adinni ya bada?

Alhaji Sikiru Alabi-Macfoy ya bukaci limaman yankin su kafa cibiyar musamman da za ta adana tarihin Musulunci, muhimman bayanai, abubuwan tarihi, musamman wadanda suka shafi Najeriya da Kudu maso Yamma.

Baba Adinnin ya kuma nemi kungiyar ta buɗe cibiyar karatu ta zamani domin tattara bayanai da abubuwan da suka shafi Musulunci musamman a Legas da Najeriya gaba ɗaya.

Hakazalika, ya bayyana cewa zai taimaka wajen kafa kwamiti domin ganin an cika wannan buri, rahoton sunrise.ng ya tabbatar da labarin.

Ya shawarci Musulmai da su shirya tun wuri game da zaben 2027, tare da gujewa sake faruwar abin da ya sa jam’iyyar adawa ta lashe jihar Legas a zaben da ya gabata na shekarar 2023, duk da cewa ita ce mahaifar Shugaba Tinubu.

Ya bayyana yadda babban masallacin Legas ya jagoranci tunkude matsalolin siyasa ta hanyar hada kungiyoyi, cibiyoyi da al’ummomi na Musulunci waje guda.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya mika bukatarsa ga jami'an tsaro kan 'yan ta'adda

A cewarsa wannan matakin ya taimaka wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar APC da kuma sake zaben Gwamna Babajide Sanwo-Olu.

Shugaba Bola Tinubu ya samu yabo

“Shugabanmu ya ɗauki wasu muhimman matakai masu wahala domin aiwatar da kyawawan manufofi da bunkasa kasar nan."
"Tuni muka fara ganin tasirin wadannan dabarun gwamnati masu kyau.”

- Alhaji Sikiru Alabi-Macfoy

An bukaci a sake zaben Shugaba Tinubu a 2027
Mai girma Bola Ahmed Tinubu na jawabi Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Alhaji Sikiru Alabi-Macfoy ya kara da cewa tun kafin Shugaba Tinubu ya hau kan kujerar mulki, ya san matsalolin da ke damun Najeriya, kuma ya shafe shekaru yana samar da tsari mai kyau kafin 2023.

“Ya zo da cikakken shiri. Ya yi abubuwan da shugabanni da dama da suka gabace shi suka kasa ko suka ki yi."

- Alhaji Sikiru Alabi-Macfoy

Atiku ya ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ragargaji Shugaba Bola Tinubu kan matsalar rashin tsaro.

Atiku ya bukaci Tinubu ya tashi tsaye wajen magance matsalar ko kuma ya yi murabus idan ba zai iya ba.

Kara karanta wannan

Alaka ta yi tsami tsakanin Tinubu da Yahaya Bello? An ji gaskiyar zance

Ya koka kan yadda ake ci gaba da rasa rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya a sassa daban-daban na kasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng