An Ba Hammata Iska bayan Hana Jiga Jigan Jam'iyyar PDP Shiga Taro a Abuja
- Rikici ya barke tsakanin bangarorin jam’iyyar PDP a hedikwatar jam’iyyar bayan hatsaniya ta barke a taron ake gudanar wa a Abuja
- Jami'an tsaro sun yi yunkurin hana gwamna Bala Mohammed da Ministan Abuja, Nyesom Wike, su taron da bangarensu ya kira a Wadata Plaza
- Kamarin rikicin ya samo asali ne daga dakatar da bangaren Wike a Babban Taron Kasa na PDP da ya gudana a karshen mako
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – A safiyar Talata 18 ga watan Nuwamba, 2025 ne aka bai wa hammata iska a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Wadata Plaza, Abuja.
Rikicin ya faru ne bayan bangarorin jam’iyyar biyu da ke hamayya da juna suka iso wajen domin gudanar da taronsu daban-daban.

Source: Twitter
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa rikicin PDP ya ta’azzara tun bayan dakatar da wasu'yan jam'iyya na bangaren Nyesom Wike a babban taron jam’iyyar da aka yi a karshen mako.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar PDP ta rikice a taron Abuja
Daily Post ta wallafa cewa hukuncin dakatar da Wike da magoya bayansa ya fusata su, kuma sun dage a kan cewa su ne halastattun 'yan jam'iyya.
A martanin dakatarwar, bangaren Wike ya kira taron gaggawa a hedikwatar jam’iyyar domin tattauna mataki na gaba.
Shi ma bangaren shugabancin jam’iyyar da Kabiru Tanimu Turaki ke tare da su ya shirya nasa zaman a rana guda.

Source: UGC
A yayin da bangarorin biyu suka iso hedikwatar da safiyar Talata, jami’an tsaro da aka jibge a kofar shiga sun hana Ministan Abuja, Nyesom Wike, shiga harabar.
Su ma Gwamna Bala Mohammed, wanda shi ne shugaban gwamnonin PDP, an dakatar da shi daga shiga don kauce wa karin hatsaniya.
An dambatu a taron jam'iyyar PDP
Tun da safiyar Talata, an ga manyan jami’an tsaro suna sintiri a bakin kofar shigar ginin PDP, yayin da 'yan bangarorin biyu ke tururuwar neman shiga don gudanar da zaman da suka shirya.
An ga yadda bangarori daban-daban ke ta kai-komo a kofar shiga, wasu ma tare da ‘yan daba, lamarin da ya haddasa turmutsitsi da hayaniya.
Hotunan da suka bayyana daga wurin sun nuna yadda aka kulle wasu sassa na harabar yayin da motocin tsaro ke sintiri domin dakile tashin hankali.
Daga bisani jama'a suka barke da dambe, inda aka rika naushin juna da ture wadansu, su kuma jami'an tsaro na na su aiki.
Ana zanga-zanga a hedikwatar PDP
A baya, mun wallafa cewa magoya bayan bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, sun yi zanga-zanga a Wadata Plaza suna adawa da sabon shugaban PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki.
Wadanda suka fito zanga-zangar—galibi mata da matasa—sun nuna adawa kai tsaye ga sabon shugaban jam’iyyar na kasa, Kabiru Tanimu Turaki, SAN da aka zaba a Ibdan.
Rahotanni sun ce boren da aka yi a Abuja ya samo asali ne daga sabon shugabanci da aka zaba a babban taron jam’iyyar da aka gudanar ranar Asabar a Ibadan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


