Tanimu Turaki: Muhimman Abubuwa 7 da Ya Kamata a Sani game da Sabon Shugaban PDP
- An gudanar da babban taron jam'iyyar adawa ta PDP a birnin Ibadan da ke jihar Oyo inda aka zabi sabon shugaba na kasa
- Minista a mulkin Goodluck Jonathan, Kabiru Tanimu Turaki ya zama sabon shugaban PDP bayan zabensa babu hamayya
- Yayin taron da aka gudanar, PDP ta sallami wasu daga cikin jagororinta da suka hada da tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Tanimu Turaki ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP na kasa a taronta da aka gudanar.
Babban lauya kuma tsohon minista ya zama sabon shugaban na jam’iyyar PDP bayan babban taron da aka gudanar babu hamayya

Source: Facebook
Turaki: Abubuwan sani game da shugaban PDP
Rahoton Channels TV ya ce Tanimu Turaki ya samu nasara ba tare da hamayya ba wanda hakan ya sanya shi cikin muhimman mutane da ake sa ran za su sake tsarawa da farfaɗo da jam’iyyar adawa a matakin ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da yake jawabi Turaki ya yi godiya matuka bisa nasarar da ya samu tare da ba da tabbacin cewa zai yi duk mai yiwuwa domin farfado da jam'iyyar PDP.
Legit Hausa ta duba wasu muhimman abubuwa game da Kabiru Tanimu Turaki wanda ya zama shugaban PDP.
1. Karatu da zama fitaccen lauya
Kamar sauran yaran zamaninsa, an tura Kabiru Tanimu makarantar Alkur'ani domin samun ilimin addini.
Don samun ilimin zamani, an sake sanya shi a makarantar Firamare ta Nasarawa, Babban Birnin Kebbi.
Turaki ya halarci kwalejin Barewa da ke a Zariya, kuma ya kasance mataimakin kyaftin a gidan Suleiman Barau.
Don ci gaba da karatunsa, Kabiru ya tafi Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Sakkwato don IJMB, sannan ya sami shiga Jami’ar Jos, don karanta shari’a.
Ya kammala ba matsala, sannan ya tafi Makarantar koyon aikin Lauyoyi ta Najeriya, Lagos inda aka kira shi domin zama lauyan Nijeriya a shekarar 1986.
2. Ƙwarewa a fannin shari’a
Kabiru Tanimu Turaki (SAN) sananne ne a bangaren shari’a, inda ya shafe shekaru yana gudanar da manyan shari'a masu nasaba da kundin tsarin mulki, ƙorafe-ƙorafen zaɓe.
Sannan ya kware wurin sasanta rikice-rikice, harkokin shari’ar ƙasa da ƙasa da mallakar fasaha.
Ya kuma yi suna a fannoni kamar haɗin kamfanoni da gudanar da takardun shaidar gwamnati a matsayinsa na mai kula da bangarorin da suka shafi shari'a.

Source: Facebook
3. Tasirinsa a ƙungiyoyin ƙwararru
Sabon shugaban jam'iyyar PDP yana daga cikin wadanda ake girmamawa a fannin sana’arsu ta lauya duba da kwarewarsa.
Turaki yana daga cikin kungiyoyin kwararru kamar 'Chartered Institute of Arbitrators' (FCIArb) da kuma 'Institute of Corporate Administration' (FCIDA).
Wannan ke kara nuna matsayinsa tsakanin ƙwararrun masu shari’a a ɗaukacin ƙasar nan, kamar yadda muka samu daga Vanguard.
4. Kwarewa a gwamnati da rike mukamai
A baya ya yi aiki a matsayin Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnatoci, kuma ya taɓa rike mukamin Ministan Ma’aikata na wucin-gadi.
Wadannan mukamai sun ƙara masa ƙwarewa da tasiri a gudanar da harkokin gwamnati a matakin tarayya.
5. Dangantakarsa da jam'iyyar PDP
Turaki na daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP, domin yana shugabantar kungiyar ministocin jam'iyyar PDP.
Tsohon ministan ya kuma yi takarar gwamnan Jihar Kebbi da na shugaban ƙasa na jam’iyyar, cewar Punch.
Dadewar da ya yi a cikin jam’iyyar ta karfafa masa alaƙa da manyan jam'iyyar da goyon baya a sassa daban-daban.

Source: Facebook
6. Asali da martabar gidan Tanimu Turaki
An haife Kabiru Tanimu Turaki a ranar 3 ga Afrilu, 1957, a Birnin Kebbi, kuma ya fito daga gida mai daraja da tarihinsa ya shahara wajen ilimi da hidimar jama’a.
A yanzu, yana rike da sarautar Dan Masanin Gwandu da Zarumman Kebbi, manyan mukamai na gargajiya da ke ƙara darajarsa a yankinsa.
7. Jajircewa da kuma halayensa na kirki
Wadanda suke da kusanci da shi suna bayyana 'dan siyasar a matsayin mutum mai ladabi, nutsuwa da jajircewa wajen yi wa al’umma hidima.
Tsayuwarsa da dogewa kan ci gaban PDP duk da mawuyacin halin siyasar da jam’iyyar ta shiga a wasu lokuta ya kara masa mutunci da karɓuwa.
Wannan na daga cikin dalilan da wasu ke ganin zai ba shi damar ba da gudunmawa sosai gare ta bisa la'akari da kwarewa da kuma dadewa a cikinta.
PDP ta kori Wike, Fayose kan cin amanarta
A baya, mun ba ku labarin cewa jam'iyyar PDP mai adawa ta yi ta maza a taronta da aka gudanar a jihar Oyo inda ta sallami wasu daga cikin jiga-jiganta.
Daga cikin wadanda jam'iyyar ta tabbatar da korarsu akwai ministan Abuja, Nyesom Wike, Ayodele Fayose da ke kawo mata cikas.
Tsagin Wike ya yi ƙoƙarin dakatar da taron ta hanyar kotu, amma PDP ta samu hukuncin kotun Oyo da ya ba ta damar gudanar da taron.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



