Ana Wata ga Wata: PDP Ta Fatattaki Gwamna Bala da Wasu Gwamnoni 2 daga Jam'iyya

Ana Wata ga Wata: PDP Ta Fatattaki Gwamna Bala da Wasu Gwamnoni 2 daga Jam'iyya

  • PDP ta tabbatar da korar gwamnoni uku da tsofaffin jagorori saboda aikata wasu laifuffuka da suka sabawa jam'iyya
  • Tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike, ta ce ta kori gwamnonin da kuma kusoshin ne domin dawo da martabar PDP
  • Hakazalika, PDP ta tsige dukkanin shugabanninta a jihohi shida tare da ba kwamitin NWC umarnin kafa shugabannin riko

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar zartarwa ta kasa ta PDP, tsagin Nyesom Wike, ta gudanar da muhimmin zama a Abuja domin tattauna rikicin cikin gida da ya yi kamarin gaske a jam’iyyar.

Zaman na NEC ya mayar da hankali ne kan hukuncin da ya shafi manyan shugabannin jam’iyyar da suka ci karo da tanade-tanaden doka da tsare-tsaren PDP.

Jam'iyyar PDP ta kori gwamnoni uku da wasu kusoshi daga jam'iyyar.
Hoton Gwamna Bala Mohammed, Gwamna Seyi Makinde da shugaban PDP a sakatariyar jam'iyyar. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

PDP ta kori gwamnoni 3 daga jam'iyyar

Jaridar Punch ta rahoto cewa, PDP tsagin ministan Abuja ta fatattaki Gwamna Bala Mohammed, Gwamna Dauda Lawal da Gwamna Seyi Makinde daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Mulki da mulki: Gwamna Bala, Makinde da Wike sun yi cirko cirko a hedkwatar PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban tsagin PDP, Alhaji Mohammed Abdulrahman, ya bayyana dalilai masu nauyi da suka sa NEC ta kori kusoshin jam'iyyar, ciki har da gwamnonin na Bauchi, Oyo da Zamfara.

Ya ce wadannan mutane sun halarci wani taro ba tare da izinin jam’iyya ba, kuma hakan ya saba wa hukuncin kotu da ke aiki a wancan lokaci.

A cewar Abdulrahman, irin wadannan matakai na karya doka sun girgiza tsarin jam’iyya, sun haifar da ruɗani, sun kuma janyo wa PDP ficewar gwamnoni da ’yan majalisa zuwa wasu jam’iyyu.

Ya ce idan PDP za ta farfado ta dawo da karfinta, dole ne a hukunta wadanda suka karya dokoki domin zama darasi ga sauran mambobin jam’iyya a matakai daban-daban.

PDP ta saki sunayen kusoshin da ta kora

A bayanin da sakataren PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya karanta, NEC ta ce jam’iyyar ba za ta ci gaba da lamutar tauye doka ko abin da zai zubar da mutuncin PDP ba.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Halin da ake ciki bayan jibge jami'an tsaro a hedkwatar PDP

An ce dole ne a hukunta duk wanda ya karya kundin tsarin jam’iyya ko ya zama barazana ga zaman lafiya a cikin jam’iyyar, in ji rahoton TVC News.

NEC ta amince da fara aiwatar da ladabtar da manyan jiga-jigai da suka hada da: Adolphus Wabara, Olabode George, Ben Obi, Kabiru Tanimu Turaki, Bala Mohammed, Seyi Makinde, Dauda Lawal da wasu shugabanni da dama.

An kuma bayyana cewa manufar wannan mataki shi ne a dawo da bin doka da oda, da tabbatar da cewa PDP ba ta karkata daga tsarin da ta yi imanin shi ne ginshikin jam’iyyun dimokuradiyya.

PDP tsagin Wike ta tsige shugabanninta a jihohi 6.
Hoton taron NEC na PDP da shugabannin jam'iyyar tsagin Nyesom Wike suka gudanar a Abuja. Hoto: @OlayinkaLere
Source: Twitter

PDP ta tsige shugabanninta a jihohi 6

A wani muhimmin mataki, PDP ta kuma sanar da rushe shugabancin jam'iyyar a jihohi shida da suka hada da Bauchi, Oyo, Zamfara, Yobe, Lagos da Ekiti.

PDP tsagin ministan Abuja, sun bayyana cewa sun dauki wannan matakin ne saboda shugabannin jam'iyyar a jihohin sun gaza bin tsarin da ya kamata jam’iyya ta rika tafiya a kai.

Tsagin na NEC ya umarci NWC da ya gaggauta kafa kwamitocin riko wadanda za su rika shugabantar jam’iyya har zuwa lokacin da za a gudanar da sababbin zabuka a jihohin.

Kara karanta wannan

An ba hammata iska bayan hana jiga jigan jam'iyyar PDP shiga taro a Abuja

An ba hammata iska a sakatariyar PDP

Tun da fari, mun ruwaito cewa, rikici mai zafi ya barke a hedikwatar PDP bayan jagororin bangarorin jam'iyyar sun yi kokarin shiga ofishin a Abuja.

Jami'an tsaro sun yi yunkurin hana gwamna Bala Mohammed da Gwamna Seyi Makinde shiga sakatariyar, domin halartar wani taro da bangarensu ya kira a Wadata Plaza.

An kuma rahoto cewa, jami’an tsaro da aka jibge a kofar shiga hedikwatar PDP sun kuma hana Ministan Abuja, Nyesom Wike, shiga harabar sakatariyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com