Turaki: Zanga Zanga Mai Zafi Ta Barke a Hedkwatar Jam'iyyar PDP a Abuja

Turaki: Zanga Zanga Mai Zafi Ta Barke a Hedkwatar Jam'iyyar PDP a Abuja

  • Magoya bayan tsagin ministan Abuja a rigimar PDP sun fantsama zanga-zangar adawa da sabon shugaban jam'iyyar na kasa, Tanimu Turaki
  • Rahotanni sun nuna cewa an ga matasa maza da mata dauke da kwalaye sun mamaye titunan da je kewaye da Wadata Plaza a birnin Abuja
  • Tuni dai jami'an rundunar 'yan sanda suka mamaye wurin domin dakile duk wata barazana da iya tasowa a hedkwatar jam'iyyar hamayyar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Zanga-zanga mai zafi ta barke a Wadata Plaza, babban ofishin jam'iyyar PDP ta kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Magoya bayan bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike na jam’iyyar PDP sun mamaye titunan da ke kewaye da Wadata Plaza, hedikwatar jam’iyyar da ke Wuse Zone 5, Abuja.

Zanga zanga a hedkwatar PDP.
Hoton masu zanga-zangar adawa da Tanimu Turaki a kewayen hedkwatar PDP da ke Abuja Hoto: @OfficialPDP
Source: Twitter

Dalilin zanga-zanga a hedkwatar PDP

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Halin da ake ciki bayan jibge jami'an tsaro a hedkwatar PDP

Jaridar Punch ta ce masu zanga-zangar, wadanda suka kunshi mata da matasa, sun bayyana adawarsu ga sabon shugaban jam’iyyar na kasa, Kabiru Tanimu Turaki, (SAN).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa matasan sun daga kwalayen da nuna adawa da shugabancin Turaki, masu dauke da sakonni kamar, "Ba ma son Turaki," "dole Turaki ya sauka."

An zabi Turaki, tsohon Ministan Ayyuka na Musamman a matsayin shugaban jam’iyyar PDP a babban taron da aka gudanar ranar Asabar a Ibadan, wanda tsagin Wike suka kauracewa, tare da kiran taron “ba bisa ka’ida ba”.

Wannan dai na zuwa ne bayan bangarori biyu masu adawa da juna, tsagin Turaki da na Wike, sun shirya taron kwamitin gudanarwa (NWC) rana daya a hedkwatar PDP.

Dukkansu dai sun sanya taron ne yau Talata, 18 ga watan Nuwamba, 2025, lamarin da tun farko aka yi hasashen zai wahala a karkare lafiya.

Tsagin Wike sun dura Wadata Plaza

Tun farko tsagin Wike, karkashin jagorancin Abdulrahman Mohammed, ne suka fara isa hedikwatar jam’iyyar tare da tawagar ‘yan sanda masu dauke da makamai.

Kara karanta wannan

An ba hammata iska bayan hana jiga jigan jam'iyyar PDP shiga taro a Abuja

Jami’an tsaron sun mamaye tituna da hanyoyin shiga ginin Wadata Plaza tun bayan shigar tawagar tsagin Wike, sun tsaya a muhimman wurare domin dakile duk wata barazana, in ji Daily Trust.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wani mamba daga bangaren Tanimu Turaki da ya bayyana a harabar Wadata Plaza.

Zanga zanga a Abuja.
Hoton masu zanga-zanga a hedkwatar PDP da ke Abuja Hoto: @ayofe
Source: Twitter

Turaki dai yana da goyon bayan gwamnonin PDP, majalisar amintattu (BoT) da sauran manyan kusoshin babbar jam'iyyar adawa.

Sai kuma tsagin Abdulrahman Mohammed, wanda ke samun goyon baya daga Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Ezenwo Wike.

Anyanwu ya dora laifi kan gwamnonin PDP

A wani labarin, kun ji cewa jagoran tsagin PDP da ke goyon bayan ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya caccaki gwamnonin jam'iyyar.

Anyanwu, tsohon sakataren PDP na kasa ya yi ikirarin cewa gwamnoni bakwai da da suka rage a PDP ne suka janyo matsalolin da ake ciki a jam'iyya.

Ya yi fatali da korarsa daga jam’iyyar PDP, yana mai cewa matakin bai da inganci kuma ba bisa ka’ida aka yi shi ba kuma ba zai kai karar abin da ya kira “karya doka” kotu ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262