Abu Ya Girma: Halin da Ake Cikin bayan Jibge Jami'an Tsaro a Hedkwatar PDP

Abu Ya Girma: Halin da Ake Cikin bayan Jibge Jami'an Tsaro a Hedkwatar PDP

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya na ci gaba da tsintar kanta cikin rikicin shugabanci wanda ya ki karewa har yau
  • Rikicin ya jawo bangarori biyu masu hamayya da juna sun kira tarurruka daban-daban a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja
  • Sai dai, tun da sassafe an jibge jami'an tsaro a hedkwatar jam'iyyar domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - An kara tsaurara matakan tsaro a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke babban birnin tarayya Abuja.

An dauki matakin ne yayin da bangarori biyu masu hamayya da juna suka shirya gudanar da tarurruka daban-daban a wuri guda.

An jibge jami'an tsaro a hedkwatar PDP
Hedkwatar jam'iyyar PDP da ke Wadata Plaza a Abuja Hoto: @OfficialPDPNig
Source: UGC

Jaridar The Punch ta ce an ga ’yan sanda dauke da makamai da motocin sintiri sun tsaya a bakin kofar shiga hedikwatar jam’iyyar da safe a ranar Talata.

Kara karanta wannan

An ba hammata iska bayan hana jiga jigan jam'iyyar PDP shiga taro a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sam Anyanwu ya isa hedkwatar PDP

Samuel Anyanwu, wanda shi ne sakatare a baya kuma 'yan bangaren jam’iyyar da ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, ya isa da sassafe inda ya karbe iko da hedkwatar.

Da yake zantawa da manema labarai, Anyanwu ya jaddada cewa shi ne har yanzu sakataren jam’iyyar domin wa’adinsa zai kare ne a watan Disamba, duk da rikicin shugabanci da ake fama da shi.

Lokacin da aka tambaye shi ko shi ne ya kira jami’an tsaron da suka zo hedkwatar, sai Anyanwu ya tabbatar da cewa shi ne ya gayyato su.

“Dabi’ar PDP ce a kira jami’an tsaro idan akwai babban taro domin tabbatar da zaman lafiya da doka.”

- Samuel Anyanwu

Ya kara da cewa jami’an tsaron suna nan cikin shiri domin hana wasu masu kutse da suka sanar da gudanar da taro na daban shiga cikin harabar hedkwatar jam'iyyar.

Bangarorin PDP 2 na rigima da juna

Kara karanta wannan

Turaki: Zanga zanga mai zafi ta barke a hedkwatar jam'iyyar PDP a Abuja

Rikicin PDP ya tsananta a ranar Litinin bayan da bangaren Wike da na Gwamna Seyi Makinde na Oyo suka kira tarurukkan NEC daban-daban a hedikwatar jam’iyyar.

Bangarorin biyu na kai ruwa rana kan shugabancin jam’iyyar, bayan babban taron Ibadan na ranar Asabar da ya samar da sabon kwamitin NWC tare da korar wasu manyan magoya bayan Wike.

Duk da korar da aka yi musu, magoya bayan Wike sun fitar da sanarwar kiran taron NEC da BoT na gagagawa a hedkwatar jam'iyyar.

Jaridar Vanguard ta ce a wata sanarwa da Anyanwu ya fitar a ranar Litinin, ya ce an shirya gudanar da tarurrukan ne a dakin taro na NEC a hedkwatar jam'iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja.

Sai dai bangaren Kabiru Tanimu Turaki, wanda shi ne sabon shugaban da aka zaɓa a Ibadan, ya sanya wani taronsa a hedkwatar, inda suka zargi Anyanwu da shirin tayar da tarzoma.

An kai jami'an tsaro hedkwatar PDP
Hedkwatar PDP da ke Wadata Plaza a Abuja Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Da yake jawabi ga manema labarai, Kabiru Tanimu Turaki ya ce:

“Mun zo ne mu gana da kwamishinan ’yan Sanda na Abuja game da taronmu na gobe. Wannan shi ne zaman farko na sabon kwamitin NWC ɗinmu.”

Kara karanta wannan

Abu ya kacame, sabon shugaban PDP da tsagin Wike na iya arangama a taro

Ya jaddada cewa magoya bayan Wike ba su da hurumi a fuskar doka, bayan da aka kore su a Ibadan.

Anyanwu ya dora laifi kan gwamnonin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa sakataren jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya yi tsokaci kan rikicin da ya addabi jam'iyyar.

Sanata Samuel Anyanwu ya zargi kungiyar gwamnonin jam'iyyar da haifar da rikicin da ya dabaibaye PDP.

Sakataren na PDP na kasa ya yi ikirarin cewa gwamnoni bakwai da da suka rage a PDP ne suka janyo matsalolin da ake ciki a jam'iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng