Ana Jimamin Sace Dalibai, Gwamnatin Kebbi Ta Yi Martani kan Shirin Malami na Tsayawa Takara
- Ministan shari'a a gwamnatin marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abubakar Malami ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Kebbi
- Abubakar Malami ya bayyana cewa zai fito takara ne domin magance matsalolin da suka addabi jihar a fannin tsaro tare da farfado da noma
- Gwamnatin Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris, ta fito ta yi magana kan shirin tsohon ministan na tsayawa takarar gwamnan jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi martani kan shirin tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami, na tsayawa takarar gwamna.
Gwamna Nasir Idris ya ce shirin Abubakar Malami SAN, na tsayawa takarar gwamna a 2027 bai haifar da wata fargaba ga gwamnatinsa ba.

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta hannun babban sakataren yada labaransa, Ahmed Idris, yayin wata tattaunawa da jaridar The Punch.
Malami ya shirya tsayawa takarar gwamnan Kebbi
A wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin, Malami ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan jihar Kebbi.
Tsohon ministan ya yi alkawarin kawo tsari mai karfi wajen magance matsalar tsaro da farfaɗo da sashen noma da ke tangal-tangal a jihar Kebbi.
Malami ya ce yana da cikakken goyon bayan jama’a a fadin jihar, yana mai cewa burinsa na siyasa wani yunkuri ne ceto jihar, musamman wajen kawo karshen hare-haren ’yan bindiga, buɗe gonaki da kuma kare masana’antu na cikin gida.
Ya ce magoya bayansa a sassa daban-daban sun yi karfi, duk da cewa dokokin zabe ba su amince da fara yakin neman zabe da wuri ba.
Hakazalika ya kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki da jefa Arewacin kasar nan cikin karin wahala tare da barin manoma cikin rashin tsaro, abin da ya ce ya lalata harkar noma.
Me gwamnatin Kebbi ta ce kan takarar Malami?
A martanin da ya yi, Ahmed Idris, ya ce sanarwar Malami ba ta zama abin mamaki ko damuwa a wajen gwamnati ba.

Source: Facebook
Ya jaddada cewa mutanen jihar ne kaɗai za su yanke hukunci kan shugaban da suke so ya jagorance su.
“Wannan ba sabon abu ba ne ga kowa a Kebbi. Kowa yana da damar bayyana aniyarsa ta takara.”
"Masu kada kuri'a ne kawai za su tantance wanda zai zama gwamnan su a babban zaben gaba da ake tunkara."
"Ba mu da wani dalilin damuwa ko firgici game da wannan sanarwar."
- Ahmed Idris
Gwamnan Kebbi ya yi alkawari kan sace dalibai
A wani labarin kuma, kuma kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kai ziyarar gani da ido zuwa garin Mada da ke karamar hukumar Danku/Wasagu, inda 'yan bindiga suka sace dalibai mata.
Gwamna Nasir Idris ya daukarwa iyayen yaran da aka sace alkawarin cewa gwamnati za ta yi bakin kokarinta domin kubutar da su.
Ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa yaran sun kubuta cikin aminci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


