2027: Tsohon Hadimin Osinbajo Ya Fadi Kullin da APC Ta Yi wa Kano
- Jigon APC a Kano, Mallam Alwan Hassan, ya faɗi yadda jam’iyyarsu ta shirya karɓe mulkin Kano a zaben 2027
- Alwan Hassan ya janye zargin da ya yi wa Sanatoci kan cin hancin Dala miliyan 10, ya roƙe su su yafe masa
- Ya kuma nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Injiniya Ramat Abdullahi a matsayin Shugaban NERC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon mai ba wa mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shawara, kuma jigon APC a jihar Kano, Mallam Alwan Hassan ya ce za su karɓi Kano.
Ya ce yana da cikakken tabbacin cewa jam’iyyarsa za ta karɓe mulkin jihar Kano daga NNPP a zaɓen 2027 saboda sabon shirinsu

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Alwan Hassan ya ce APC na ƙara ƙarfafa tasirinta tun daga cikin gida
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC na shirin kwace Kano a zaben 2027
Alwan Hassan ya ce yanzu haka ana haɗa kan manyan ’yan siyasa a fadin jihar domin tunkarar babban zaben da ke tafe don kifar da NNPP.
Ya ce jam’iyyar na gudanar da shirye-shirye da suka haɗa da sake farfaɗo da karsashin yan jam'iyya, tattaunawa da tsofaffin jiga-jigai, da kuma jan hankalin matasa zuwa APC.
Ya bayyana cewa dole ne jihar Kano ta sake daidaita da gwamnati ta tarayya domin kowa ya amfana.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Ku jira ku gani. APC za ta karɓe Kano a 2027.”
Ya ce suna da kwarin gwiwa a kan ayyukansu, kuma za a samu nasara da zarar an buga a zabe mai zuwa.
Jigon APC ya nemi afuwar Sanatoci
Alwan Hassan ya janye maganar da ya yi a baya cewa akwai ’yan majalisar dattawa da suka karɓi cin hancin Dala miliyan 10.
Da farko, ya yi zargin sun karbi cin hanci domin hana tabbatar da nadin Ramat Abdullahi a matsayin shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC). Ya ce:
"Na janye wannan magana gaba ɗaya, kuma ina neman afuwa daga Majalisar Dattawa da shugabancinta.”
Ya ce bayan dogon nazari da tattaunawa, ya fahimci cewa bayanansa sun haifar da rudani, kuma ya ɗauki matakin janye su domin mutunta majalisa da kare martabar siyasa.
Alwan Hassan ya sake roƙon ’yan majalisar da su tabbatar da nadin Ramat Abdullahi, yana mai cewa shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu, ya zaɓe shi ne bisa cancanta.
Ya ce tabbatar da shi zai ƙara hanzarta gyaran bangaren wutar lantarki da al’umma ke matuƙar buƙata.
Kalaman Shugaban APC ya tayar da ƙura
A baya, kun ji cewa shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya nemi afuwar mazauna karamar hukumar Fagge bayan wasu kalamansa sun haddasa ce-ce-ku-ce.
Kalamansa sun jawo martani daga wasu shugabannin al’umma da suka nuna cewa kalaman sun yi zafi, lamarin da ya kai su ga garzayawa kotu domin neman hakkinsu.
Hoton Abdullahi Abbas da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yadda ce-ce-ku-cen ta karu, inda al’umma suka nuna rashin jin daɗi kan tauye darajar yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


