Umar: 'Wike Ya Gindaya Sharadi Mai Tsanani kafin a Samu Zaman Lafiya a PDP
- Wani jigon PDP, Umar Sani ya ce Nyesom Wike ya bukaci jam'iyyar da ta hakura da takarar shugabancin kasa a 2027
- A cewar Umar, hakura da takarar ne sharadin sulhu da ministan Abuja ya ba PDP, tare da barazanar sake jefa ta a rikici
- Jigon ya kuma yi magana game da rashin halartar jihohin Rivers, Osun da Taraba babban taron PDP da aka gudanar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wani babban jigon PDP, Umar Sani, ya bayyana cewa sharadin sulhu da ministan Abuja, Nyesom Wike, ya gindaya wa jam’iyyar gabanin 2027.
Umar Sani ya ce Wike ya umarci PDP da ta amince ba za ta tsayar da dan takarar shugaban kasa ba a 2027 idan har jam'iyyar na son kwanciyar hankali.

Source: UGC
Wike na so PDP ta hakura da takara a 2027
A zantawarsa da jaridar Daily Independent, Umar Sani ya bayyana cewa Wike ya fadi hakan ne lokacin da kwamitin sulhu da BoT ta kafa ya kai masa ziyara domin sasanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, Wike ya bayyana cewa za a samu rikici mai muni idan PDP ta tsayar da dan takarar shugaban kasa domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Umar Sani ya ce bayan ganin wannan matsaya ta Wike, jam’iyyar ta fahimci cewa babu wata hanyar sulhu da za ta yiwu, saboda sharuddan nasa sun sabawa manufa da tsarin jam’iyyar.
Saboda haka, Umar Sani ya ce PDP yanke hukunci cewa cire shi daga jam’iyyar ya zama dole duk da cewa an yi hakan ne a makare.
Yadda rikicin ya shafi taron PDP a Ibadan
Umar Sani ya ce rikicin cikin gida ya bayyana sosai a babban gangamin PDP da aka gudanar a Ibadan, inda wasu jihohi ba su halarta ba.
Ya ce jihohin Osun, Taraba da Rivers ba su turo wakilai ba, haka ma gwamnoninsu ba su halarta ba. Wannan, a cewarsa, ya nuna irin gagarumar matsalar da jam’iyyar ke fama da ita.
Ya ce wannan rashin halarta daga manyan jihohi ya janyo dimuwa a cikin jam’iyya, musamman ganin cewa 2027 na tafe kuma har yanzu PDP ba ta da cikakken tsari ko hadin kai.
Jigon na PDP ya bayyana cewa yanayin da jam'iyyar ta fada a halin yanzu shi ne mafi muni tun kafuwarta, saboda rashin zaman lafiya ya hana jam’iyyar sake farfado da martabarta.

Source: Twitter
Korar kusoshi za ta sake rikita PDP
Babban jigon na PDP ya ce korar manyan jiga-jigai daga jam’iyyar, ciki har da Nyesom Wike, Ayo Fayose da Samuel Anyanwu, zai kara tsananta rashin kwanciyar hankali.
Ya ce wadannan mutanen suna da girman tasiri a jam’iyyar, kuma rashinsu su zai iya janyo durkushewar PDP gaba ɗaya.
Ya yi tambaya kan yadda jam’iyyar za ta iya jure guguwar shari’u, rarrabuwar kawuna, da rashin amincewa na cikin gida da ke ci gaba da danne ta gabanin 2027.
PDP ta kori gwamnoni 3 daga jam'iyyar
A wani labarin, mun ruwaito cewa, PDP ta tabbatar da korar gwamnoni uku da tsofaffin jagorori saboda aikata wasu laifuffuka da suka sabawa jam'iyya.
Jam'iyyar da ke karkashin tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike, ta ce ta kori gwamnonin da kuma kusoshin ne domin dawo da martabar PDP.
Hakazalika, PDP ta sanar da tsige dukkanin shugabanninta a jihohi shida tare da ba kwamitin NWC umarnin kafa shugabannin riko kafin a yi zabe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


